GOMA SHA ƊAYA

355 52 3
                                    


https://www.wattpad.com/story/182867269?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_reading

October 1, 2020

JINI YA TSAGA.....👭

  ®NWA

Haƙƙin Mallakata
(©Oum-Nass)

page 11

   "Wannan itace godiyar da zaki min? Ko kuma wannnan shine kalar naki santin? Ki dai ci a hankali, kada daɗinsa ya ɗebeki har ki ƙwarai." Ya gama maganar yana murmushi da lumshe mata idanuwansa.

     Ɗago da kanta ta yi, tana kallonsa, ta sha jin ana cewa maza suna da saurin tashi da hassala idan mace ta kushe su, amma bata ga hakan ga Abdul-Mannan ba, domin shi ko alamun jin haushin kalamanta bai yi ba, balle ta samu wata ƙofar da zai nuna mata ta yi nasara akan sa.

    "Kana so kace baka ji haushin abin da na maka ba? Ko kuma so kake kace baka gane inda na dosa ba?"
  Kafaɗarsa ya ɗaga sannan ya taɓe bakinsa "Kin san ni bana iya rarrabe tsakanin magana mai daɗi da akasinta. Musamman idan a bakin mace ta futo, balle kuma matar da ta yi kwana ɗaya tal a gidan mijinta.
Ko wata maganarki mai daɗi ce da sanyi a gare ni Hafsat. Ba yan haka bana jin kunnuwana sun ji wani abu mai rauni a cikinsa."
   Ya ƙarasa maganar yana lumshe idanuwansa da kuma kai loma bakinsa, yana gyaɗa kai.

   "Abun da mamaki ace Malam Abdul-Mannan ne ya girka wannan haɗaɗɗiyar taliyar. To amma idan aka duba cewar girkinsa na farko ga haɗaɗɗiyar amaryarsa ne, wannan abin a jinjina min ne. A kuma yi koyi da ni." Ya sake maganar yana kurɓar ruwan shayi mai ɗumi kasancewarsa ma'abocin shan baƙin shayi.

    "Alhamdulillah ala ni'imatihi ta tumussalihat."
  Ya faɗa yana goge bakinsa da tushin da ke jikin table ɗin, sannan ya miƙe ya risina a dai-dai kunnuwanta.
    "Mata rahama ne ga mazajensu Hafsa, su ne kuma babbar kyautar da Allah kan bamu a duk tsawon rayuwar mu.
  A yayin da suka kasance uwaye a garemu da mataye, sannan masu hidima ga yaranmu. Su ɗin ne dai ƙashin bayan al'umma gaba ɗayanta.  Ba namiji ne yake zama bangon tsayuwa ga mata kaɗa ba, asalin kafuwar katangar tana ga matan da suka tafiya a tare da su.
  Ni kawai Abdul ne a tare da ke, ba zan iya zame miki wani abu ba, ba tare da kin ruƙo ƙafafuwana dan na tsayu a kan taku na ba.
  Sai dai zan ci gaba da shimfiɗa miki daular farin ciki a rayuwar aurenmu har sai kince ya ishe ki. Zan zama futular da zata haska gabanki, zan baki dukkanin kulawar da ya kamata har sai kinji a ranki cewar ni mijin da ya ke kawo farih ciki ne ga iyalinsa."

   Yana gama faɗar haka ya shige ya barta, yana jin idanuwanta na yawo akansa, yana fatan idanuwan da ke biye da shi su kasance masu aminci a tare da shi.
  A kai-a kai yake sauƙar da ajiyar zuciya, dan ya samarwa da zuciyarsa nutsuwa, domin ba kaɗan ba yake jin rashin daɗin kalaman Hafsat da kuma gwale shin da ta ke.
   Amma ya danganta hakan da rashin sabo da shaƙuwar da ke tsakaninsu, ya tabbata wata rana zai sauyata.

   ****

Kai ta jinjina tana ci gaba da cin abincinta, da ace bata jin yunwa da babu abin da zai sa ta ci abincin, sai dai kuma idan tayi hakan kamar ya ci bulus a kanta, kamar yayi nasara ne a kanta.

  Sai da ta cinye cikin filet har da ƙari, sannan ta kora da ruwan lemo. Tana lumshe idanuwanta saboda jin wata shawara da ta zo mata.

   A haka ta je ta kunna kallo a Tv da ke falon, abin haushi duk babu wasu toshar da za'a kalli 'yan zamani masu gwangwajewa, daga Sunna T.V sai Manara da sauran tashoshin wa'azi.

    Tashi ta yi ta shiga ɗakin Abdul-Mannan ta tarar da shi yana sa hula akansa, da farin hirami a wuyansa, duka kayan jikinsa farare ne.
    Yayi kyau ƙwarai, kamalarsa ta futo rangaɗau, ƙwarjininsa ya haura shekarunsa.
   Murmushi ya mata a lokacin da ta ƙaraso ɗakin "Ya aka yi ne Hafsa? Na ga fuskarki da damuwa."
   Idonta ta juya ta shiga yawo da ƙwayar cikinta cikin ƙwarewa irin tata.
   "Ina son ganin wani abu na nishaɗin da zai sa na manta da wanda nake zaune ne. Babu komi a gidan nan na farin cikin da mutum zai iya mantawa da abin baƙin cikin da ke damunsa.
   Ba zan iya zama a cikin wannan rayuwar ta gidadanci ba Abdul."
Murmushi ya yi a lokacin da ya gama jin maganarta, sannan ya ɗauko mata Alƙur'anin da ke jikin lokar litattafansa ya ɗaura mata shi akan hannunta.

