HUƊU

787 82 3
                                    

HAƘƘIN MALLAKATA

July, 13, 2019

JINI YA TSAGA....! 👭

©BY UM_NASS 🏇

®NWA

DEDICATED: DEAR SADY JEGAL

PAGE 4

Shuru ne ya ratsa atsakanin su, ba tare da sun sake magana ba, sai dai har yanzu hannayen Adda Halima na riƙe dana Hafsat tana kuma kallon ta.

Zame hannunta Hafsa tayi ta kalli Adda Halima tana girgiza kai "Bazan iya cewa na sauya ba Adda Halima, kamar yanda bazan iya hararo abin da zai faru dani agobe ba. Tabbaci ɗaya nake dashi akaina shine zan iya miki biyayya kwatan-kwacin yadda ɗiya kema uwar ta."

Kallonta Adda Halima tayi, ta girgiza kai "Wanan ma bazan sameshi ba atare da ke ba Hafsa. Kawai zan iya kawar da kaina kamar yanda na saba awancan lokacin. Amma alfarma ɗaya nake buƙata agare ki dan Allah." ta ƙarasa maganar tana haɗe hannayen ta biyu awaje ɗaya.

Kallon ta Hafsa tayi tana faman ɗaga mata kai "Ina jinki Adda Halima. Wata alfarma kike so agare ni?"

"Nan unguwar sabuwar unguwa ce agaremu, haka kuma sabon waje ne da yake ɗauke da mabam-banta muta ne. Ta ko ina akewaye nake da maƙota kaɗan masu sona da yawa kuma masu jiran ganin gazawa da tawaya atare da ni na kasawa."

Numfashi taja ta fuzgar da iska mai zafi abakin ta sanan ta sauƙe wata ajiyar zuciya ahankali, kana taci gaba da magana "Hafsa ɗabi'arki da halayyarki ba sabon abu bane agare ni, amma bazan iya jure ƙananun maganganun da suke ɗabi'arki bane, koda zama yayi zama atsakanin mu idan wani saɓani yazo ya gifta to dan Allah ya ƙare alokacin, kada ki fiddashi waje wani yaji cikinmu, kada kuma ki fesar da zafin sa ta yanda zai zama abin gori da manuniya akan zumuncin mu."

"In sha Allah Adda Halima, na faɗa miki atare da ke wanan sabuwar Hafsa ce. Bazan mai-maita abin da nake abaya ba. Koda ace zama yayi zama to na tabbata zan ƙaru ne da kyawawan ɗabi'u daga gareki, wanda zasu sauya nawa ɗabi'un."

"Allah yasa hakan to."

"Ameen."

Daga nan suka shiga hirar su ta yaushe gamo. Kaɗan-kaɗan sukan taɓa abin da ya shafi rayuwar su da kuma gidan su. Wanda ga Adda Halima takanji kewar gida atare da ita, amma ganin Hafsa ayau sai ya cike mata ko wata irin kewa da take tare da ita. Sai da suka kusan raba dare suna hira kafin kowaccen su ta tafi ta kwanta.

*****
Washe gari.
Kafin Adda Halima ta tashi, Hafsa ta tashi tayi aiyukan gidan hatta shirya yara ita tayi suka tafi makaranta. Kana ta sake gyara gidan.
Lokacin da Adda Halima ta fito taga gidan tarwai atsaftacce tasha mamaki "Kaddai kice min yau kin gama komi na gidan?" ta ƙarasa maganar tana riƙe da haɓarta.

Murmushi Hafsa tayi tana gyaɗa kanta "Aikuwa yau kam na hutar da ke komi Adda. Ga ruwan wanka can na haɗa miki yana toilet, idan kin shirya sai muyi karin kumallo."

"Ikon Allah! Kice yau kin maida ni asalin basarakiya Hafsa. Lallai na ƙara yadda mutum rahama ne babba, yau gashi babu wanda ya tasheni dan wata hidimarsa, kin ɗauke min wanan nauyin. Nagode ƙwarai da gaske."

Kai Hafsa ta girgiza mata "A'a Adda Halima duk abin da na miki ko nayima yaran ki kaina nayiwa. Duk wani abu aduniya na kirki ko akasin sa idan mutum ya aikata to kansa ya aikatawa. Balle kuma abin da ya fito daga naki tsagin to sai ya cika ko wata ƙauna atare dani."

Riƙe hannun ta Adda Halima tayi tana kallon ta idonta ya ɗan taru da hawaye, kasancewar ta mace mai rauni da saurin karayar zuciya "Ba iya yau kaɗai ba! Zanso hakan yaci gaba atare da mu muddum ranmu. Ina fatan wanan halayyar itace zahirin da zata ci gaba da shumfuɗuwa acikin kyakkyawar fuskar ki."

Kallon ta Hafsa tayi ta ɗan turo bakin ta "Har yanzu kina da tan-tama da shakku akaina Adda halima. Sai dai so nake zuciyar ki ta baki tabbaci da gamsuwa akan wanan sabuwa ce, mai tafe da alkhairai masu yawa atare da ita."

Sakin Hannun ta Adda Halima tayi tana murmushi "Ba'a iya sauyawa tuwo suna Hafsa, ba kuma a iya canja abin da ya zama jiki da ɗabi'a. Amma ana iya hasashen wata rana zai iya sabuntawa ko kuma ya sauƙaƙa wasu daga cikin su."

