09: Hadiza

146 40 36
                                    


Da sauri Ibrahim ya yo kaina ya riqo ni kan na fadi. Kankame ni yayi in his arms protectively "Be careful" ya fadi, not letting me free from his embrace.

"Jiri ne ya ja ni". Na fadi masa. Kallona fuskar sa dauke da damuwa matuka.

"You don't look too well". Ya fadi nayi masa murmushi kan nace masa it was nothing serious. Hankalin sa be kwanta ba dan duk yadda nayi dan naga nayi calming dinsa ya qi sai da ya matsa muje hospital muga doctor. Wucewa nayi na fara shirin zuwa doctor din. Sai da na bari ya futa daga dakin tukun nayi sauri na dau wayata na kira Dr Sarah. Tana ansawa ban tsaya pleasantries ba nayi going straight to my reason for calling.

"Muna hanyar zuwa da Ibrahim. Nan da thirty minutes". Na mata bayani kan na qara da "Breath no word to him". Sarah zatayi protesting nace mata "please Sarah. Not now, you know how he is". Ba dan ta so ba tace shikenan. Kashe wayar nayi na cigaba da shiri na.

Hira Ibrahim ya dinga ja na da shi on our way to the hospital. Duk da I was tensed haka na biye masa muka yi ta hira. Ina gudun ya gano cewar ina cikin damuwa dan haka I had to act as normal as possible. Bini bini yana da shafo hannu na yana tambayata ya jikina, ya nike ji a jikina. Duk ya bi ya shiga damuwa. That's Ibrahim for you. Abu kadan ke saka shi shiga yanayi na damuwa.

Muna isa hospital ba da wani jimawa ba muka samu ganin Dr Sarah dan dama ta riga ta san da zuwan namu and there weren't much people on queue. Mutum biyu ne kawai aka duba kan aka zo kaina. Tare da Ibrahim muka shiga suka fara gaisawa da Sarah.

"Alhaji Ibrahim kenan kayi wuyan gani. Yaranka har sun gaji da tambayata Uncle dinsu". Sarah tace da Ibrahim wanda ya sa hannayen sa biyu ya riqo kunnuwan sa.

"Nayi laifi gaskia. Bana samun zama ne amma wannan weekend din In Shaa Allah zan zo na duba su".

"Ai kema kin daina kawo su gidan". Na fadi kan tayi dariya tace "Kai Hadiza koh wata biyu anyi da suka zo sleepover?". Duka muka yi dariya aka shiga hirar rayuwa and everything kan Sarah ta fara duba ni.

In Ibrahim ya lura da tension inda ke tsakanina da Sarah he didn't talk about it. Shuru duka mukayi ta cigaba da aikin ta, idanunta a kai na nikuma na dauke nawa idanun daga kanta dan na san saqo take kokarin tura mun through eye contact. There was nothing that Sarah was going to do to make me change my mind, bani da niyyar fadawa Ibrahim wannan babban sirrin da nike boye masa har sai lokacin da nike ganin ya kamata ya sani tukunna. Inda ma ina da dama da sai nace bazan taba fada masa wannan mummunar labarin ba har ranar da zan dau numfashi na na karshe a duniya. Bayani Sarah ta fara mana cewar cikina ya kai sati bakwai a wannan lokacin kuma blood pressure dina ya dan hau hakan yana iya zama dalilin da ya sa nike yawan jin jiri da zazzabi. Magunguna ta fara rubuta mun tana cigaba da ma Ibrahim bayani. Sai da muka tafia tukun ta fada mun lokacin da zamu dawo dan yin first ultrasound. Ibrahim ya kuma tambayar ta for about the hundredth time tun zuwan mu hospital din kan lafiyar baby din ita kuma ta sake assuring dinsa cewar the baby was in perfect condition, kada ya sama wata damuwa. Godia ya mata ya sa hannu ya ciro kudi daga aljihun sa ya miqa mata cewar ta siyawa yara abu. Da kyar ta iya karban kudin, sai da Ibrahim ya bude mata ido cewar ba ita ya ba kyautan ba yaran sa ya ba ma dan haka ta karba.

"We need to talk". Ta fadi mun softly cikin kunne na da tazo hugging dina. Kan muyi releasing juna daga hug din nace mata "I'll be here tomorrow when he's out". Shoulder na daya ta dan murza bayan munyi releasing juna daga hug din tace mun na kula da kaina. Yar murmushi na mata kan muka wuce da Ibrahim. Reception muka koma yayi settling hospital bill din muka kama hanyar gida.

Muna hanyar bamu isa gida ba aka kira Ibrahim a waya yayi connecting call din to speaker din motar dan haka nike jin abunda suke fadi. Magana ne akan motar da ya siya is ready za a kai masa gida yanzu. Daga masa gira daya nayi da ya gama call din nace "Mota kuma? Mun gama hawa wanda suke gida ne?".

Lawh-Al-MahfouzWhere stories live. Discover now