11: 1996.

119 39 14
                                    

Biki na saura kwana biyu ranar Yaburra ta tashi da sassafe ta futa. Koh sallan asubah ba a tada ba sanda ta futa daga gidanta ta sama qawarta a tashar mota inda suka kama hanyar Kukawa gun wani malami da aka musu kwatance, wanda shi kuma a nasa tsari baya ganin baqi sai da safe koh dare. Suna isa Yaburra ta isar ma boka da qudirorin ta, harda kukan ta dan ya tausaya mata ya taimaka mata ta kwatar ma diyar ta mijinta da kanwar ta ta satar mata. Nan da nan boka yace ta kwantar da hankali sannan ta dauka cewa buqatar ta tamkar an biya mata shine. Kudi ya caje ta masu yawan gaske ta sauke masa su kan ya fara mata aiki.

"Kinga wannan" ya fadi yana miqa mata wani magani da ya daure shi da igiyar doguwa "Karbi ki dora shi a qugun ki yanzun nan" jiki na bari Yaburra ta karba ta miqa ta dora shi a qugun ta kamar yadda ya fadi. "Ga wannan kuma ki saka a hammatanki". Ya miqa mata wani maganin. Karba tayi ta saka a cikin hammatar ta kamar yadda ya fadi sannan ya miqa mata wani qullin maganin a leda kan yace. "Ku tashi ku wuce. Kada ki kuskura kicewa kowa komi daga yanzu in kun futa nan da maganin a jikinki har ku kai gida. Lokacin zaki cire ki dake su daban daban su zama gari. Na qugun ki zaki barbada so uku a miya ki kira sunan diyar taki da sunan shi saurayin. Na hammatan ki kuma zaki barbada shi so daya tal amma a cikin abinci mara miya sai ki kira sunan dayar yarinyar so tara ki basu su ci. Da zarar ta ci wannan abinci saurayin zai ji kiran da kika masa bazai taba samun sukuni ba har sai ya zo anyi auran su". Dariya duka sukayi na jin dadin abunda boka ke fadi.

"Ita kuwa dayar yarinyar tana cin wannan abincin ke bama mutum ba, koh bunsuru bazai qara muku sallama bakin qofar gida neman ta ba".

"Wannan kuma". Ya fadi yana nuna dayan kullin da ya bata "Sai ranar da ita diyar taki zata hadu da shi saurayin sai ta zuba shi a ruwan wankan ta tayi wanka da shi amma ta saka baho ta tara ruwan wankan sai ayi masa dahuwa da shi ya ci. Me raba ta da shi sai mutuwa". Murmushi boka yayi musu da haqoran sa da suka dawo yellow sabida rashin kula.

Godiya su Yaburra suka fara zubawa boka suna ta sa masa albarka. Boka yayi dariya kan su tafi yace "Baiwar Allah kan ki tafi sai kin ije jingina". Ya fadi yana washe baki.

"Jingina kuma malam bayan kudin da na biya". Dariya yayi kan yace "Ehh sai an ijewa Aljana Naja'atu jingina dan yaranta ne zasuyi wannan aikin. In wani abun ya faru kikayi wani kuskure aikin be je daidai ba zasu qone in kuma suka qone sai sun sha jinin Biladama kan su warke dan haka kan ki bar nan sai kin bar mata jinginar mutum daya daga cikin zuri'a  da Allah ya baki sabida tsaro". Kallon juna Yaburra sukayi da qawarta, Yaburra ido na neman raina fata dan ita duk duniya ba abunda take so kamar yaranta. Har ta fara cewa qawar ta bazata iya ba qawar tayi maza tace da ita "Dallah can wawuya. Menene zai tafi ba daidai ba? Yau kika saba barbade ne Yaburra? Ai cewa yayi jingina sai in wani abu ya faru ne zaa buqaci jinin. Ki bada sunan Hamza kawai mu tafi".

"Hakane koh?". Yaburra kamar wawuya ta fadi qawar tace "Ehmana. Mu da muka san sirrin tsiya". Suka sha hannu kan suka juya ga boka ta fadi sunan d'an ta Hamza harma da sunan mahaifin sa. Kan azahar sun koma cikin gari sun isa gida. Gidan dama ba kowa sai yara dan dama baqin Yola a can gidan su Haji Modu aka sauke su dan Yaburra tace koh taron bikin bata so ayi mata a gida a bata mata gida haka nan Haji Modu ba yadda ya iya sai can gidan ya sauke baqi kuma ya maida taro.

Hayaniya sukaji tun kan su shiga cikin gida. Koh da suka shiga dambe suka ga ya kaure tsakanin Fusam da Shatu. Ana ta kokarin raba su an gagara Fusam ta danne Shatu a qasa tana ta kai mata naushi. Qawar Yaburra ce tayo kan su ta jawo Fusam ta jefar da ita gefe kan ta daga Shatu wadda ta ruga gun mahaifiyar su a guje tana kokarin mata bayanin abunda ya faru a harshen kanuri. Takaicin Shatu ya sa Yaburra ta kai mata wani irin mari wanda sai da ya razana masu tsaye a wurin. Masifa ta fara mata itama a harshen yare tana fada mata taji kunya da ta bari yarinya yar shekaru sha bakwai ta kai ta qasa tana bata kashi. Sai da ta gama da Shatu ta daka mata tsawa cewar ta wuce su shiga ciki tukun ta juya ta kalle Fusam da ke jikin Hadiza ta riqe ta tace musu "Toh karya tayi! Ba tsumman kuke sanye da shi ba. Kuna da suturan da ya wuce tsumma. Almajiran banza". Ta fadi kan ta juya sai dai kan ta wuce ciki kalaman Fusam suka tsayar da ita cak.

Lawh-Al-MahfouzWhere stories live. Discover now