Tana gama faɗar haka ta shige banɗakin ta bar Hafsa da mata rakiyar ido.
Hannunta ta haɗa ta danƙwasa yatsunta suka bada sautin ƙash-ƙash sanan ta gyaɗa kanta, cikin sautin da kunnen ta kaɗai yake isa tace "Kin faɗi gaskiya Adda Halima, bazan iya sauyawa ba, ni na sani. Amma zan iya rangwata miki kaɗan daga cikin wasu abubuwan da sukan zama ɗabi'a agare ni, masu ban haushi."

Sanan ta koma ɗakin Adda Halima ta gyara mata shi tsaff.
Ta kuma shimfiɗa musu tabarma, ta jera musu ɗumamen tuwon data musu, gefe kuma jalof ɗin taliyar hausa ce wadda tayima yara ita suka tafi makaranta da ita aka samu ragowa, ta haɗo musu da ita. Gefe kuma kunun tsamiya ta dama musu, kasancewar Adda Halima bata rabuwa da garin kunun saboda ƙaunar ta da shi.

Dai-dai fitowar Adda Halima, ta kalli wajan tana jinjina wanan sabon salon na Hafsa, Allah ya sani Zuciyar ta bata samu nutsuwa da gamsuwa da sabbin ɗabi'un da take zuwar mata da su ba. Ita kam da zata mata Adalci to kawai ta fito mata a Hafsan data sani, ba wai tana mata Ƙumbiya-ƙumbiya ba.

Kayanta tasa sanan ta zauna suka fara cin abincin, bayan gaisuwar da suka sake yi.
Babu mai magana acikin su har suka kammala ci.

Anan wayar Adda Halima ta ɗauki ƙara da tsiwa, da sauri Hafsa ta ɗauko ta miƙa mata tana murmushi "Yaya Ado ke kiran ki."

Karɓa tayi tana latsa wayar "Assalama alaikum kawun yara."
Daga ɗaya ɓangaran ya amsa mata yana faɗaɗa fara'arsa.
"Mun tashi lafiya Halima? Ya yaran da kuma haƙurin rayuwa."

Murmushi tayi mai sauti "Mun gode Allah Kawu. Ya Anty Lubabatu da yaran?"
"Lafiya lau." ya faɗa yana taƙaita maganar.

"Umm Hafsa ko ta zo wajanki?"

"Eh gata jiya ta zo, na bata ku gaisa ne?"
Saurin dakatar da ita yayi "A'a bana buƙatar jin muryar ta ko kaɗan. Dan kema na kiraki na miki kashedi akanta, idan da hali ma ki koreta tasan inda dare ya mata."

Cikin mamaki da furgicin jin maganar sa ta kalli Hafsa wadda ta tashi tabar musu wajan, tana matsar hawaye.
Kai ta fara girgizawa kamar yana gaban ta "Kasan abin da kake faɗa kuwa kawu? Hafsa ƙanwata kake cewa na kora agidana? Hafsa fa kawu? Ko dai kayi suɓutar baki ne."

"Ko kaɗan Halima! Asalima na faɗa cikin sani da baki zaɓi akan abin da baki sani ba akan halayyar Hafsan, nasan bazata faɗa miki maƙasudin korar da Alhajinmu ya mata ba......" anan ya sanar da ita duk abin daya faru.

"Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un." kalmar da Adda Halima ta faɗa hawaye na zuba a idonta.

"Dan haka nake baki shawara ki tattara ki koreta, tun kafin kema ta zame miki masifa kamar yadda ta zamewa mahaifinmu."

Cikin sautin kuka ta fara magana "A'a Kawu! Korar Hafsa ba shine mafita agare mu ba, har yanzu Hafsa jinin mu ce, duk abin da zatayi bazamu iya ƙyamatar ta mu koreta daga garemu ba. Na tabbata wata rana zata sauya. Haka kuma ni zan iya zama da ita, saboda nafi kowa sanin halayya da ɗabi'ar ta."

"Um-Um Halima! Ke kina da haƙuri da yawa, Hafsa kuma rigimammiya ce. Bana so ta zama silar sake jefaki cikin wani ƙunci da damuwar."

Murmushi tayi "Ba komi Kawu. In sha Allah zamu zauna da ita lafiya, a yanda na lura da ita kamar ta sauya yanzu saɓanin baya."

"Kayya dai Halima! Ba sauyawa tayiba, tayi dai kwantan ɓauna ne."

Dariya tayi tana girgiza kai kamar yana ganin ta "Kawu wani irin kwantan ɓauna kuma? Kai dai kawai ka yadda ta sauya."

Shima dariyar yayi yana girgiza kai "Ina baki tabbacin Bata sauyaba Halima. Kawai dai tayi tuban baƙin muzuru ne, amma nan kaɗan zaki sheda hakan." daga haka ya kashe wayar ya barta da bin ta da kallo.

🥀🥀🥀🥀🥀

_An dai ce da ƙibarsa gara ramarsa, shi yasa na baku ko ba yawa. Kuyi haƙuri bazaku na samun post JINI YA TSAGA akai-akai ba, dan da har na jingine labarin, amma saboda samun cikiya da amo mai sauti akan neman sa yasa na ƙoƙarta na muku. wata-ƙila kuna samun sa sau ɗaya asati, wata-ƙila kuma ya iya fin hakan. Amma dai ga lambar Girmamawarku acikin shafin. Ngd da kulawa sosai._

#JiniYaTsaga
#UmNass
#NWA
#Cmnts,like share
#GIRMAMAWA

JINI YA TSAGAWhere stories live. Discover now