Chapter 1

424 27 6
                                    


Saukar ruwan saman, bai hanashi tafiya da sauri a filin Headquarter, dake nan Abuja ba. Cikin izza, taƙama, da taurin zuciya irinta sojoji, yake taka ƙafafuwan nasa, ruwan na sauka da ƙarfi a jikinsa, da ka ganshi kaga ingarman namiji.

Gaba ɗaya sansanin sojojin cike yake, da manya da ƙana nan sojoji. (Part of Nigerian Armed forces headquarters Abuja, Motto (s) victory is from God Alone!".

Gaba ɗaya sojojin dake cikin Headquarter ɗin, basu damu da ruwan dake sauka kamar da bakin ƙwarya ba, wasu na tsaye, wasu na zaune wasu kuma suna abinda ya shafe su, wasu kuma suna in da babu ruwan suna shan Cigarettes (sigari).

Tun yana tafiya da sauri har ya fara daidaita tafiyarsa ,wanda daman hakan al'adar sa ce, duk inda ya gilma cikin Headquarter ɗin hannu ake sara masa zuwa sama, alama dai shi ɗin Babban mutum ne, matsayi mai girma gareshi a cikin sojojin.

Wani office ya nufa cike da nutsuwa, yana zuwa aka bashi hanya ya shige, yana shiga office ɗin ya ƙame!.. tare da ɗaga hannunsa sama alamar girmamawa da masu ɗamara kewa junansu.  Sojan da yake zaune sanye da kaaki, yayi Murmushi cikin sakin fuska yace

"Have a seat.." yai Maganar yana nuna masa kujera.
Kamar ba zai zauna ba, se kuma ya zauna saman Kujera. General Ibrahim A.M ya kalli matashin saurayin dake gabansa kafin yace "Munyi magana da Chief of Army staff, akan Operation da za'a fita, aiki ne mai wahala kuma bama son, Kidnappers ɗin su samu information na aikin nan, dan opretion ne me hatsarin gaske, yana da kyau ku kula, bamu da tabbaci kowa zai dawo da rai acikin ku, dan kun san komai dai"

Matashin dai kansa yake a ƙasa, yana sauraren General babu alamar zai magana, ya tattara dukkan nutsuwarsa yana sauraren shugaban nasa.
General Ibrahim ya buɗe wani file yana dubawa kafin ya kalli saurayin yace

"Hope you are ready for it, and  kayi sallama da iyalanka?" .

Sai a lokacin Matashin saurayin ya ɗaga idanunsa wanda sukai ja sosai ya kalli General Ibrahim, kallon da yake masa yasa General Ibrahim faɗin "Oh, I forgot  you just came back from Zamfara yesterday"
Matashin dai bai ce komai ba, da Idanu kawai yake bin General.

General Ibrahim yace "Zaka iya tafiya, jirgi na jiranku a airport, and airforce zasu rigaku zuwa ku kula da kyau akan dukkanin bayanan da zasu baku, da kuma umarnin da zaku samu daga garemu"

Matashin saurayin ya miƙe tsaye yace "ok sir" tare da sake sara masa, sannan ya juya, yana tafiya a hankali har ya fice daga cikin office ɗin General Ibrahim.

Cikin nutsuwa General Ibrahim  ya ɗauki Wayarsa tare da danna wasu lambobi, babu jimawa aka ɗauki wayar daya kira, ƙasa ya yi da Murya yace

"Akwai kyakykyawan labari" daga cikin wayar wata shaƙaƙƙiyar murya ta bayyana akace "Mene labarin?"

General Ibrahim ya ce "Chief of Army staff, ya bada umarni ga Sojojin da suke Headquarter na nan Abuja zuwa Naija state, kai tsaye kuma cikin Dajin Zugurma in da kuke tsare da yaran nan, kuma a wannan karon sun samu cikakken ikon yin harbi,  umarni ne daga NAC. _Nigerian Army council_"

Mutumin da General Ibrahim ya kira ya yi dariya kafin ya ce. "Ganganci haihuwa da damuna, a tunaninsu zasu Iya ƙwace ƴan matan da mukai  kidnapping ne? Bayan gwamnati ta hanamu abinda muka buƙata?"

General Ibrahim yace "Na kira dai dan in sanar maka da zuwan su, a Kowane lokaci sojojin sama zasu tsinkayi dajin, nine zan tsara komai na Operation ɗin tare da jami'anmu na nan Naija state,  zan sanar maka da duk wani arrangement na yaƙin, kaga kuna da damar da zaku samu galaba a kansu, dan haka se ku shirya zuwansu" 

Mutumin ya yi dariya yace "Daman ance da ɗan gari akanci gari, mune mutanan banza, kai kuma maci amanar ƙasa"
General Ibrahim ya yi Murmushi yace "To Rayuwar sai da haka, in ba haka ba a banza za ka gama aiki Kai retire amma na abinci ya gagareka, ko a kashe ka a banza gurin kare ƙasar da ta gaza biyawa masu bata tsaro buƙatunsu, dan haka zan tura maka account number, ka bani share ɗina saboda na samu labarin wasu daga iyayen yaran sun baku kuɗi akan ku sakar musu yaransu"

DARE DA DUHUWhere stories live. Discover now