Chapter 4

167 11 2
                                    


Captain Khamal ya yi saurin zame kan matarsa dake kafaɗarsa, idanunsa ya ware tare da sakin kwantaccen Murmushi, saboda ganin waɗanda suka shigo Room ɗin.  Babbar mace ce, fara tas da ita zata iya yin shekaru hamsin a duniya.

"Finally, my son survived Alhamdilillah" Hajiya A'isha ta ce, tana ƙarasawa bakin gadon da Major Khamal yake kwance.

Lumshe idanunsa ya yi, He breathed slowly kafin ya ware idanunsa akan matar cikin ƙasa da murya yace.
"First love" Ya Faɗi maganar yana ƙara sakar mata Murmushi. hannunsa ta kama tare dayi masa ƙuri da Idanunta, she tries to understand, if there is something wrong with him.

A Hankali tace "Hankali na, ya tashi sosai Babana, na kasa samun nutsuwa bana son aikin nan naka, kullum cikin zullumi nake da tashin hankali" Captain Khamal ya kama hannun Hajiya A'isha wacce ta kasance Uwa a gare shi, ya ɗan yi murmushi yace

"First love, ba gashi kinga lafiya nake ba? Zan warke insha Allah"

"Tsoro take kada a kashe mata Jaruminta" Da sauri Captain Khamal ya ɗaga kansa, with so much surprise yake kallon mai maganar, Sai a lokacin ya kula dashi.

"Baffa" Captain ya ce, yana  ware idanunsa akan mahaifinsa dake tsaye cikin shigar manyan kaya, kamarsa da Major Khamal ta bayyana sosai, hatta baƙar fatar Captain irinta Baffa ce.

Baffa ya harari Khamal, cikin wasa ya ce "An manta da Baffa saboda anga first love? Shine ni aka ƙi kulani" 

"It's not like that, Baffa" waje Baffa ya nema tare da zama cikin tausayin ɗan nasa ya ce "Ya jikin naka?" .

"Jiki Alhamdilillah Baffa"
Jinjina kai Baffa ya yi yana kallon wajan da aka harbi Khamal, cikin sanyin murya Baffa yace

"I received a call on  phone, from the military command in Abuja, sun gaya min Wanda suka rasa rayukansu a dajin, hankali na ya tashi sosai, mun ɗauka ko har da kai, Sai daga baya muka samu full information akan cewar kai raunuka ka samu"
Captain dai murmushi yake, yana son iyayensa bashi da kamar su.
"Yaya K, ya jiki?" Cewar wani matashin saurayi. Khamal ya kalli ƙaninsa Shureim yace "You?" Shureim ya kwaɓe fuska tare da faɗin "Duk na damu zan rasa Big bro, shine ya kula kowa banda ni"

"Sorry Shureim"
Shureim ya ce "Ya jikin Yaya K?" Captain ya rufe idanunsa A hankali ya ce "I'm good" surutun da yake yi, gaba ɗaya ya fama masa ciwon, yana jin yadda gurin yake masa zafi sosai.

Na'ima dake gefensa, ji take kamar ta ɗauke mijinta su tafi gida haka take ji. Tayi kewarsa sosai, har tsanar aikin take saboda tsayin lokacin da suke ɗauka basa tare.

Army Doctor ɗin daya shigo ne, ya kalli su Baffa cikin sakin fuska ya ce "Ana buƙatar ya samu nutsuwa, wajan harsashin bai warke ba haryanzu"
Baffa ya miƙe tsaye, Yana faɗin "Daman da yaya aka barmu muka shigo ganinsa, tafiya za mu yi tunda kun mana fin ƙarfi" Dr ɗin dai murmushi ya yi, Baffa ya yi waje. Hajiya A'isha ta kalli Captain ta ce "Allah ya ƙara sauƙi Babana, Zuwa yaushe zaka dawo gida ka huta?".

"First love ban sani ba, but Soon in sha Allah"
ta ce "To, Allah ya tsare min kai"

yunƙurawa ya yi zai tashi da sauri Na'ima ta kamashi tana faɗin "Be careful"
Duk yadda yaso miƙewa kasawa ya yi, Dole ya koma tare da zama ya ce "Allah ya kiyaye hanya first love" fita duk sukai hadda Shureim.

Na'ima ta kalleshi tace "My man, ni ina nan tare da kai ko?"

Ya ware Idanu ya ce "Are You sure?" Kai ta ɗaga masa tana  kama hannunsa tace "I really really miss you Man, Over eight months banji ɗumin ka ba"

hancinta ya ja "I miss you both, i mean you and my unborn child" Lamo tai a kafaɗar sa, kewarsa na fisgarta, She misses every single thing about him, she wants to be with her husband.

DARE DA DUHUWhere stories live. Discover now