Chapter 5

177 14 5
                                    


Wani irin kallo Captain ya bi Faruk da shi, yana son gazgata abun da kunnuwansa suka jiye masa ya fito daga bakin Faruk.

"Do you mean my Abra?" Yai maganar yana nuna kansa da yatsansa.

Faruk cikin damuwa yace "eh, Abra ba'a ganta ba, na duba duk in da ya dace a cikin barrack ɗin nan ba'a same ta ba"

"Shhhhhh, kar ka gayamin maganar banza mana Faruk, ya za'ai ace yarinyar nan ta ɓata how comes? Kaga, i have no option for now am going make sure you bring back my daughter"

"Haba Captain, ta ya zan maka ƙarya, Wallahi a.....

Be ƙarasa maganar ba Captain Khamal ya ɗaga masa hannu yace "na gama Magana, duk in da 'ya ta take ka tabbatar ka nemo ta ka kawo min a bata"
daga haka ya cigaba da takunsa sannu a hankali me kama da na ƙasaita yaa bar Faruk a tsaye a gurin.

Faruk yace "ya salam, Madam Halima kin kashe ni ina kika bar yarinyar nan ta tafi? Ya a kai ta ɓata?" ya ƙarasa maganar yana sauke wani irin nannauyan numfashi, kafin daga bisani ya juya cikin sassarfa ya nufi wani sashi na barrack ɗin.

Zaune take a kan gwiwonwinta, ta zubawa kyakkyawar yarinyar me kama da 'yar larabawa idanu, hawaye ne kwance akan fuskar yarinyar, hannunta ɗaya riƙe da teddy bear, ta zura yatsanta ɗaya a baki tana tsotsa kamar me shan nono.

"Hey look up, kina son chocolate?" Tai Maganar tana kallon idon Abra.

Shiru Abra tai tana binta da kallo, dan sam ba ta ji me tace ba.

"In baki chocolate, ai zaki sha ko?* Still Abra bata amsa ba, kallonta kawai take kamar wata gunki.

Salima ta tashi ta ɗakko jakarta,ta ciro Chocolate ta miƙawa Abra, maimakon Abra ta karɓi Chocolate ɗin, se ta fashe da kuka tana kiran "Abbi, Abbi".

"Shhhhhh, is ok i will take you to your Abbi, amma ki yi shiru, I have plenty chocolate and teddies, zan baki idan ki kai shiru"

Ƙaro sautin kukan Abra tai, tana kiran sunan Abbi.

"Ji min makirar yarinya zata ɗaga min hankali, will you shut up?"

Babban abunda ya bawa Salima mamaki, be wuce yadda sam Abra ba ta responding ga Maganar da duk za tai mata ba, kukanta kawai take yi.

Salima tace "what so ever, da ke zanyi amfani in cika burina, se na nunawa matar Khalid bariki iyawa ce, sena rusa gidan da mijin da take taƙa ma da shi.

TWO DAYS BACK. Kwana biyu da suka shige!

tun bayan faɗan nan da Salima sukayi da Naima, Salima ba ta sake komawa gurin Khamal ba, se ta fita waje ta kama Hotel tai zamanta, sakamakon rashin posting ɗin su da ba'a yi ba.

Tun abun da ya faru a tsakanin ta da Na'ima matar Khamal, tace se ta ga abunda ya turewa buzu naɗi in dai akan Khamal ne, se ta gwadawa Na'ima kalar nata rashin mutuncin da iya barikanci.

Khamal kuwa da ƙyar ya rarrashi Na'ima, kasancewar ta mace me tsananin kishin tsiya, ba ta da haƙuri ko kaɗan akan kishi, ita da ta zo dubiya ƙarshe se da su kai faɗa da Khamal akan Salima.

Na'ima ta daɗe da sanin Salima na bibiyar Khmal, amma tafi kowa sanin halin mijinta, mutum ne kamili da be ɗau duniya da zafi ba, sam ba shi da wannan ɗabi'ar ta kule kulen mata, hasali ma mutum ne me tsare gida, wanda ba'a kawo masa wargi, amma Salima ke ta cusa kanta a wajensa.
Tun kan ya Auri Na'ima, Salima take son sa, amma kasancewar Salima ba mutuniyar arziki ba ce ya sa ko saurararta ba ya yi sam, ya sha yi mata gargadi da jan kunne, akan ta fita daga rayuwar sa amma taƙi, se da ta ƙure shi ta kai ga ta sa ya gaya mata miyagun maganganu, amma still ta ƙi barin rayuwarsa, sannan tai alwashin se ta ga bayan Na'ima, se ta raba shi da ita.

DARE DA DUHUWhere stories live. Discover now