chapter 1

4 1 1
                                    

              🌈 *AKILA* 🌈

*Elegant online writer's*

Paid book
*بسم الله الرحمن الر حيم*

*In the name of Allah,the most gracious, most merciful.
Praise be to Allah the cherisher and sustainer of the worlds.
Most gracious most merciful.
Master of the day of judgement.
You alone we worship and your aid alone we seek.
Show us the straight way.
The way those on whom you have bestowed your grace and whose ( partion) is not wrath and who go not astray. "Amin"*

Chapter 1

Cike da izzah yashigo office din sanye da uniform nasa na sojoji" da sukayi matukar  amsar fatar jikinsa.fuskarnan tasa a murtuk'e, hakan be hana kyawunsa bayyana ba" k'amewa yyi tare  da  buga kafafunsa a kasa ya sarawa ogan nashi cikin girmamawa ya ce, " Sir"  ogan ma k'amewa yyi fuska murtuk'e ya ce, " General Maleek Abubakar. kashiga hurumin da ba naka ba, kasan  Abu khal Babban dan ta'adda ne   a garin nan zakaje ka harb'esu dashi da mutanen sa  bayan k'asan daurin gindin da yake dashi why?" Cike da izzah ya ce, "Sir Abu khal bashi da amfanin a kamashi domin ba abunda za'a iya masa face a tsakesa kuma shima ya kashe mana mayyan Sojoji sama da goma, shine na harb'eshi idan an nemi korafi ace a musayan wuta aka harb'eshi.
Maleek.... ogan nasu ya fada a sawace kai gaka mai zuciya ko?" Sorry Sir" ya fada tare da kara k'amewa,  mika masa wasu takardu yyi ya ce," General Maleek Abubakar an dakatar da kai har sai lokacin da aka nemeka" karbar takardun yyi ya Sara masa tare da juyawa yabar office din zuciyarsa cike da bakin ciki idan ba haka sukeyiwa  yan ta'addan ba yaushe za'a rage miyagun mutane masu ai kata barna a k'asa.....tsaki yaja lokacin da ya isah masaukin sa, hada kayansa ya farayi sbd ya gudirta a ransa bazai kwana a garin ba, yana cikin hadawanne wani picture dinsa shida wata kyakyawar yarinya ya Fadi daga jakar, a hankali ya sanya hannayensa ya dauko pic din yana murmushi mai hade da bakin ciki tunawar da yayi da abunda ya faru shekaru biyar da suka wuce, idanunsa ya lumshe na wasu minutes ya bud'esu lokaci daya fararen idanunsa ya koma j'a. ajiye pic din yyi ya k'arasa hada komai nasa ya dauke kayansa ya shiga toilet  din dake wajen ya shirya cikin wando jeans black and white t_shirt sai white cap daya sanya saman sumar kansa ya fito  sosai kyawunsa  bayyana ba duk da fuskarnan a d'aure tamau....jakarsa ya rataya ya fita daga wajen ya shiga Motan yabar wajen da mugun gudu.....Sir Jabbar na tsaye nesa da d'akin nasa ya hangoshi ya fitoh baiji dad'i ba duk da har ransa bai so dakatar dashi ba but ba yanda ya iya domin bayason ya fuskanci wani masalar a masayinshi na kwarairai Soja daya iya harbi da aiki tukuru.

             Had'add'iyar yarinya ce ajin karshe take sakkowa daga kan stairs din fara kyakkyawa wacce bazata wuce kimanin shekaru 25 aduniya" tanada k'ira mai daukar hankali, kallo daya zaka mata kasan ilimin, aji, izzah suna yawo ajikinta.
K'arasa saukowa parlor tayi fuskarta dauke da murmushi yarinyar d'ake zaune saman cinyar wani kyakykyawan guys dake zaune Saman kujeran, tayi kissing dinta a goshi ta ce, "Babyn tashi mu tafi kada ki biyewa Daddy mu makara ko" murmushi mutumin yyi ya ce," sweetheart wlh keba  akoi ki da rigima yanzu dole sai kinje meeting dinnan ke da AkILA" murmushi tayi  ta ce,"   no dear kasan banason in rinka nisa da ita,gashi kai ma fita zakayi" ta fada cikin shuwgub'e fuska, murmushi yyi ya ce," toh ai nima haka banason habuwa daku but dole mu rabu din, ki tafi da security ko escorts please, d'aga yarinyar daga cinyarsa tayi ta ce, " Daddy n AkILA kasan ni ban cika son irin waen nan abubuwan ba nafiso nayi diving daga ni sai yata, kaga zamu biya shagon ice cream ma na saya mana" ta fada tana masa gwalo" mikewa yyi yana murmushi ya  shafa kan AkILA ya ce," Babyn sai mun sake haduwa ko" murmushi kawai itama tayi ta ce" bye " ta fada suna ficewa d'aga parlor. Shima yana murmushin ya ce," bye". Suna fita drive ya bude mata back sit ta ajiye AkILA ta ce, " ya rufe murfin ita zatayi diving da kanta, saurin rufewa yyi ya bude mata ta shiga ya rufe murfin ya mata a dawo lafiya taja Motar ta fita d'aga gidan.
Diving take cikin kwanciyar hankali AkILA  Kuma na wasa da doli_dolin yara a baya. Hango wani black cat daya masa mata da hon tayi  cikin madubi, tsaki tayi ta bashi waje ya wuce taci gaba da tafiyar ta har ta isoh shagon ice cream tayi parking ta fitoh ta rufe  AkILA cikin Motar, ta shiga shagon ice cream din ta saya musu ta fitoh rike dashi a hannunta tana murmushi ta bude Motar tanà kokarin shiga taji an fisgota da karfi a ka kai mata wani wari da ya sa kanta buguwa da Motar take jini ya balle mata ta fadi kasa, wasu katti mutane hudu ta gani dukan su fuskokinsu rufe da bakin kelle baka ganin komai sai idanunsu, daya daga cikin su dake rike da wani karfe ne ya fara  buga mata shi a jiki har tayi laushi ko yasarta bata iya dagawa, bude Motar sukayi suka dauki AkILA data fara bacci, kokarin mgn da daga hannunta  take amma ta kasa, a haka tana ganinsu har idanunta ya rufe bata sake ganin inda take.

Suna daukarta suka shiga Motarsu da ita suka bar wajen. mutanen wayen na ganin wuce warsu sukajo kanta da gudu nan take suka kira yan Sanda da Motan asibiti aka dauketa a ciki.

(Yanda duniyar ta koma kenan ko ana kashe mutun a gaban jama'a ba wanda zai ce komai kanaji kana Gani a gabanka, kai Allah ya kawo mana zaman lafiya a k'asarmu Amin)

   Direct asibiti suka wuce da ita suna isah aka wuce emergency room aka shige da ita  ganin bata numfashi sosai Likituci suke iya bakin kokarin su a kanta na gani ta farka amma shiru" tana cik'in kila wa kala" har yanzu basu tabbatar da ta mutu ko tanaraye b.........!

Wannan littafin na kudine normal group 300 post ba kullunba. Vip 500 PC 1k zaki turu kudin ki ta wanan asusun 0431560118 fadimatu Babangida gt bank screenshot ta wanna number 07061204735 ko katin MTN thanks ❤️ ❤️❤️

Comment and sharen fisabilliah

🌈 AKILA 🌈Where stories live. Discover now