TAKWASS

469 62 11
                                    

HAƘƘIN MALLAKATA

August 10, 2020

JINI YA TSAGA.....👭

®NWA

©Oum-Nass

page 8

"Dama duk wanda ya sayi rariya yasan zata zubar masa da ruwa. Ni kaina nasan ba zaka iya siyan abu mafi girma ba sai ka tsaya kana zaɓen ƙarami dan kace abu ƙarami shine mai lada.
Kamar dai yanda kullum kuke cika mutane da wa'azinku." Ta ƙarasa maganar tana yankar cinyar kaza a bakinta.
Ƙarasawa yayi kusa da ita, fuskarsa ɗauke da murmushi ya zauna a kusa da ita, yana harɗe ƙafafuwansa, da kuma ɗaukan kofin lemon da ke gabanta, ya kurɓa.
"A tarihin rayuwata ban taɓa jin labarin Amarya ya zauna tana cin kazar aurenta ba kamar ke.
Koda ace ta ci ɗinma tana cine ta sigar lallashinta da kuma yi mata magiya, amma sai gashi ke ba'a miki tayiba ma kin hau cinta." Abdul-Mannan ya faɗa yana murmushi.

Ɗago da kanta Hafsat tayi tana murmushi itama "Shi yasa kenan ka siyo kaji ƙanana dan kana da labarin amare basa cin kajin aurensu?"
Kansa ya girgiza har a lokacin murmushi na kwance akan fuskarta "Na siya ne dai-dai da aljihuna."

"Uhm Sheakh Abdul-Mannan amma duk labarin da ka samu na ƙin cin kazar amarya, hakan baya hana asha romonta koda ace bata ci daga abun da aka sunnanta ma angonta bata shi ba."
Idonsa ya waro yana kallon Hafsan da itama shi take kallo fuskarta ɗauke da murmushi.
"Hafsat wai bakya jin kunyata da nauyin faɗar ko wata magana a gabana?"
"Idan naji kunyarka da wa zan yi magana? Bayan a yanzu duniya ta sheda mun zama abu ɗaya ni da kai.
Komi nawa daban yake Abdul-Mannan, ban yarda na yi rayuwar gidadanci da aron halayyar da ba tawa ba."
"Kina so ki ce min wanan shine zahirinki?"
Kai ta gyaɗa masa tana lumshe ƙanannun idanuwanta "Komi da ka ga a tare da ni nawa ne! Kana so kace min ba'a baka labarin ko wace ni ba ka yarda ka aure ni?" Ta ƙarasa magana tana tauna ƙashin haƙarƙarin kazarta, wanda ta cinye ta tas.

"Yaushe rabonki da ki ci kaza?" Ya tambayeta yana murmushi da ƙoƙarin sauya hirar tasu.
"Daƙiƙa ɗaya da ta wuce." Ta faɗa tana dariya.
"INa nufun kafin yau."

"Da yake dai gidanmu na malamai ne kullum akanyi ƙoƙarin maida baƙin yawu. Amma ban saniba ko almajiri na samun damar ci kullum kamar yanda malaminsa ke ci."
Ta faɗa tana goge bakinta da tushu ɗin da ke kan table ɗin gabanta, sanan ta ɗauki ruwan lemo ta sha.
"Nagode da ka sunnanta abun da aka sanar da ku. Saura kuma ka tambaye ni akan abun da ya shafi addinina."
Bai kalleta ba ya janyo sauran kazar da ta rage masa, wuya ne sai kuma makafakin kazar da ta barshi, amma duk ta cinye kazar har guda biyu.
Kallon Hafsat ɗin ya sake yi da mamaki wanda ita bata san me yake ba, dan ta naɗe akan kujerar da ke palon nasu.
Ruwan lemon ya kurɓa sanan ya tattare naman ya shigar da shi kitchen ɗinsu.
Har ya dawo tana zaune bata motsa ba "Ki je kiyi alwala za muyi sallah."
"Ina da alwalata."
Tsayawa yayi ya kalleta "Duk tauna kajin da kika yi da sakin layin da kika yi amma kice min kina da alwala?"
Tashi tayi ta shige ɗakinta ba tare da tayi masa magana ba, shima nasa ɗakin ya shiga sanan ya girgiza kansa, al'amarin Hafsa sai ita. Amma kuma duk abun da tayi bai ji ransa ya ɓaci ba, asalima ji yayi wata sabuwar ƙaunarta na shigarsa, dan ya fahimci harda ƙuruciya ce ta ke damunta.

