Al'adarmu

15 0 0
                                    

AL'ADAR MU

By _Qamshi_ ✍️

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LnmhM4gO8toIH8oxYEobJ9
4...

Tare suka fita parlorn, yanda Barr ya iske yaran shi ya d'an tab'a shi, sai dai rashin sanin abinyi ya sashi d'auke kai tare da cema Anwar "I thought har yanzun baka dai na kukan ba" Au kuka ma ya keyi? to na me?" Yabi ta fad'i hakan bayan ta zauna a gefen jikokin nata, had'a baki wurin ce mata ina yini su kayi, da lafiya lau ta ansa, sannan ta maida hankali wurin 'ya 'yanta da suke ta k'ok'arin fita daga parlorn, musamman Barr, "Ina yini Baba" Suka cema Proff. ansa masu yayi da lafiya lau tare da k'arawa da ya Ummahn naku, Ikhram ce kawai tace lafia lau, daganan sukaja baki suka tsuke, "Mu mun tafi". Proff yace a lokacin daya d'age cotton d'in d'akin, saida Yabi tace a sauka lafiya sannan ta dawo da duban ta akansu Jiddah da suka rakub'e tamkar bak'i, k'are masu kallo ta rink'ayi na kusan 20second's, ta nayi kuma tana kwab'e fuska kamar wacce taga abin k'i, kafin tace "Yau ni naga hi'ili, kuma nice yau na zame maku bak'uwa?" Cikin su babu wanda yayi yun k'urin d'ago kai balle tayi tunanin samun ansa daga garesu, ganin bazata samu ansa bane ya sata cewa "Toh ai shikenan tunda ba kuda lokaci na, kai Anwaru tashi mu shiga ciki, ku kuma in kun shirya zaku iya biyoni d'aki" Daga haka ta mik'e rik'eda hannun Anwar a hannu suka shige bedroom d'inta, tana shigewa ciki Ikhram ta mik'e tsaye tana fad'ar "Wai me Abbah ke nufi da haka?" me yake nufi da kawomu gidan tsohuwar nan? karde yace anan zamu zauna? To ita kuma Ummah mubarta dawa, koko damuwa ta kasheta?" Da idanu kawai suk'a rink'a binta, dan basuda abun ce mata, su ganin k'ok'arinta ma sukeyi, da harta iyayin wata k'wak'wk'warar magana, "Kunyi shiru yaya, wai anan zamu zauna?". ta maimaita tana mai fashewa da kuka, a hankali Khalipha ya mik'e ya rik'ota, Saida ya zaunar da ita, sannan yace. "Calm down Ikhyn Ummah, koma abinda ki kayi tunani hakan ne to ya kamata mu d'auke shi as part of our destiny" Destiny?". Destiny fa kace yaya, Jiddah ta katse shi da fad'ar hakan, ba tareda kuma jiran jin ta bakin shi ba ta cigaba da magana, "Haka zamu zauna kullum cikin destiny, kadafa kamanta wannan destinyn ce tayi silar guduwan Aunty Ridorh daga gida, shikenn fa ta tafi, ta tafi tabarmu, taje inda ayanzun koda za'a samana wuk'a ba zamu fad'eshi ba, ta tafi fa kenan, sannan wannan destinyn da kake fad'i a kullum ce tayi silar mutuwar auren mahaifiyar mu" Shin wai sai yaushe ne zata tsaya ita destinyn, sai yaushe ne zata zo k'arshe, koko sai ta k'arar damu gaba d'aya, gawarwakin mu ko kuma jikkunan mu da suka zama sai an d'aga sai an tayar saboda bak'in ciki ne za suyi taking action akan ita destinyn?" Iye yaya, pls answer me?. kana ganin ya kamata mu cigaba da tafiya a haka, ta k'arasa maganar tana mai fashewa da kukan da ya saka jikkunan su yin sanyi, ya kuma saka Ikhram yin shiru daga nata kukan, dan ta fahimci nata nafila ne, Wannan rana ta zama karo na farko da Khalipha ya fara tsananin tunanin kawo k'arshen wannan matsalar, sai dai rasa ta ina?, da kuma wane courage