BIYAR

1.2K 110 22
                                    


HAƘƘIN MALLAKATA
  
   July, 26, 2019

JINI YA TSAGA......👭

© by Um-Nass

  ®NAGARTA WRI.ASSOCIATION

  Dedicated by :Sady Jegal

PAGE 5

Shuru Adda Halima tayi, taci gaba da kallon wayar tana jujjuyata  bayan ya tsinketa daga kiran.

ta ko ina gumi ne yake tsatssafowa ajikin ta. 'Tabbas ta san wacece Hafsa, zata aikata fiye da abin da Kawu ya faɗa. Amma bata ɗauka lamarin nata yayi juyin uwar ba'u ya koma har kan Alhaji Malam ba, amatsayin sa na babban malami agarin wanda mutane suke bashi girmamawa, suke kambama tsagwaron alkhairin sa agare su. Ta gefe guda kuma ya zama silar wanzuwarta acikin wanan duniyar.'

"Ya ALLAH!" Ta faɗa tana shafo fuskarta da duka tafukan hannun ta.
sanan ta ɗauki tunanin ta ta cillashi can baya, a lokacin da mijin ta yake raye.

  ******
BIRNIN KEBBI
JEGA L.G

10April 2008

"An ɗaura Auren Hafsat Kamaludden Muhammad, da Angonta shugaban Hisbah na jahar Sokoto Sheikh Abdul-mannan Isyaku, akan sadaki Dubu Ashirin lakadan ba ajalanba."

   Wani maɗaukin lasifa ya faɗa yana nanatawa, yayin da mutane da yawa suke hamdala da kuma musayar hannu wajan yin musabaha a tsakaninsu.

   Tabbas wanan shine ɗaurin auren da ya tara manyan malamai da kuma 'yan hisbar dake jahar. Wasu ma ba daga jahar suke ba, amma saboda kasancewar jigon Hisbah agarin yasa suka masa kara suka zo.

Gefe guda kuma shi kansa Mahaifin Amaryar Kamaludden babban malami ne agarin, wanda yake sahun manyan da sukan faɗa aji.

Tabbas Ilimi baiwa ne, akwai kuma tausasawa da taimakon mutane atare da shi, ba kawai ilimin zaka kwasa agareshi ba, idan ka zauna da shi koda sau ɗaya ne, zaka ribata da tarin alkhairansa.

  "Alhamdulillah!" Itace kalmar da yake ta nanatawa akan bakinsa.
  Wanan shine babban burinsa a rayuwa, duka yaransa su auri malamai masana addini da kuma haƙƙoƙin zaman-takewa ta aure. Wa ɗanda suke da kyakkyawar mu'amula da mutane.

Sai gashi Allah ya cika masa fatansa da burinsa, duk da Hafsa rikitacciya ce acikin yaransa, amma yasan zaman aure zai iya gyara mata rayuwa, musamman da ya kasance mijinta yana da haƙuri masanin addini kuma.

Abinci akayi ta fitowa da shi daga cikin gidan ana ajiyema 'yan ɗaurin auren.
  Kafin wani lokacin wajan ya zama dan-dalin cin abinci, kowa fuskarsa ɗauke da maɗaukakiyar fara'a na samun gamsasshen abinci.

  *****
Daga cikin gidan kuma mata ne, suke nasu budurin, da yawa Matan gidan suna murna akan Hafsat zata barsu susha iska, shi yasa komi da hanzarinsu suke yinsa.

    "Hafsa! Ina so ki ɗauki wanan auren naki a matsayin ibada. So nake mutane susha mamakinki Hafsa. Kowa cewa yake fitinarki ba zata bari ki zaunaba, amma ni ina da kyakkyawar sheda akan ɗiyata."

  Ɗagowa Hafsa tayi tana kallon Mahaifiyar tasu, yanayinta bai yi kama dana mai damuwa ba, asalima ba zaka ban-bance abin dake damunta ba.

  "Umma! Ban san taya zan zauna da mutumin da babu ƙaunarsa ko kaɗan a ƙasan zuciyata ba? Kin sani ba'a sani abun da banyi niyaba, Alhaji Malam yayi kuskure da yake ganin nima zai tilastani ne kamar yanda yakema su Addah Halima.

Allah ya sani babu auren ustazi acikin rayuwata ba, wanda kullum hidimarsa akan mutane ne da warware musu matsalarsu."

  Cikin sigar lallashi Umma take mata magana "Kiyi haƙuri, bawa baya wuce ƙaddararsa. Mahaifinki shike da hakkin zaɓar miki miji na farko, haka ya duba can-cantar wanda ya aurar miki. Samun kamar Abdul-mannan awanan duniyar ba abune mai sauƙiba.

Kamata yayi ki ɗaga hannu ki godema Allah a bisa ni'imar daya sauƙar gareki, ya baki mahaifi masanin Alqur'ani ƙarshe ya baki miji kwatan-kwacin mahaifinki."

  Cire hannun Ummanta tayi daga kan kafaɗunta, tayi murmushi tana cizan laɓɓanta "Wanan shine takaicinah ai Ummah. Samun miji mai irin ɗabi'un Alhaji malam, ni banga alkhairin da kike ta yaɗawa akansu ba.

Har yanzu ban manta dalilin rabuwarku da Alhajinmu ba Ummah. Idan har ya rabu dake saboda ɗan kuskure ƙarami ya kike ga Abdul-mannan zai aikata agareni."

  Hannu Umma ta ɗaga mata cikin ɓacin rai ta fara magana, dan Hafsan nata ba sauƙi akwai murɗaɗɗan hali da taurin kai, ga rashin mantuwa.

  "Ƙaddarar zamanmu ce ta ƙare tun awancan lokacin, da kuma rabon su Al'ameen daya raba atsakani.
  Hafsa babu wanda baya aikata kuskure a rayuwarsa, ɗan-Adam ajizine. Har gobe bana ganin laifin mahaifinki, tunda gashi har yanzu muna tare ba'a rabu ba, kuma ina alfahari da kasancewarsa mijina awancan lokacin."

Miƙewa Hafsa tayi tana kaɗe zaninta "Haka kullum kike faɗa dan ki kareshi. Amma ni zuciyata taƙi yafe masa da yi mana katanga da mahaifiyarmu.

Zan gasawa mijin da yayi gigin aurena aya ahannunsa, har sai ya gaji ya rabu dani.
  Babu miji atsarin rayuwata Ummah, babu ƙaunar hakan araina."

  Tana gama faɗar haka ta fice tabar mata ɗakin.
Dafe kai Ummah tayi hawaye na bin kuncinta "Ya Allah!"
  Ta faɗa akan laɓɓanta.

  Wanan kuskurensu ne da suka aikata ita da Alhaji Malam. Ita tayi kuskure a matsayinta na mace mai rauni.

Shi kuma a matsayinsa na namiji masani ya kasa danne ɓacin ransa, har ya aikata abin da Hafsa take ganin laifinsa ne.
  Take kuma ganin baikinsa akan hakan.

🌷🌷🌷🌷🌷🌷

  _Ya kuke gani akan dawowar labarin  JINI YA TSAGA bayan shuɗaɗɗan lokacin da aka ɗauka?_

  Idan har yanzu akwai ra'ayinku akansa, ku ajiye mutuntakarku, zan ƙoƙarta na shimfiɗa kowacce Girmamawar dake gareni, koda sau biyu ne zaku iya samunsa a mako guda.

#JiniYaTsaga....
#NWA
#DaAmana
#Girmamawa

   ©by Oum-Nass

JINI YA TSAGAWhere stories live. Discover now