chapter 3

0 0 0
                                    

🌈 *AKILA* 🌈

*Elegant online write's*

Paid book

بسم الله الر حمر الر جيم

In the name of Allah, the most gracious, most merciful.
Praise be to Allah the cherisher and sustainer of the worlds.
Most gracious most merciful.
Master of the day of judgement.
You alone we worship and your aid alone we seek.
Show us the straight way.
The way those on whom you have bestowed your grace and whose (partion) is not wrath and who go not astray." Amin"

Chapter 3

Ya ce," suci gaba da in ƴin bincike yana dawowa.
daya daga cikin security ne ya ce," but Sir bai kamata ka tafi kai kadai ba t....... mgnr tsayawa yyi a makoshinsa tsakamakon wani kallo da Daddy AkILA ya jefeshe dashi ya ce," wannan ba abunda ya shafeka bane. "sorry Sir ya fada yana tsara masa, baice komai ba ya ja Motarshi ya bar waje.

A hankali ya shiga cikin gidan tun abaƙin gets security suke sara masa da mamakin ganinsa a wannan lokacin da basuyi sammanin ganinsa ba.
BALA mai gad'i kuwa mutseke idanusa ya farayi yana mamakin baki sake ya ce," ranka ya dad'e da gaske kai nake gani ko dai mafarkin dana sabane?" Murmushi kawai Maleek yyi ya wuce cikin.
wani nannauyan ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya shige cikin parlor bakinsa dauke da sallama ya shiga ganin ba kowa ya sashi shigewa part dinsa ya bude ajiye jakarsa ya wuce toilet ya watsa ruwa ya fitoh ya shirya cikin wando da riga da yyi masifar yi masa kyau, parlor ya sauko ya samu har BALA ya musu shelar dawowarsa gaba dayansu sun fitoh, da gudu kannensa mata biyu suka rungumesa suka fashe da kuka farincin dawowar dan'uwansu murmushi ya daga su daga jikinsa ya share musu hawaye ya ce," kukan fa name toh?" cikin shugwub'a sukace toh Yaya ba kai bane ka tafi ka barmu" murmushi yay ya ce," toh ba gani na dawoba sai ku daina kukan shugwub'anbun Ummi watoh kun girmanma bazaku bar rigiman nan naku bako?" dariya suka sa a tare sukace ba wani har yanzu da sauran mu, murmushi kawai yyi ya wuce wajen tsohuwar dake zaune saman kujera fuskarta dauke da murmushi zama yyi gefenta ya rike hanayenta ya ce," Yar tsohuwata da fatan na sameku lafiya?" kansa ta zungura ta ce," lafiya kalau shine daga tafiya ka manta damu haba Maleek abunda kayi ya dace sbd da Allah, Kansa ya tsosa ya ce," am sorry matar yanzu ba gani na dawoba gaskiya nayi kewarku sosai" ba waninan da kayi kewarmu dakazo shekara nawa yanzu bakanan? karbar zancen BALA dake hakimci saman kujera kamar parlor gida shi yayi yana washe baki ya ce," shekara biyar kenan hajiya wlh ni d'ana ganshima na aza irin mafarkan dake nanne".
kallon sa Maleek yayi ya ce," watoh BALA har yanzun bazaka canja bako?" gyera zama BALA yayi ya ce" ba haka bane maigida Maleek watoh tun ina yaro Mama tayi tamin fada kan cewa Bala ka daina cin ƙafar kaza zaka rinka zuba k'amar gonar au....dakatar dashi Maleek ƴayi yana murmushi ƴa ce," tashi ƙa koma baƙin aikinka banson maganad'isu sai na fitoh" datoh ƴa amsa yana murmushi ya fice daga parlor yana faman kiran Abba shima ya shafa mishi."
ƙalle-ƙalle Maleek ya farayi yana cewa" ina Ummi na nifa banganta ba?" tana bedroom dinta fushi take da kai cewar Munirat ƙanwarsa, murmushi yaƴi ya wuce bedroom dinta baƙinsa dauke da sallama ya shiga zaune ya sameta Saman kujeran daƙe dakin tana duba littafin hannunta, sallamansa da tajine ya sata dago fusƙarta ta ƙallesa na wani minutes ta dauƙe kanta tana jin farin ciki na ziƴarci zuciƴarta amma bata nunaba sai ma kara daure fuskarda taƴi ta amsa masa sallamar ad'akile, ƙarasowa yaƴi ya zauna gefin ƙafanta a kasa ƴa ce" Fushi ƙike dani Ummi na? shiru tayi batace masa ƙomai ba tana sauraron sa, Ummi na!" ya sake kiranta marairaice am very sorry Ummi na nasan naƴi laifi but kiƴi hakuri ki yafemin bazan saƙeba"ƴa fada kamar zaiƴi kuka.
ajiƴe littafin hannunta tayi saman desk ta ƙama ƙunnensa ta ce" sbd kasan bana iƴa fushi dakai shine zaka tafi kamanta damu ƙo? ƴanzu kazo kana wani marairaice min. Auhh! Ummi na dazafi fa" ƴa fada yana murmushi, runkushi ta ƙai mai a kai daya sashi ƴin yar ƙara ƴa ce"wlh natuba Ummi na" dariya taƴi ta sakemai kunne suka gaisa cikin so da kaunar junansu domin sosai Ummi take kaunar dannan nata hira sosai sukasha kafin ƴa mata sallama ƴa fita lokacin har ana kiran mangarib, part dinsa ya wuce yayi Alwala ya wuce masjeeb shida Bala yana zuba mishi tsurutu.