   "Babu wani abin nishaɗin da zaki nema a duniya ba tare da kin same shi anan ba Hafsa.
  Komi da kike son sani na rayuwa jin daɗi da zai shagalar da ke ƙuncin da kike ciki zaki same shi anan."
  Sannan ya juya ya ɗauki turarensa ya fesa, da ɗaukan  Litattafansa ya shige ya barta.
  "Na tafi masallaci, daga nan zan tsaya na yi karatu da ɗalibaina, in sha Allah zuwa yamma zan dawo."

   Shan gabansa ta yi tana kallonsa wanda ya sa shi tsayawa shima yana kallonta.
  Idanuwanta ta sake shigar da su ciki "Ranar farkona a gidan naka ne zaka futa tun sha biyu kace ba zaka dawo ba sai Yamma? Idan ka tafi kuma wa zai min abincin ranar, ka dai san bani da lafiya, ƙasusuwana duka basu dawo dai-dai ba balle nace zan yi girki."
  Idonsa ya wara yana kallonta, da mamaki akan fuskarsa "Yanzu har kina maganar wani abincin bayan ko mintu goma baki yi da cin wani ba?"

  Idonta ta fiddo waje "Ba dai horon yunwa zaka min a gidanka ba Abdul? Ba dai so kake kace kana rukunin Uztazan da suke haramta cin abinci ba? Ta ya zan iya jure ɗaukan nauyinka a kaina idan har sau biyu zanna cin abinci a rana?
   Oh na gane! So kake ka haramta min cin abinci sau uku, saboda kai zaka futa kana ciye-ciyenka a mumbari. Ni ba waliyiya ba ce Abdul. Idan har ba zaka iya ciyar da ni ba, to ba zan iya ci gaba da zama da kai a gidan nan ba."
  Ta ƙarasa maganar tana juyawa da barin ɗakin, kamar soko haka ya tsaya yana binta da kallo bakinsa a buɗe, bai san ta ina zai iya da rikicin Hafsa ba kuma yanzu.

  Sai dai kafin ya dawo tunanin da yake, ya hangota janye da jaka tana faman janta.
   Da sauri ya ajiye litattafansa a table ya nufeta, ya riƙe jakar.
  "Ina zaki da wannan uwar jakar kuma Hafsat?"

  "Duniya zan shiga Abdul-mannan. Duniya zan shiga tun kafin ka kashe ni da rai na. Dan nasan ban isa zuwa gida da sunan yaji ba, gara na je inda ba'a san ni ba a amshi baƙunta ta.
Dan wallahi ba zan zauna da ciwo biyu ya kashe ni ba, baƙin cikin aurenka da kuma horon yunwarka."

     "Haba mana Hafsat! Me ya yi zafi abin maganar baki kuma. Shikenan ki yi haƙuri ki maida jakar, idan an idar da sallah zan dawo na miki girkin da kike so kinji."
   Ido ta wurga kamar ba zata juya ba, ganin hakan ya amshi jakarta ya shige da ita ɗakin nata, ya ruƙo hannunta ya zaunar da ita akan kujerar.
   "Ki yi haƙuri Noorie, ba zan daɗe ba, ana idar da sallah zan dawo. Zan ba su haƙuri yau ɗaya nasan za su min uzurin basu karatun.
  In sha Allah zan zo na girka miki abin da kike so.
  Ko kuma na siyo miki wani ne mai kyau a gidan abinci?" Ya ƙarasa maganar yana kwantar da muryarsa.

  "Taɓɗijam! Ni Hafsa ce zan ci wani abincin waje? Abincin da ban san su waye suka girka ba? Ai gara na shiga duniya na ga wanda suke yi. Idan ya so na siya da kai na."
   "Shikenan! Abun bai kai haka ba. Zan dawo sai mu shiga tare kina gani ina girka miki ma."

  Idonta ta wurga waje "Yanzu naji batu kam."
  Daga haka ya fuce yabar gidan, yana jin ƙafafuwansa kamar ba za su ci gaba da ɗaukansa ba.
   Sai da ta ga fitarsa sannan ta kwashe da dariya.
   "Muje dai zuwa! Da kanka zaka gaji ka sake ni, sakarai ko wa ya faɗa masa duk tijarata zan iya shiga duniya? Nasan me zan gani a cikinta." Ta yi maganar tana bushewa da dariya.

  🌷🌷🌷🌷
Sai fa kuna haɗawa da haƙuri, saboda rubutun yanzu na ƙoƙarin gudu ya barni.

   Wattpad @Oum_Nass

JINI YA TSAGAWhere stories live. Discover now