Chapter 9

127 6 0
                                    


Wata irin bugawa zuciyar Na'ima ta yi, cikin ƙaraji ta ce. "What? Wacece ke?"

Dariyar rainin hankali wadda ta kira wayar ta yi ta ce. "Ko ba ki ji abun da na faɗa dai-dai ba ne in ƙara maimaita miki?"

Wata Uwar ashariya Na'ima ta ƙunduma ta ce. "Wallahi k'arya kike matsiya, Shegiya karuwa, Khamal nawa ne ni kaɗai babu wacce ta isa ko da rab'ar shi ne ta yi balle har ta aure shi, ba'a halicci mace ba wallahi."

Cikin murmurshi ta ce. "Za kuwa ki gani, ganin idonki, ki cigaba da kular mun da my Daughter yanda ya kamata." Sannan ta ja tsaki ta kashe wayar.

A haukace Na'ima ta sauke wayar daga kunnenta ta shiga bin screen ɗin wayar da kallo, tamkar za ta ga matar da ta kira ta a cikinsa, babban baƙin cikinta sai da aka b'oye numbern sannan a kira ta.

Wani irin tuƙuƙwin baƙin ciki zuciyarta take mata, cikin takaici ta cillar da wayar, Allah ya taimaka ta faɗa kan gado. Hannunta ta ɗora akan goshinta tana bubbuga kanta ta fara magana ita kaɗai.

"Impossible! Wallahi ba zai yiwu ba, sai na gano ko wace ce ke na kashe ki, sai dai ki auri Khamal a lahira ba dai a duniya ba, matuƙar ina numfashi babu macen da ta isa ta shigo cikin gidana a matsayin matar Mijina.

Wayarta da ta cillar ta ɗauka ta fice daga ɗakin a matuƙar fusace ta nufi part ɗin Khamal.

Salman dake zaune a parlour yana kallon Ball ya bi ta da kallo cikin mamakin ganin yanayin da ta fito kamar wadda ba ta cikin hayyacinta.

"To Macuci, mayaudari, azzalumi, mugu, yau Allah ya toni asinka, dama an ce rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tal ta mai kaya."

Abun da Na'ima ta faɗa kenan bayan ta tura ƙofar ɗakin Khamal da ƙarfi ta shiga.

Da mugun mamaki Khamal dake zaune yana operating system yake kallon ta, kasa cewa komai ya yi saboda tsananin mamaki.

Cikin kuka ta ce. "Ka cuce ni, na yarda da kai Khamal, amma ban san me ya rud'e ka, ka ci amanata ba."

"Na'ima, wannan maganar banzan da kike yi duk na mene ne?"

"Na cikin shegen da kika yi aka haifi waccan shegiyar yarinyar ne."

Fauu! Fauu!

Khamal da ya miƙe cikin sauri kamar wanda aka hankad'a ya saukewa Na'ima tagwayen maruka a fuska.

Cikin tsananin ɓacin rai ya fara magana.

"I told you Na'ima, duk abun da zaki yi ki yi amma kar ki ƙara danganta mun ƴa da Shegiya, na faɗa miki ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba."

Na'ima dake riƙe da kuncinta wanda take jin kamar ba ya jikinta saboda tsananin azaba, idanunta na zubar da hawaye ta ce. "Ni ka mara Khamal akan waccan yarinyar mara asali?"

"Yes, kuma idan kika ƙara maimaita abun da kika faɗa, abun da ya fi mari ma zan miki wallahi!"

Yana gama faɗar haka ya fice ya bar mata ɗakin ya tafi other room dake part ɗin ransa a matuƙar b'ace.

Da wani irin kallo ta bi shi har ya fice, wani irin ɗaci take ji tun daga zuciyarta har zuwa bakinta.

Zama ta yi a bakin gado tare da fashewa da kuka, a ranta tana faɗin, 'Komai zai faru sai dai ya faru, amma wannan karon ba za ta hak'ura ba, ba za ta cigaba da zama da Shegiya a gidanta ba, sai a yi duk wacce za'a yi.'

Sai da ta ci kukanta ta ƙoshi sannan ta lalubo wayarta dake gefenta, dan ko gani ba ta yi sosai saboda masifar ciwon da kanta yake mata. Numbern Aunty Suwaiba ta kira, ringing biyu ta ɗaga tare da ambatar sunanta.

Kuka Na'ima ta sakar mata cikin rashin abun yi.

"A'a, Lafiya? Me ya faru? Wani abun ne ya samu Khamal ko Salman zaki kira ni a daren nan ki saka mun kuka?"

DARE DA DUHUWhere stories live. Discover now