Chapter 10

277 12 7
                                    


Marairaice fuska Abra tayi, lokacin da suka isa ƙofar da zata kaisu zuwa parlourn gidan kakarsu wacce ta haifi Na'ima.

Salman ya kalli yayar ta sa kafin a hankali yace "Mene Yaya?" Muryar ta na rawa tace "Faris tsoro na keji"
Salam ya buɗe ido sai kuma ya yi dry yana faɗin "Yaya ba gani ba, ki daina tsoro idan ina tare dake"
Shiru tayi masa, gane cewa da gaske tsoran ta keji yasa Salman kama hannunta suka shiga cikin parlourn bakinsu ɗauke da Sallama.

Muryar Salman ita ta danne siririyar muryar Abra, hakan yasa Mama dake zaune, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya zaton iya shi kaɗai ne yazo.
Cikin farin ciki ta ɗaga Idanunta tana faɗin.
"Maraba, lale da Mai gidana"

Salman ya yi Murmushi yace.
"Ƴar Tsohuwa"
"Wace Tsohuwar Salmanun Faris? Kabar ganina a haka auren naka sai nayi niy....," Maganar Mama ta tsaya lokacin da Idanunta ya sauka akan Abra, wacce take ɓoyewa bayan Salman sai ka rantse shine gaba da ita.
Mama ta haɗe fuska, tare da ɗauke kanta gefe guda, sam bata ƙaunar ganin Abra da jikan nata Salman, tsoro da fargaba da tunanin wani abu, yana kawowa Zuciyarta farmaki.

Anuty Suwaiba tunda suka shigo take bin Abra da wani irin kallo, musamman ganin yadda lokaci guda Abra ta zama cikakkiyar budurwa kamar ita ta yi kanta sbd tsananin kyau, zubi, diri, na tsarin da Ubangiji ya yi wa jikin na ta.

Cikin sakin fuska, Salman ya ƙaraso cikin parlourn still holding her hands, Abra tayi saurin zame hannunta daga cikin na Salman, ta zauna ƙasan carpet muryarta na rawa tace.
"In...Ina...Inna...,"
Gaba ɗaya ta nemi gaisuwar ta rasa a cikin bakinta, Sbd Mama data murje mata yatsun hannunta da ƙafa.
Zafi da azaba yasa Abra sakin ajjiyar zcy, gomi na tsastsafo mata daga tsakiyar goshinta.

A fusace Mama ta juya inda Abra take zaune tace. "Kinga riƙe gaisuwar ki, munafukar yarinya mai mugun nufi a zuciya, ire-iren wannan baƙin halin naki yake sawa wani yayi zaton cutarki muke, ban taɓa yin jika mai mugun hali irin naki ba, KURMA kawai!"

"Wlh Mama mugun halin yarinyar nan yafi ƙarfin ta, na samu labarin ita take hana Salman zuwa gidan nan, Allah na tuba mene haɗin kashi da kiyashi ma? Shegiyar yarinya ke dai wlh Allah wadarai da halinki"

Anuty Suwaiba ta ƙarashe zan can tana Miƙewa tsaye, ita ta yadda ta tsani mutuwarta haka ta tsani ganin buɗe idanunta ta ga Abra a cikin gidan Na'ima, musamman yanzu yadda duniya ta lalace ka gama kiwata yarinya ka waye gari Uban riƙon ya aureta.

Abra tayi ƙasa da kanta, cikin damuwa Salman yace "haba Mama! haba Mama!! haba Mama!!!.. laluran nan fa Allah ne ya ɗorawa Yaya, babu wanda ya shige haka fa, kuma ni Anuty ki daina cewa yaya ta hanani zuwa gidan nan, ni yaro ne da za'a hanani abinda nai niyya? I don't want to go to your house since you don't like to see my sister"

Anuty Suwaiba ta saki baki kafin tace "your fifteenth year in the world, ban fa manta time ɗin da akai maka kaciya ba, yanzu nan kai har jinka kake wani babba?"

Wani irin baƙin ciki ya ziyarci zuciyar Salman, babu abinda ya tsaya masa a rai irin maganar kaciyar da Anuty Suwaiba ta yi, idanunsa har wani ruwu ruwa ya tara sbd zafin zuciya.

Mama ta riƙe baki tace.
"Salmanu! Akan wannan mowar kake faɗa mana Mgn? Kalli yadda ta gagara gaishe ni balle ta gaida Suwaiba? is this is what Na'ima train to you?"

Mama tayi mganar tana bugawa Abra tsawa, wacce ta sanya tayi saurin fashewa da kuka muryarta na rawa tace.
"Kiyi hqr Mama"
Miƙewa Mama tayi, domin idan taci gaba da zama a nan, zata iya lakaɗawa Abra dokan mutuwa!.

Salman yabi Grandma ɗin su da kallo, zuciyarsa nayi masa wani irin zafi baya ƙaunar duk abinda zai sanya yayarsa kuka, duk abinda ake wa Abra shine ya kejin zafin abin a zuciyarsa (Heartache) yana tsanin so da ƙaunar farin cikinta He is jealous of his sister, he sympathizes with her.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 10, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

DARE DA DUHUWhere stories live. Discover now