14: Hadiza.

181 40 11
                                    


Tun da aka kirani cewar Umma ba lafia gaba daya na rasa sukuni. Duk da ance jikin da sauki na kasa samun kwanciyar hankali na san kuma nayi na gan ta da kai na ba dan haka na fara hada yar travelling bag qarama. Na hada yan kayan da zanyi using for a few days na jera a ciki. Kan Ibrahim da Bibi su dawo daga aiki na gama shirye shiryen tafia na Maiduguri dan har flight ticket na siya.

"You're always so thoughtful my love" Ibrahim ya fadi yana kissing saman kai na. Dawowa yayi ya samu na riga na gama shirin komi na tafia Maiduguri. Sai dai tafiyar namu babu Bibi sabida aikin ta. Itama tana dawowa aiki ta hada nata kayan, tare muka bar gida. Ita ta kama hanyar zuwa gidansu Muhibbah inda zatayi spending few days zuwa lokacin da zamu dawo mu kuma driver ya wuce airport da mu. Kan ayi sallar isha'i muna garin Maiduguri, driver din gidansu Ibrahim already an aiko shi airport yana jiran mu.

A duk da na ziyarci garin Maiduguri, sai na sama kaina da tuno da memories masu yawa. Wasu masu dadi, wasu marasa dadi. Da wanda zasu saka ni murmushi, wasu ma har su saka ni dariya wanda zanyi ta yi har sai cikina ya kusa qullewa, wasu abubuwan kuwa da na tuno sai dai na share hawaye daga idanu na. Yanzu zaman mu a mota samun kaina nayi da lumshe idanuna, na saki wata murmushi ina reliving wasu memories. Nayi murmushi ne ba dan abunda nike tunowa na farin ciki bane, nayi murmushi ne dan whatever it was i was thinking of ya riga ya wuce, ya zama tarihi a rayuwa na. Dago kai na nayi na ga Ibrahim gaba daya hankalin sa na kan wayar da yike ansawa. Gaba daya concentration dinsa na kan wayar sabida abunda yike tattaunawa me muhimmanci ne, abu ne da ya shafi aiki. Hannu na na dora kan nasa na dan shafa shi hakan ya sa ya juya ya kalle ni yayi mun murmushi kan ya sake maida attention dinsa kan wayar sa. Ba a wani jima ba muka iso gidan su Ibrahim. Gidan da ke dauke da memories da yawa na farkon rayuwar auran mu da Ibrahim.

Gidan qato ne haddade, da ka ga gidan ba sai an fadi maka cewar mutanen da ke cikin sa mutane ne masu arziki ba. Girma da haduwar gidan kadai ya isa ya sa mutum ya fahimci haka. Bayan main house din, akwai two other smaller apartments cikin gidan wanda yan uwan Ibrahim biyu ne ke zaune ciki tare da iyalan su. Main house din kuwa nan ne sasan suruka ta, Hajia Falmata nan kuma muka wuce kai tsaye. Koh da muka shiga a cike muka sama sasan Umma, surukan ta da jikoki harma da sauran yan dubiya duk sun zagaye da ita. Kowa yayi murnan ganin mu musamman ma Umma wadda muna shiga na isa inda take zaune na rungume ta. Yadda Umma ta dauke ni da irin kauna da kuma kulawar da take nuna mun yasa a duk lokacin da na kasance tare da ita nike ji tamkar ina tare da uwar da ta haife ni ne.

"Ina kishiya?". Ta tambaya da bata ga Bibi ba. Tun kan nayi magana Ibrahim ya bata ansa cewar mun bar Bibi a kaduna sabida yanayin aikin ta. "Iyyeeh! Gaskia Kishiya an girma, Tabarakallah".

Kayan abinci aka fara shigo mana da su duka muka ce sai mun gabatar da Isha tukun zamu ci. "Mu je dakina kiyi sallan". Umma ta fadi tana riqo hannu na kan ta ce masu aiki su biyo mu dakin da abincin. Muna shiga na fada bandaki nayi alwala kan na futo Umma har ta shimfida mun sallaya. A koh da yaushe bata taba gajiyawa da hidima ta, indai ina tare da Umma bata kaunar taga nayi komi. Duk sanda ta gan ni rasa inda zata sa kan ta take yi dan murna, wannan shine irin son da Hajia Falmata ke yi mun.

Ina cin abinci Umma na zauna gefe na tana mun hira. Da mun hada idanu zata yi mun murmushi mu cigaba da hirar mu. A haka Ibrahim ya shigo ya same mu shima ya zauna ya fara cin abinci daga plate dina. A wannan yanayin, duk wata damuwa da tashin hankalin da nike ciki yan kwanakin nan duk na nime su na rasa. Naji zuciya ta babu komi in ba farin ciki ba.

"Ummaaaaaa" na fadi da muka hada ido da Umma naga ni take ta kallo. Murmushi tayi kan tace "Naji dadin ganin ki ne Hadiza yar albarka". Kan nayi magana Ibrahim ya riga ni "Kin fada mata?". Ya tambaye ni. Shuru da nayi ya basa ansar tambayar sa.

"Menene ba a fada mun ba?". Umma ta tambaya.

"Yanzu duk yadda kuke da Umma dama baki fada mata ba?". Ibrahim ya fadi in a dramatic way "Ai nayi tunanin kan ki fada mun ma ita kika fara fadawa". Yayi murmushi kan yace Umma ta kawo kunnen ta kusa ya fadi mata "Amma in na fada miki sai kin bani tukwuici". Sai da Umma ta yarda zata basa tukwuici tukun ya kai bakinsa daidai kunnen ta ya mata rada. Hamdalan da naji Umma ta fara ya sa na sunkuyar da kai na, lokaci guda naji kunyar ta ya kama ni. Sujudus-shukur Umma tayi ta dago tana zubda hawayen farin ciki tana fadin "Ashe ina da rabon ganin wannan ranar ni Falmata. Allahu Akbar Kabeeran, Alhamdulillah". Ta fadi tana share hawayen ta. Nima ban ankara ba naji hawaye sun fara zubowa daga idanu na, kai na a qasa nayi kokarin boye hawaye na amma already sun riga sun gani.

Lawh-Al-MahfouzWhere stories live. Discover now