ya sashi kasa ce mata komai, he so much wish ace Aunty Faridah nanan, dan yasan itace kad'ai zata iya te makamai, itace kad'ai zata sanya mai jarumta da k'warin guiwar yin hakan, although su Jiddahn ma za su iya, amma Ridorh ta fisu k'arfin hali, "Ni bara na shiga daga ciki" Ikhram ta fad'i hakan saboda takaicin yayan nasu daya isheta, dama tasan koda sunyi niyyar yin wani abun shine zai dakushe su, kullum shike maida possible ya zama impossible, "Wait for me Ikhy" Jiddah ta fad'i hakan itama tana mik'ewa, a parlor suka barshi abin duniya duk ya isheshi, Saboda ya kawar da damuwar data tayimai yawa yasa shi binsu, sai da Yabi ta zazzagesu kamar wad'anda sukayi wani laifi kana ta cema Khalipha idan yaga dama ya dauk'i key ya tafi d'akin da yake opposite da guest room ya saka su, su kuma su Jiddah su dauk'i nasu kayan su saka a second bedroom d'inta" Kamar ko jira suke duk suka mik'e, saboda gajiya da su kayi da k'ananun maganganun ta, tabarsu da damuwar su amma a'a tabi ta ishe su, "Ku dai kuka sani" Ta fad'a, bayan sun shige. Hajiya Marwah da damuwa tayi mata yawa, sai ta mik'e ta shiga toilet ta d'auro alwallah, tazo ta tada sallahn nafilfili, bata dakata ba har saida aka kira magrib tayi sannan ta d'auk'i alqur'ani, ko kad'an ba tayi tunanin kiran hajiya Aysha ko wani daga cikin aminan ta ba, saboda sanin datayi na cewa inma ta kiran wata damuwar ce zata k'aru mata, dan tasan ko ba ace mata komai ba za'ayi mata maganar Faridah. Tana zaune akan carpet har akayi ishsha'i tayi, tana iddarwa ta tashi ta d'ora daga inda ta tsaya, dan duk saboda ta sama ma kanta sallamar ruhi da gangar jiki, Sosai ta keson koya ma kanta hak'uri da juriya akan komai da ake yi mata, idan tace hak'uri tana nufin hak'uri wanda ko asarar hawayen ta ba tason ta kumayi, Shigowar Barr d'akin ne ya sata sallame sallar, ba tace mai komai ba, saboda batasan abinda zata cemai d'in ba, ganin shirun yayi ya wane gashi yanada uzuri ya sashi cewa "Kayan Anwar fa?" mik'ewa tayi ta d'akko mai kayan da tunda suka fita ta had'a, dan dama tayi tunanin zai dawo, yana fita ta cigaba dayin sallar ta, A parlor ya tarar da su duk sunyi jugum jugum, Yabi kuma tanata faman fad'a akan operating phone's d'in da su keyi, "Ai bara Abbakar d'in ya shigo mu daddaleta, Dan sam bazan lamunci iya shege ba, ba ruwana da wata makaranta, da'ita ake fakewa ana baku wad'annan wayoyin, ku kuma kuyita tsula tsiyar ku, to na gaji, "Gwara daka shigo awannan lokacin". ta fad'a a lokacin da Barr ya shigo, bayan ta ansa mai sallama, tsayawa yayi yana k'are masu kallo kafin ya juya ya kalli Yabi yace lafiya koh hajiya" A'ah ga sunan ka tambaye su, dan ni wannan wayoyin nasu sun isheni, bashi babban ba. ba kuma su k'ananun ba, duk waya ta bi ta lalata su, ba suda wani aiki saina danna waya, tun jiyafa su keta danna ta, kofa rintsawa ba suyi ba, shi maganar ta tama dariya taso bashi, sai dai da yaga ta d'auki maganar serious ne ya dake, tare da maida hankalin shi garesu, "Kai me ka keyi da waya da dare?, bana hanaku mik'a duk ka lokutan ku gareta ba, kuna ma yin muraji kuwa?" ya fad'i hakan yana kakkafe Khalipha da ya sunkuyar dakai yana