Can asibiti ƙuwa ba wacce tazo ta bangaren Meerah sai ƙawarta sofiya data samu labari, ƙasan cewarsu ba yan nan din bane, ba dangin iƴa bare Baba" sai dangin mijinta su kuma basonta suƙeba ɓalle suzu dubata.

Sofiƴa da Sani driver suƙa ƴini a asibitin shima 4 naƴi ya sallameta ya ce" bari yaje gida akoi sakom dazai duba ƴana dawowa, batace masa ƙomai ya fice abunshi
bai dawo ba har bayan mangarib.
Ko da Daddy AKILA suka gama meeting gida ya wuce yayi wanka ya wuce police station nan aka fada masa basu samu komai dangane da mutanen da suka sace AkILA ba, baice komai ba ya fice daga station din zuciyarsa na zafi idan ma kudi sukeso ai sai su kira ko nawane zai basu su sake masa yarshi daya tilo da yake dashi a duniya gashi ba mgn takeba ko wani hali take ciki yanzun da wannan tunanin ya isah asibitin yana shiga word din ya samu Sani driver na waya yana ganinsa ya yanke kiran ya k'araso gunsa da sauri ya ce" yallabai ina fatan dai ansamu wani abu dangane da mutanen da suka dauki AkILA?" cikin muryar dake nuna yana cikin damuwa ya ce" ba'a samo komai ba har yanzu ana kanyin abincike" cikin tausayawa Sani ya ce" Allah ya bayyanata su kuma Allah ya toni asirinsu, da Amin ya amsa ya shiga cikin dakin da aka kwantarda Meerah.
shi kuma Sani ya zauna kan kujera dake bakin kofar yana jinjina kai.

Can bangaren AkILA kuwa basu tsaya da ita ko ina ba sai wani katafaren gida dake cikin wani bakin daji da suka masa Lakani da dajin guguwa dajin mutuwa, dajine dake dauke da manya_manyan mutane kamar samudawa hannayensu dauke da manyan bind'igogi kallon fuskukin su kawai zaisa ka kadiye zuciyarka ka mutu sabar tsorata. gasu da manya_manyan karnukan da haushin ya karad'e dajin.
tabbas duk wanda aka kawo dajin bazai tab'a tsiraba koshi wayen.
Jefata cikin wani daki sukayi tare da cire hulunan da suka rufe fuskukin su dashi suka kwashe da dariya hahahaha, cikin kakkausar murya daya daga cikinsu ya fara kiran Rozy!Rozy!! Fitowa Rozy tayi cikin wani daki tana hura tsigari kallo daya zaka mata kagane ba Imani a zuciyarta, fuskarta murtuk'e cikin tsawa tace "
Ina take?" nuna mata dakin sukayi batace komai ta bude ta hangita kwance batasan ma inda take ba sbd hudan da suka fesa mata, a tsawace tace " ubanwa yace kushakar mata da hudarnan?" A tsorace sukace Bizy....basu k'arasa magana ba ta harb'i Bizy a goshi nan take yabar duniya tace.......!

Paid book

Mrs Ahfat ce

🌈 AKILA 🌈Where stories live. Discover now