TARA

355 61 10
                                    

HAƘƘIN MALLAKATA (Oum-Nass)

September 19, 2020

JINI YA TSAGA......👭

®NWA

  page 9

Ta daɗe tana jin labarin maza da ƙumajinsu, amma bata yarda cewa  kamar Abdul-mannan zai iya sa ƙarfi ya keta ta ba, kamar yanda sauran mata ke bada labari.
  Ta yi takaicin zamo warta a matsayin jinsi mai rauni da ta kasa hana Abdul-Mannan kaiwa ga buƙatarsa ba, ta yi kuka ya fi sau a ƙirga, ta wanke jikinta da dirza shi da sabulu kamar zata sauya fatar jikinta.
     Sai dai bata daina jin zafin da ke ratsa jikinta ya sauƙaƙa ba. "Tabbas da sa ke." Ta faɗa tana share hawayen kan fuskarta.
  "Ya yi kusa ace na fara zubar da hawaye na akan ɗan wannan al'amarin."  Ta faɗa a karo na biyu a lokacin da take zubawa kanta ruwa.
   Ta futo daga toilet ɗin daga ita sai ɗan guntun tawul a jikinta, a lokacin shi Abdul-Mannan yaana tsaye akan abun sallah yana gabatar da sallar dare.
   "A haka kamar waliyi." Ta faɗa tana wuce shi da raɓawa ta bayansa.
  Ɗakinta ta shige ta saka doguwar rigar barci, sannan ta bi lafiyar gado, har a lokacin zuciyarta bata daina tafasa da abun da Abdul-Mannan ya mata ba.
    "Ashe dai mazan haka su ke a riga." Ta faɗa tana tuno kalar azabar da ta sha. 
  "Ni kuwa idan ban gasawa Wannan mutumi aya a hannuba me na yi kenann a duniyar?" Ta sake faɗa  tana ƙwafa anan barci ya ɗauketa tana saƙa da ƙullu na mugun zare.