shafar k'eya da ido, "Network d'in side d'in nan gaba d'aya be da kyau Abbah, sai dare yafi k'arfi, kuma Aunty Jiddah ce tayi operating phone at night time, saboda presentation da kuma assignment d'in da tayi jiya, Ikhram ta fad'i hakan ba tare da tabari Khaliphan da'aka tambaya ya ansa ba, dan dai tasan shi kame kame zai tsayayi, "Ok to meyasa bakuyi mata bayani ba, kuka barta tana fad'a". To ai ita granny ko anyi mata bayani bata shiru, sai tayi ta fad'a kamar anyi mata laifi. Anwar ya tsoma masu baki acikin zancen nasu, ita dai Jiddah zura masu ido tayi, dan tana ganin bama tada lokacin shiga cikin sabgar wannan tsohuwar da ta maida kanta rud'ad'd'iyar k'arfi da yaji, "Au Allah" watukum ku masu 'yan uwa koh, duk kun tsomo wa mutane baki kamar anyi daku, harda kai ko Anwaru da nike ganin ka kamar wani salihi, ashe maciji ne acikin koriyar ciyawa, To bari kuji ba asenment ba koma a menene ni Rabi nace baza ayiman shi a gida na ba, gwara tun wuri kusa ni, saboda banga wata ma'anar k'in yin baccin ba, ban kuma ga anfanun barrar ma tab'ararrun yara irin wada'nnan da k'ananun shed'anu zasu iya hure ma kunne cikin k'ank'anin lokaci waya ba, To wai ma shi Abubakar d'in nawa yake, kuma yaushe ya girman da za'a bashi waya, dukka dukka yaushe yabar yawo tsirara a cikin gidan nan da har za'ace an ba k'annan shi irin wa'innan wayoyin bama fa shid'in ba, haba Abbakar, ya kamata ka d'auki darasi, kasan Annabi ya faku ko kan abinda ya faru da yayar su, kafa duba kagani, ita kanta da take babbar su shaid'anun nan basu barta ba, to taya kake tunanin su zasu barsu, da har kasamu karsashin barin su da wayoyin. Hannu Ikhram tasa ta rufe baki, saboda gudun kufcewar dariyar da take ta dannewa since akan cewan da Yabin tayi wai yaushe Khalipha ya daina yawo tsirara, shikam ai Khalipha wani irin kallo ya jefa mata, wanda be san ta ankare ba, sai dai yaji tace hararar ni dakyau, ba kuma zan fasa fad'a ba, ma tuk'ar uban ku nason gyara tarbiyyar ku dan gudun fad'awa tarkon da Faridah ta fad'a to fa dole sai ya tashi tsaye, ba kuma zai ta shiba sai ya kakkarb'e wad'annan wayoyin na hannu ku, da suke saka ku kwana zuk'um kuna danna su, Ganin surutun Yabi bame k'arewa bane, sannan kuma ta juya maganar ta zuwa wurin Barr yasa Jiddah mik'ewa ta nufi hanyar d'akin su, da wata iriyar kakkausar murya mahaifin nasu ya kirata kafin ya k'arasa gareta, koda zata jiyo bata ankara ba taji saukar hannun shi a fuska, ba kuma ta k'arayin wata wata ba ta kuma jin wasu, a gigice ta zube k'asa tare da sakin razananniyar k'ara, sai kuma ta koma tayi shiru kamar wacce ruwa yaci, "Ke dan ubanki waye sa'anki?". wato abunda ake fad'aman kullum bana yarda ne kike k'ok'arin gwadaman ko, who did u think u are da har tana magana zaki tafi?, kina ganin koni na isa na tafi a lokacin da take magana ballantana ke, koko yanda aka koya maki abayan idanuna ne ki keson nunaman saboda wuyar ki ta isa yanka iyeeh?, Ya fad'a cikin d'aga murya, ita dai ba abinda ta keyi sai ajiyar zuciya, dan har cikin jininta ta kejin zafin marin, "Ku mik'oman wayoyin naku ya fad'a cikin zafin rai" Cikin rashin kuzari suka ijjemai wayoyin akan center