Bayan ya shiga ɗakinsa ya cire kayansa ya shiga wanka, daga nan ta ɗauro alolarsa, ya saka doguwar zaleka fara ƙal a jikinsa, bayan ya shafe ko ina na jikinsa da mai da kuma turare. Abdul-Mannan mutum ne ma'abocin ƙamshi da son turare, baya sake da ƙamshi da tsaftar jikinsa.
Cikin nutsuwa ya futo ya nufi ɗakin da Hafsat ɗin take anan ya sameta ta futo daga wanka itama, tana sanye da ɗan ƙaramin tawul a jikinta, wanda iyakarsa gwuiwarta, santala-santalar cinyoyinta sun futo farare da su.
"Ya Rabb!" Ya faɗa lokacin da yaji wani abu ya tsirge masa tun daga tsakiyar kansa har zuwa yatsan ƙafarsa.
"Wai dama haka malaman suke su shigowa mutane ɗaki babu sallama?" Ta faɗa tana harararsa da murguɗa bakinta, yayin da ta ja dogon hijabinta ta zurma a jikinta.
"Idan kinsa kayanki ki zo ɗakina ina jiranki." Ya faɗa yana fucewa a ɗakin.

Baki ta taɓe ta ɗauko wata doguwar riga marar nauyi ta sa a jikinta, bayan ta shafa manta mai ƙamshin daɗi, kaɗan ta fesa wani turare da Adda Halima ta bata shi.
"Ni a duniya ina mamakin wanan tsarabe-tsaraben da su Adda Halima suka sani. Komi ace ayi idan miji ya kiraka, kada ka tafi babu ƙamshi.
Wallahi da ace banda wani shiri akansa da babu wanda ya isa ya sani na tsaya ina ɓatawa kaima lokaci. Kana ganinsa da shanyayyun idonsa ya iya shigowa ɗakin mace babu sallama." Ita kaɗai take magana kamar zata tashi ɗakin saboda masifa ta fice ta shiga ɗakin nasa.
Sanda taje ɗakin har ya shimfiɗa musu sallaya hakan yasa ta hau ba tare da ta masa magana ba.
Shima bai tanka mata ba, dan har a lokacin yana jin jikinsa babu laka.
Raka'a biyu ya jasu daga nana ya shiga karanto musu Addu'a tana kiran Ameen. Yanda yake zazzago larabci abun sai ya ɗan birgeta kaɗan, duk da ta san ko waye mijin nata. Shafawa yayi itama ta shafa, kamar gaske.
Daga nan ya juyo ya ɗora hannun damansa akanta ya shiga yin wata sabuwar addu'ar, jikinta ne taji yayi sanyi tana jin ko wata ƙofar gashi na jikinta na buɗe, wani sabon tsoro na ratsa zuciyarta.
Tsoron abun da bata san ko na miye ba, ga kuma sanyin da ko wata laka ta jikinta yayi.
Sai da ya gama sanaan ya shiga tambayarta akan abun da ya shafi addininta tun daga sallah da kuma karatunta.
Yasha mamaki da yaki ko mi ya tambayeta ta sani, duk da cewa yasan waye mahaifinta, ya kuma san tsayuwarsa akan addininsa da ma rayuwar yaransa.
Ajiyar zuciya ya sauƙe "Alhamdulillah! Madallah da samun mace ta gari." Ya faɗa yana ɗaukarta a hannunsa kamar wata jaririya wanda yasa Hafsat buɗe idanuwanta tana kallonsa.
Idonsa ya kanne mata guda ɗaya "Amaren da basu ci kazaba ma ana shan romonsa. Ya kikaga amaryar da ta ci kaza har ta tauna ƙashinta?"
Baki ta buɗe da niyar magana sai dai hakan ya gagara domin tuni ya shigar da bakinsa cikin nata, ya kuma kashe musu futlar da ta haska ɗakin. .

ASUBA TA GARI HAFSAT

🌷🌷🌷🌷🌷

#JiniYaTsaga
#NWA
#Cmnta,vote,share
#GIRMAMAWA

OUM-NASS

JINI YA TSAGAWhere stories live. Discover now