Chapter 7

158 11 4
                                    


Cikin wani irin ɓacin rai, Na'ima ke bin Abra da kallo! Wacce ke tsugune a toilet ɗin Captain, tayi kashi a ƙasa gaba ɗaya ta ɓata toilet ɗin da jikinta.
Bata taɓa jin, akwai wani data taɓa tsana a duniya kamar ABRA KHAMAL ba, ta tsani Yarinyar tsana mai yawan gaske. Gani take shigowarta rayuwarsu gaba ɗaya matsala ce.
Wannan dalilin ke sa wa Na'ima ta ƙara jin ranta ya ɓaci akan Abra. Kishin Abra ya kama Na'ima, irin kishin nan na tsakanin Kishiya da kishiya (crazy jealousy) mussaman yadda ta ga Khamal ɗin ya na bawa Abra kulawa.

Rai ɓace, Na'ima ta ja hannun Abra zuwa Part ɗin ta, Abra na tirjewa tana ƙoƙarin ƙwala kiran sunan “Abbi” Na'ima ta hankaɗa ta zuwa cikin toilet ɗin dake nata part ɗin. Wannan shi ne dama ta Farko, Da Za tai amfani da ita wajan cin Uban Abra, ta san idan tace a part ɗin Captain Khamal Khamis zatai Punishing ɗin ta, Tabbas zata ɓata rawar ta da tsalle, wanda zai sanya Captain Khamal Khamis ya din ga yi mata kallon Munafuka mai Fuska biyu, ita kuma bata son duk wani abu da zai shafi mu'amalar ta da Khamal.

"Zaki ci Ubanki, ƴar banza mai siffa irin ta sadaka yalla!" Na'ima ta faɗa tana murɗe kunnen Abra cike da mugunta, zafin da Abra taji ya sa ta saki wata siririyar ƙara mara sauti, saboda rufe mata baki da Na'ima tayi.
A fusace kuma ta shiga zarewa Abra, kayan jikinta tare dayi mata tsirara.

Ficewa Na'ima tayi, daga cikin toilet ɗin ta nufi ƙofar part ɗin nata, cikin sauri ko lura da cikinta ba tayi, taja ƙofar ta rufe, ta sa mata key, saboda kada Khamal ya jiyo sautin kukan Abra.
Tana komawa toilet ta nemi wayar chaji, Abra na durƙushe in da ta ajiyeta, babu zato ta ji saukar bulala akan fatar gadon bayanta.

Ihu ta saki da dukkan ƙarfinta tana kiran sunan Abbi, bata taɓa tunanin akwai azaba irin wannan ba, saukar bulalar ya gigita Abra Khamal Khamis ƙwarai, har wani irin shiɗewa take na rashin sabo!.

Na'ima tace "Yadda ki ka rabani da farin ciki na, ki kai sanadiyyar shiga tsakani na da mijina, haka zaki dauwama cikin gidan nan ina gana maki azaba kala kala, wacce zata saka da ƙafarki ki fice ki bar min gida na,
Gidana nawa ne, da ga ni, sai Mijina sai kuma yaran da zan haifa masa, bana buƙatar kowa cikin rayuwarmu, zuwanki ya ruguza min dukkan wani  burina, ba zaki taɓa jin daɗi ba in dai a gidan nan ne, mufuka, Algungumin".
Tai Maganar Kamar ta na yi da sa'arta.

Yadda Na'ima ke kumfar baki zaka ɗauka da wata ƙatuwar mace, sa'arta take wannan ihun, ba da little Abra da ba ta wuce a goyata. A. Abra kasa kuka tayi sai sakin ajjiyar zuciya kawai take, bayanta yayi kwance da zanan bulala, ta kasa ko ɗaga kai ta kalli Na'ima.

Tana bala'i da kumfar baki ta wanke wa Abra kashin, tare dayi mata wanka. Na'ima ta kalli Abra kafin da ɗan ƙarfi tace "Tsinanniyyar yarinya, Allah ya isa tsakani na dake, wlh da ƙafarki zaki bar gidan nan" Abra bata san me Na'ima take faɗa ba, hakan yasa bata ma fahimta ba, wani irin tsoron Na'ima ya kama Abra, tsoran dake neman sanyata cikin mugun hali, da son raunata mata ƙaramar ƙwaƙwalwarta.

Kama gashin kanta tayi da ƙarfi, cikin tsanar Yarinyar tace "Keee!!"
Abra ko motsi ba tayi ba, sai jikinta kawai take tsuma da karkarwa na azaba.
"Kika sake, naji kin faɗawa Abbi wannan maganar sai na yanka ki" Na'ima ta faɗi maganar cikin kunnen Abra, tana nuna mata wuyanta da hannu.
“A...Abbi jani" cewar Abra wanda ilahirin jikinta rawa yake, Na'ima ta figi hannunta zuwa bedroom tana faɗin "Abbin uwarki, ko na Ubanki? Baki da Uba a gidan nan Wallahi zan tabbatar dana gurɓata wannan muguwar fuskar taki. Kura da fatar Akuya!" Abra bata fahimta, da alamar yarinyar ta gama gigita da Na'ima, a haka Na'ima ta shirya Abra cikin Pria shirt short dress. Red colour, ta ɗaure mata tulin sumar kanta da ribbon.

Yadda Na'ima taji ana knocking ƙofar ta, yasa tayi saurin Miƙewa tare da gogewa Abra Fuskarta tas, ta nemi perfume ta fesa mata, hannunta ta saka ta ɗauki Abra tana gasa mata mintsini a haka ta nufi ƙofa da ita.
Tana buɗe ƙofar taga Captain Khamal tsaye sanye cikin ƙana nan kaya masu kyau, sai ɗaukan idanu yake.

DARE DA DUHUWhere stories live. Discover now