table din da yake kusa dashi, be ko kalli inda suke ba, yace have ur way, ba Jiddah da tasha mari ba, hattasu a kid'eme suka fita daga parlorn, saboda dai su a iya tsawon rayuwan su, basu tab'a ganin mahaifin nasu a irin wannan yanayin ba, be ma tab'a bugun wani ba, koya ko zasu kai ga b'atamai rai, sai dai fad'a da zagi, "Kiyi hak'uri Yabi" Barr ya fad'a bayan sun shige ciki, kamanta da abunda ya faru Abbakar, yaran ne ka haifesu baka haifi halin su ba, amma fa maganar gaskiya banason wad'annan wayoyin kwata kwata, tunda dai inaji kuma ina ganin labaren su a telebijin, matsala ce babba musamman ga yara mata, duk da suma yara mazan ba sauk'i bace a garesu, musamman da wa'incan jajayen kunnuwan ke fidda fina finan lalacewa saboda assasa tab'arbarewar tarbiyyar d'iyan musulmi. "Murmushi Barr yayi kafin ya fara maganar cikin sassayan murya dake cike da alamar girmamawa ga mahaifiyar tashi, "Hakane Yabi" Amma a wannan zamanin da muke ciki dole sai da wayoyin, saboda bincike a cikin karatu, kuma bincinken be yiwo saida wayar, Shiyasa muke hak'ura muna basu wayoyin, sai mu rink'a yi masu addu'ah", Nasan wannan Abbakar, tunda ba yaran ka kad'ai keda manyan wayoyi ba, amma yanda naga yaran ka na anfani da sune yasha banban dana sauran yara, kuma ni gaskiya bazan zuba ido inga lalacewar su ba, nafa fad'ama jiya kwana sukayi dannata,. Kasan ni kan fita idan nagama sallah tun sanda muka samu 'yar gobarar nan, to nayi haka jiya, da yake nabar su suna kallo, nayi tunanin sun barman tv a kunne, dana fita sai naga sun kashe, inaganin hakan sai nace barama na k'arasa wurin shi Abbakar d'in tunda dai naji su 'yan matan basu kwanta ba, aiko in gayama ina zuwa naji surutu rak'ak'a a waya, alamun kallo ya keyi, wurin k'arfe biyu da wani abu na dare fa, dana k'wank'wasa sai naji anyi shiru, da nayita k'wank'wasawa sai ya taso yake ceman wai kallo ya keyi, Nace ya kamata dai a kwanta hakan nan, yace to, daganan na koma wurin 'yan uwan, su dai banji me sukeyi ba amma dai nace masu su kwanta, sai dai koda na fad'a basu kwanta ba, dan tunda na farka bacci kuma yayi k'auran zabo a idanuwana, Wuraren k'arfe ukku ma dana k'ara zagawa bansa mu wani canji ba, "In sha Allah za'a ja masu kunne hajiya, Barr ya fad'i hakan cikin muryan dake cike nuni da k'ararar tabbaci hakan, "Shikenan" Yabi tace tana jinjina kai, kuma ya kamata a rink'a sama zuciya sallama dan be kamata a rink'a yima 'ya 'ya mata irin wannan hukuncin ba, in sha Allah yace sannan ya mik'e ya shiga bedroom d'inta, Tunda suka shiga ciki Ikhram da Anwar keyima Jiddah magana cikin sigar rarrashi, amma tak'i ta d'aga koda kai ne balle su sa ran ji daga gareta, ba abinda ta keyi sai ajiyar zuciya, dan har iwarnan lokacin jin bugun take tamkar a lokacin ya yimata shi, sannan data tuna ayanda taga idanun mahaifin nata, sai taji gaba d'aya tsikar jikin ta na tashi, tambayoyi tayi tayiwa kanta akan wannan fushin na mahaifin nasu wanda be tab'ayin irin shi ba, amma har sanda ya shigo d'akin bata samu wata k'wak'wk'warar ansa ba, sallamar shi ce ta sata d'ago kai. Ba yabo ba fallasa kan fuskokin nasu suka ansa shi, shi d'inma hakan take gareshi, tunda