     Asubar fari ta ji Abdul-Mannan na tashinta, yana buga fulon da take kwance a kai "Hafsat! Hafsat ta shi kinji asuba ta kawo kai." Ya faɗa yana sake bibbiga fulon nata.
   "Haba mana Abdul! Duk kalar azabar da ka min a daren nan bai ishe ka ba sai ka zo ka tashe ni ka hanani barci."
   "Lokacin sallah ne ya yi, ki tashi ki yi ni zan tafi masallaci."
   "Oh to ni sai ajima zanyi, dan har yanzu ƙasusuwana ba su dawo daga raguza sun da ka yi ba.
  Shine dan kinibibi ka sha rawani a kai kamar ba abun da ka iya." Ta faɗa tana yamutsa fuskarta da jan bargo tana lulluɓai kanta.
   "Ni ne na ke Kinibibin Hafsa?"
  "Akwai wani mai rawanin ne bayan kai. Ni ka tafi ka hananin barcin wahalar da nake." Ta faɗa juya masa baya.
  Kai ya girgiza ya fuce a ɗakin a zuciyarsa yana mata Addu'ar neman shiriya.
    Har yaje masallaci ya dawo tana kwance, lokacin gari ya fara haske domin sai da ya tsaya ya yi wa'azi sannan ya dawo.
  Da mamakinsa bai ji motsinta ba, hakan ya sa ya shiga ɗakin nata  ya sameta har a lokaci tana duƙunƙune a cikin bargon.
  Bai ce mata komi ba ya ajiye rawaninsa a gefe, sannan ya cire jallabiyar da ke jikinsa, ya rage daga shi sai wando iya gwuiwa da kuma  shimi.
  bargon ya janye a hankali sannan ya cicciɓeta ya ɗauke ta shigar da ita toilet, ya sa ta a cikin ruwan da ke ƙaton baho.
  A furgice ta buɗe idanuwanta tan  kiran "Wayyo Allah!" Ganin Abdul-Mannan a gabanta ya harɗe hamnu a ƙirji yana dariya yasa ranta ya ƙara ɓaci.
  "Abdul kashe ni kuma kake son yi bayan notunan da ka gama kunce min a daren jiya?"
  Kai ya girgiza "Lokacin sallah ya wuce Hafsat. Zan iya jure komi a wajenki amma banda sakaci akan ibada."
  "Aikuwa da sake an bawa mai rago ƙafa.
   Abdul ka shirya rigima da ni kenan?"
Kafaɗarsa ya ɗage "Na shirya dai zaman aure da ke Hafsat, cikin daɗi da rashinsa, domin ina sonki sosai." Ya faɗa daga haka ya juya ya barta a banɗakin.
  Kitchen ya wuce kai tsaye ya fara musu abin kari, duk da shi ba wai gwani ba ne wajen girki amma dan ya birge Hafsa ya fara kokawar fere dankalin turawa, garin ferewa ya yanke hannunsa da sabuwar wuƙa, ya fara yarfe hannunsa saboda azabar da ya ji.
   Amma duk  da haka bai haƙura ba, ya wanke jinin ya ɗauko bandeji ya rufe ciwon, wajen suya ma mai ya yi ta ƙona shi, amma sai da ya gama, a suyar ƙwai kuma ya ɓata lokaci, dan bai san me ake sawa a soya ba, ganin dai yaana ɓata lokaci ga bai ji motsin gimbiyar tasa ba kawai sai ya soya shi haka.
Ya kashe gas ɗin bayan ya tafasa musu ruwan  sai fara'a yake, a ransa yasan yau ya na da ladan sanya matarsa cikin farin ciki. Zai kuma mata ba zata.
   Ɗakinta ya shiga ya ganta ta ci uwar kwalliya cikin atamfa riga da siket, ɗinkin ya bi jikinta ya sake futo da kyanta ƙwarai, kasancewarta mace  kyakkyawa mai diri.
    "Masha Allah, kin yi kyau sosai Uwargidana." Ya faɗa yana ƙarasawa kusa da ita.
  Fari ta yi da idanuwanta tana yawata shi, sannna ta kalle shi "Na daɗe da sanin ni kyakkyawace Abdul."
   Kansa ya gyaɗa kamar dolo "Kayan sun miki kyau." Ya sake faɗa a karo na biyu.
  Hannunta ɗaya ta ɗaga ta fara girgiza yatsanta manuni "A'a ba kayan ne suka min kyau ba Abdul, ni ɗin ce dai na musu kyau."
  Ta faɗa tana takawa cikin salo da yanga, duk jikinta na jujjuyawa, sannan ta ɗaga hannunta tana nuna jikina "Ko makaho ya laluma ni yasan kaya su ke buƙatar irin jikina Abdul Mannan."
  Kansa ya gyaɗa yana tasbihi da shu'umancin Hafsat.
   "Masha Allahu la ƙuwwata illa billahi. Ko da muna da kyau ance mu suturce jikinmu. Duk kuma gadararmu akan kyau ɗin ba za mu yi yawo tsirara ba.
  Kinga kenan mu ke buƙatar kayan ba shi ke buƙatarmu ba." Ya yi maganar da murmushi akan fuskarsa.
   "Shima zai buƙa ce mu Abdul."
"Zo mu je ki ci abinci, sai mu yi magana akan hakan." Ya ruƙo hannunta suka futo har zuwa gaban daining fuskarsa ɗauke da fara'a ya ja mata kujera ta zauna.
  Sannan ya fara zuba mata abincin, tana ganin abinci ta fara jin cikinta na hautsinewa.
   "Wannan me ye AbdulMannan?"
"Soyayyan dankali ne." ya faɗa yana ɗaga shi."
   "Turƙashi wannan ai sai dai a kira shi da baƙin gawayi..." Ta faɗa tana rufe bakinta saboda ƙarnin da ƙwan da ya cika mata hanci.

   "Wannan ƙwan ruwa ne ko na sarari  ya addabe ni da ƙarni? Kai Abdul ba zaka kashe ni da wannan cimar ba." Ta faɗa tana tashi ya bita da kallo...

 
🌷🌷🌷

IDAN VOTE'S NAKU YA YI YAWA ZAKU NA SAMUNSA KULLUM IN SHA Allah.

JINI YA TSAGAWhere stories live. Discover now