12: 1996.

112 48 20
                                    


Su Hadiza haka basuyi barci ba dan duk jikin ta ba inda be mata ciwo. Fusam na gefen ta in ba kuka ba ba abunda take yi. Ta rasa me zata yi ma Hadiza. Haka suka lallaba har zuwa wayewar gari tukun ta futa ta dinga gudu har ta isa gidan kakkanin ta. Nan ta zube dakin kishiyar mahaifiyar Haji Modu dan asalin mahaifiyar sa Allah ya mata rasuwa dan haka Baba Azumi ita suka sani a matsayin kakar su. Samun ta suka yi zaune tare da yayar mahaifiyar su da suka zo daga Yola suna karin safe suna hira. Zubewa tayi jikin Baba Azumi ta barke da kuka tana kiran sunan Hadiza. Nan da nan hankulan su suka tashi. Sai da hawayen ta suka tsakaita tukun ta musu bayanin komi dalla dalla tun kan ta gama Daadar su ta fara share hawaye tana wayyo mutuwa, in ba mutuwa ba da ya raba Maryama da yaranta da yaushe zasu shiga irin wannan halin. Nan da nan suka miqe daya daga cikin qannin Haji Modu da ke zaune a kusa da iyalin sa Baba Azumi ta aika aka kirawo mata ya dauke su a motar shi zuwa gidan Haji Modun. Koh da suka isa Haji Modu ya riga ya wuce kasuwa ita kuma Yaburra dama yana sa qafa ya futa itama ta fice wayon bin bokayen ta. Ta tafi gun bokan ta na cikin gari dan jin koh akwai taimakon da zai mata.

Kuka duka suka shiga yi ganin halin da Hadiza ke ciki ana gobe bikin ta amma ace an mata jina jina haka har an karya mata hannu. Nan da nan qanin Haji Modu ya dauke ta ya wuce asibiti da ita. Kan Baba Azumi tace ya wuce kasuwa ya kirawo mata Haji Modu. Gado aka ba Hadiza doctor ya hau kanta aka fara treating dinta. Ba a wani jima ba Haji Modu ya taho asibitin Baba Azumi ta rufe shi da masifa tana qorafi akan yadda yayi sake da lamarin marayun yaransa. Kare Yaburra Haji Modu ya shiga yi ya dinga bawa su Fusam laifi. Hakan ya kuma dagawa Baba Azumi hankali dan ta san Yaburra bata bar Haji Modu haka nan ba, babu uban da ke cikin hayyacin sa zai dinga ma yaran da ya haifa irin abubuwan nan musamman ma in aka yi la'akari da irin son da yike nuna musu a da.

Sai da ta gama jaraba tukunna tace masa sai yaje ya sama magabatan Ibrahim ya musu bayani koh za a daga bikin ne. Koh da yaje ya sama Haji Bukar ya fadi masa abunda ke wakana, sosai Haji Bukar ya jinjina maganar sannan yace In Shaa Allah zai magana da Ibrahim. Immediately ya sa aka yi aike zuwa inda Ibrahim ke bautar qasa dan a sanar da shi abunda ya faru kuma sannan a fada masa Haji Bukar din na son ganinsa. Gaba daya abunda yike yi ya tattara ya ije a gefe ya wuce asibitin duba Hadiza kan ya wuce gida. Ganin halin da Hadiza ke ciki ya sa Ibrahim kwalla, gaba daya Yaburra tayi disfiguring dinta, jikinta duk a kumbure, fuskar ba kyaun gani amma hakan be rage son da Ibrahim ke mata a ran sa sai ma qaruwa da son yayi, yaji ya mugun qosa ya aure ta ya dauke ta daga gidan ubanta. Hawayen da ya dinga kokarin riqewa sai da suka sauko da Fusam ta futo rakashi tana maida ma shi yadda abun ya faru. Haquri ya bata ya qarfafa mata kan ya ciro kudi ya miqa mata ya wuce yace mata da dare zai dawo.

Yaburra kuwa koh da taje wurin bokan cikin gari fatattako yayi yace bata zo wurin sa neman magani ba, tana so ya warware mata aikin da wani ya mata. Sai da ya kwashe mata albarka tas kan yace mata baya ma kaunar qara ganinta a gidanshi tunda ta raina aikinsa ta koma neman wani malamin. Daga nan gidan Talatu ta wuce amma tun daga bakin qofa da Talatu ta hango ta ta buya tace ma yaranta suce bata nan an mata rasuwa ta tafi can Bama garin mijinta ta'aziyya sai tayi sati guda kan ta dawo. Jiki a sanyaye Yaburra ta bar gidan Talatu. Futowa tayi daga inda ta boye tana fadin "Matsiyaciya! ya miki kyau. kullum sai dai nayi ta yawon raka ki gidan malamai kina sauke musu kudade ni koh sisin ki bana gani na ci. Kya ji da shi, ina zan iya komawa wurin malam ya hada dani".

Rasa abun yi ya sa ta wuce gidan kanwarta wadda suke yawon malaman tare dan jin nata shawaran. Nan da nan yar uwar nata ta shirya tace mata suje gidan malam Gobe da nisa ta san shi bazai rasa basu mafita ba. Koh da sukaje boka ya duba ya duba ya fada musu cewar gaskia bazai iya karya wannan asirin ba, hasalima babu wanda zai iya karya shi sai shi wanda yayi shi. Kuma tabbas kamar yadda ta bada sunan Hamza inda bataje anyi saurin karya asirin ba zata rasa shi kuma diyar ta Shatu na iya samun matsala sosai akan maganar aure. Kuka Yaburra ta fara tsakanin ta da Allah tana ta fadin ta gama yawo ta lalace. "Shikenan Hadiza ta gama dani. Uwar su ta riga ta musu asiri kan ta mutu, sun gama dani".

Lawh-Al-MahfouzWhere stories live. Discover now