ba rarrashin su ya shigayi ba, mik'ama masu wayoyin yayi, ya tsaya k'ik'am kamar ba zai ce komai ba na kusan 15second's, sai kuma yace "Ko waccen ku ta cire securityn wayarta" Jiki na rawa na tsoro da fargaban yanda zai d'auki some of they chat, dan sun san sometime's su kanyi chating romantically, thinking of babu irin wannan ranar, saboda sun san iyayen su nasu basu damu da chat d'insu ba, musamman ma Abban, saboda shi mutun ne me i don't care attitude, shiyasa hukuncin shi ga Jiddah na yau keta basu mamaki,. Mik'a mai wayoyin sukayi bayan sun ciccire d'in, fita daga d'akin yayi ya nufi na Khalipha, shima kamar yanda yace masu Jiddah haka yace mai, daganan ya baro d'akin nashi, ya dawo gun mahaifiyar shi da taketa safa da marwa a tsakar parlorn, "Harka fito?" Ta tambayeshi, "Eh" Yace mata a tak'aice, to ai dai ta hak'uri da halin yaran nan, kasan d'a ne ka haifeshi baka haifi halin shi ba". Hakane Yabi, to kagani, sai dai muyita binsu da addu'ah, "Ya kuma maganar Faridahn?, anko ji daga jami'an tsaron?" Eh d'azun munyi magana da I.G, amma fa ba wata magana tsayayya sai dai addu'ah kawai, sai da Yabi ta sauke gauran numfashi sanna tace "Wannan yarinya, wannan yariya Allah ubangiji ka ganar da ita gaskiya, wallahi ko yanzu aka ganta ta walahar da mutane, amma ita da Allah, duk kuma yanda sukaso mu wahalta daga ita har uwarta billahillazi sai dai ta k'are kansu, dan dai nasan yanzun duk inda take ba dad'i takeji ba, in dai ba hannun dangin uwarta takeba, dan nasan ba abin da Marwah ba zata iyayi ba in dai akan farin cikin yaran ta ne, tana iya b'oye ta, nan gaba in k'ura ta lafa ta dawo da ita, ta k'ark'are maganar tanajan dogon tsaki tareda cewa "Aiko da taga tsiya" Shi dai Barr sauraren ta kawai yake, hartayi ta gama be katse ta ba, tana gama maganar Faridah kuma ta d'akko na Salmah, "To shikuma maganar auren naka fa, Nafa fahimci baka damu da batun auren nan ba, ai dai kuma ga yanda mukayi dakai tun rannan, agaban d'an uwanka, ba dai takura ka akayi ba, ina nan Baba na har cewa yayi idan ba zaka ba Marwah gida ba ba, shi zai bata saboda sanin halinka na shiriri ta, amma kace a'ah, to kuma naji shiru, haka akeyi, ni sai naga kamar ma kishin Marwahn ka keyi, zaro ido yayi waje yana kallonta, fuskar shi d'auke da fara'a,. Kafin yace hajiya nizan tafi, kuma in sha Allah yau idan na shiga zanyi mata magana, gobe idan Allah ya kaimu sai ta kwashe kayan, kinga yau yamma tayi, zuwa goben sai a fara gyaran, "Au wai dama ba kayi mata magana ba, shine kullum in na tambaye ka kake ceman tana nan tana had'a kaya?" To ka kyauta, tunda gatanan da za'ayi maka ne bakaso, in sha Allahu bazan sake shiga sabgar ka ba, indai ta wannan b'arayin ne, kayi abunda kake ganin yafi cancanta dakai, tana gama fad'ar hakan tayi hanyar d'akin ta fuuuu, shikam binta da ido yayi, a zuciyar shi kuma yana jinjina k'arfin hali da rigimar ta, sai da ya bita ya lallaso sannan yabar gidan,. "Ke Aunty kin tafi kin barni da damuwa fal raina" Saida hajiya Marwah tayi murmusa sannan tace "Keko damuwa ta mene?" Ta yara mana Aunty, to wai ma wane daliline zai sa mutun ya kwashe yara a hannun biological mother