Chapter 8

116 6 0
                                    


Abra ta sha wahala sosai zamanta a tare da Na'ima, samun sauƙinta kawai shine idan Major Khamal yana gari, ko kuma idan sun je gidan Ammi, ko idan ta na tare da Faris, wato Salman.

GY BULAMA HOSPITAL AND MATERNITY.

MD ne wato Doctor GY a office ɗinsa, tare da wani mutum, GY ya gyara zaman glass ɗinsa ya kalli mutumin yace "wannan harƙallar ana samu sosai, zamu tura musu wannan mutumin da za suyi masa aiki, zasu turo mana da namu share ɗin".

Mutumin ya gyara zama yace "amma doctor baka ganin zasu iya ganewa, dan mu ci kuɗinsu za'a tura su india?"

"Ba zasu gane ba, ai ba yau muka fara wannan harkar da doctor Aman ba, shine shugaban Asibitin Darman Shakti, wannan ne karo na huɗu ina tura masa mutane, muna wannan harka"

Mutumin yace "Amma in balli ya tashi akwai damuwa fa"

GY yace "kar ka damu, ba wani balli da ze tashi, normal ne"

Mutumin yai ajiyar zuciya yace "Shikenan doctor, Allah yai mana jagora".

"Wallahi ranka ya daɗe, gaba ɗaya ji na ke aikin nan ya fita daga kai na, bana ƙaunar aikin nan yanzu gaba ɗaya".

"Subhanallah, amma meyasa ka ke jin aikin ya fita da ga ranka ba ka so?"

Cike da damuwa yace "Yanzu fisabilillahi abun da ake ya dace? Muna sadaukar da rayukanmu saboda ƙasarmu, amma manyanmu sun mai da ranmu ba a bakin komai ba, ƙirƙiri ga Nasara mu na kallo, amma se a dinga dakatar da mu?".

Major Khamal ya gyara zamansa, ya kalli matashin saurayin da ke ta mita yace "kai min bayani sosai yadda zan gane"

Matashin yace "Ranka ya daɗe, yaƙin da mu ka je ɗin nan, just recently, an gama shirya Komai mu ka shiga dajin nan, sedai ƙiri ƙiri aka hanamu harbi, su kuma kamar sun san dabarun da za mu yi amfani da su gurin yaƙin, su ka far mana da harbi, muna ji muna gani haka su ka far mana da harbi, se ɓuya mu kai Kamar wasu sakarkaru ba sojoji ba.
Shekaranjiya mun biyo ta wani ƙauye, an turamu wani aiki, ga mu ga 'yan ta'adda muna kallonsu, su na ta wucewa akan babura, sun rako wani Babban ƙusa a cikin su, wanda da ina gabda Allah ya sa mun kama wanda suka ɗakko ɗin, da mun karya alkadarinsu, dan a lokacin mun fi su yawa da kayan aiki a hannu, mu kai waya mu kace a bamu umarnin harbi, gamu gasu, amma se cewa a kai ba ruwanmu da su, kawai mu wuce.
Dan Allah ya rayuwa za ta yuwu da haka? Muna sanye da uniform amma ya zama aikin banza, sedai mu saka mu ɗau tsofaffin bindigogi muna hura hanci, idan munje yaƙi a fito a kashe mu, ba mu da kataɓus".

Ɗan shiruu Major Khamal ya yi Sannan yace "waye kwamandannku, lokacin da kuka je yaƙin?"

Cikin damuwa sojan yace "Captain Alex ne"

Ai yana cewa Captain Alex, a hankali Major Khamal yace "General Ibrahim"

A fili yace "Komai ze wuce insha Allah, idan irinku zaratan matasan sojoji na rasa karsashi suna ajiye aikin ya goben ƙasarmu ze kasance?"

"Yallaɓai to mu ya ta mu goben za ta kasance, da mu da iyalan mu da iyayenmu, idan an tura mu daji an hanamu kare kanmu balle ƙasarmu, in mun mutu wa ze kula mana da su?"

Major Yace "Allah yana tare da ma su zuciyar taimako, wadda ta ke aiki dan Allah".

Yai ajiyar zuciya yace "to shikenan Yallaɓai, Allah ya wuce mana gaba".

Major yace "Ameen, amma kar a karaya Please" jinjina kai yayi, ya gyara zaman bindigarsa ya fice.

TWO YEARS LATER....
Tsaye yake a ƙofar kitchen, ya zuba mata idanunsa, tana sanye cikin riga da skirt na English wears, ta na gaban sink ta na wanke wanke, gefe kuma ta ajiye littafi tana yi tana karantawa.

DARE DA DUHUWhere stories live. Discover now