d'insu yakai su wurin wata, watar ma tsohuwa, idan yana tunanin sanyi da kawaicin ki sun hana ki kula da tarbiyyar su ai ka mata yayi yakai su wurin macce me jini ajiki ba tsohuwa ba, tsohuwa ma irin kakar su da bata zama wuri daya,. Saida hajiya Marwah ta sauke b'oyayyiyar ajiyar zuciya, sannan tace "Ga babban dalilin shi nan Aysha,. bak'in cikin daya turnuk'e ta ne ya hanata k'ark'are ma k'anwar tata zancen, sai da Ayshan tace "Kinyi shiru Aunty, lafiya dai koh?" Kana tace Lafiya lau Aysha, kawai dai abubuwan ne keta d'aureman kai, wallahi yau kwana biyu kenan amma har yanzun na kasa samun k'warin guiwar taran wani da zancen, sannan ga kuma wani sabon lamarin daya b'ulloman dashi, "Wane irin lamari ne wannan Aunty?, hajiya Aysha ta tambaya cikin muryar zak'uwa, a hankali ta furta kalmar "Saki, Aysha Abban su Jiddah ya sakeni, da saki ukku yaso jeraman, sanadiyyar Khalipha ya dakata da sakin,. "Hajiya Aysha da tunani ne, damuwa ce koko takaici ne ya cikata ita dai bata sani ba, ta saki wata uwar ashariya wacce bata tab'a sanin cewa ta iyata ba, "Shi dan uban shi Khaliphan uban wa yace ya dakatar dashi?, ai da ya sani yabbarshi, wallahi da  k'afafun shi zai jawo a k'asa yazo neman gafarar ki, amma wallahi ba zai same ta ba, wai shi mutumin nan me ya d'auki kanshi ne, koko an fad'amai zura ido na nufin rashin so ne, to yanzun ma da kike zaune a gidan na shi ya maida auren ne ko kuwa?" Ina fa ya mai da, ai bama ki tsaya nakai ki ba kika cab'e, Inane zaki kai ni Aunty?, to ai ke da kiketa wannan babban min da fad'ar da ya sakeni da kaza ne zai faru baki sani ba, "Menene kuma?" hajiya Aysha ta tambayi yayar tata, uhm ai next friday za'a d'aura mai aure da Salmah, sannan upper friday zai tare, yanzun maganar da nike maki yace in tattara kayana zuwa gibe zan tashi gidan nan, wai zan koma wani gidan shi da ke Kabala, saboda bakida iyaye ko kin rasa ma fad'i?, hajiya Aisha ta katseta da fad'ar hakan, ba tareda kuma jira tajira jin abinda zata ce ba ta cigaba da magana, "Ai ina tunanin inhar ya kasa barinki acikin d'akin ki to bashida wani gida daya isa ya sakaki bayan ya sakeki, ni wallahy ma ba laifin shi nake gani ba naki ne Aunty, amma dan Allah na rok'eki kiyi k'ok'ari ki fara had'a kayan naki goben in sha Allah da sassafe zan shigo gidan, tunda jikin Abban Nurain ya k'ara gyarewa sosai, ba zaki tare a gidan ba, Adamawa zaki tafi, kayan kuma nizan ijje a gidana idan komai ya lafa sai muji ta bakin su hajiya,. Ajiyar zuciya hajiya Marwah ta sauke kafin tace to dama ni ma ai banyi tunanin zama a gidan nashi ba, tun da ba nida wani abinda d'auka a kaduna ba, dama dai yara ne to ya k'wace abinshi, ko fa kira na basayi, idan na kira kuma bana samun su, to zaman Kaduna na me?" A'ah ki zauna yayi ta k'unsa maki bak'in ciki mana, tunda an fad'amai iyayen ki basa k'aunar ki, nifa yaya da zaki yarda wallahi da yau d'in ma ba ki kwana gidan" A'ah keko Aysha abi a hankali mana, ai da yau da goben duk d'aya ne, karki damu, "To shikenan" Allah ya nuna mana goben lafiya, da ameen hajiya Marwah ta ansa sannan su kayi sallama.

  *08152163536*.@

AL'ADARMUWhere stories live. Discover now