AL'ADARMU

5 1 0
                                    

AM

By Qamshi✍️

Not edited, cux banda chargy.

🌟FCW association🌟✍️

32...

"Ki kwanta Jiddah" Hajiya Salmah ta cema Jiddah hakan, bayan tagama yi mata duk wani abu da ya kamata, "toh" Kawai Jiddah tace, daga hakan Hajiyan tabar d'akin, zuciyarta na yi mata zafi akan abinda hajiya da Barrister suka yi mata, sosai ta fara gajiya da sauyin d'a da uwar, komai tayi a wurin su ba dai dai bane, musamman idan ya kasance akan Anwar, tarasa gane kadidin wannan lamari, da zuciya d'aya ta shigo gidan Barrister, dan ita sam ba taga abin k'i a tattare da yaranshi ba, a dai matsayin su na 'ya 'yanta, idan da Kara, sai dai a 'yan kwanakinan Yabi da Barristern suna son su canza mata intension.

  
Wani irin murmushi ne ya yi escaping daga lip's d'in Jiddah, saboda tuna 'yar rayuwar da su kayi da Drn ta, rayuwar ba taje ko ina ba, ba kuma tayi nisa ba, amma natsuwa gamida hutun da ta samu tana jinta tamkar wacce tayi shekaru aru aru dashi, "na yi kewar ka Yaya" Ta ce hakan a fili, tana k'ara sakin murmushi tare da shafa fuska, ta jima tana tuna abubuwan da suka wakanan a tsakanin su, na dad'i da kuma akasin hakan, kafin bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ita.
     "am talking to you Zainab" Dr da ya b'ata rai ne ya cewa Zainab da ke duk'e gabanshi haka, muryanta a dake, alamar rashin tsoro ko k'ek'ashewar zuciya ta ce, "i don't mean anythi,.."shout up my dear!!" Dr ya katseta da fad'ar hakan, a wannan karon sai da zuciyar Zainab ta buga, saboda firgici, take kuma rudu da rashin sabo ya sakata sakin kuka, sai da ya d'an ja tsaki sannan yace, "will you shout up!!?" Take ta had'iye kukan nata, saboda sanin halin mahaifin nata na zafi, although bai tab'a yin fushi irin hakan ba, "za ki fad'aman ne, ko na kira Ummulkhair d'in?" Kasa cewa komai tayi, dan har cikin ranta takejin tsoron mahaifin nata, ganin ba zata tankashi ba, ya saka shi mik'ewa ya bar d'akin, "Ummulkhair, Ummulkhair!!.. Shine sunan da Dr ya ke kira, murya a hasale, Kairy da tunda Abban nasu ya kira Zainab ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta yi firgigi ta nufi hanyar d'akin shi jiki a d'ar d'ar, clashing su kayi a dai dai bakin stairs, shi yana k'ok'arin hawa ita kuma tana k'ok'arin sakkowa, wani irin kallo ya watsa mata, wanda ya saka taji gaba d'aya tsoron mahaifin nata ya mamaye gabaki d'ayan ruhi da gangar jikinta, "Abbbbah" Tace hakan muryarta na rawa, baice mata komai ba, ya juya zuwa d'akin shi, bin shi tayi itama, a haka suka isa d'akin, zaune ta iske Zainab na sharar hawaye, abin da ya k'ara hautsina mata lissafi, itama wurin ta samu a gefen Zee d'in, shiru d'akin ya d'auka na 'yan wasu lokuta, ko wannen su zuciyar shi na yimai sak'a da warwara, Dr ne ya yi breaking silence din nasu ta hanyar cewa, "Ummulkhair" Khairy da ta sunkuyar da kai ta d'ago a hankali tace, "na'am Abbah" Sai da ya sauke ajiyar zuciya, saboda son calming kanshi before ya fara yi mata magana, sannan yace, "I wan't to ask you a question, andd mind you" Sai da ta d'ago sannan yace, "bana son k'arya, idan kuma kika yiman zan gane" Gyad'a kai kawai tayi, daga haka yace, "me Auntyn ku tace maku?, i mean d'azun bayan naje raka Dr David?" Wata irin fad'uwar gaba ce ta riski Khairy a wannan lokacin, saboda rashin sanin ansar bashi, na farko dai ita ba zata iya fad'amai abin da Yayar tasu tace ba, saboda gudun abinda kaje ya dawo, sannan kuma ba tajin zata shareshi, "toh me zaki ce mai?" Zuciyar ta tajeho mata tambayar, "kin yi shirun" Da Dr ya cene ya sakata yin firgigi, tare da d'ago kai ta kalle shi, "Ina sauraren ki" Yace murya a matuk'ar hasale, Dan Allah,..."shiiiii!!" D'in da yace ne ya dakatar da ita, take kuma kuka ya kufce mata, mtssw yaja dogon tsaki, tare da mik'ewa, rik'e da goshin shi, "ku fita ku bani wuri!!" Yace hakan rai a b'ace, tuni kuma idanun shi su kayi ja, jiki a matuk'ar sanyaye suka mik'e su ka bar d'akin, suna barin d'akin, ya nufi bathroom ya d'auro arwallah, sallah yazo ya tada bayan ya fito, ya jima yana sallan, saboda son samun relief, aiko ya samun dan bai bar wurin ba har sai da zuciyar shi ta bashi shawarar kiran Jiddah, a hankali ya mik'e ya nufi wurin wayar shi, d'auka ya yi, ya yi dialling numbern Jiddan, Jiddah dake kwance tana bacci ne taji ringing din wayar tata tamkar a mafarki, sai da ta kai zuciya nesa, sannan ta bud'e ido, tasa hannu ta d'auki wayar, a dai dai lokacin kuma kiran ya tsinke, sake dialling numbern ya yi a karo biyu, in da ringing d'aya, biyu tayi picking, duk da ko har i lokacin batasan ta wacece ba, a wannan karon Dr ne ya yi sallama, saboda gudun sake katse kiran nata, dummm taji gabanta ya buga, saboda muryar da kunnuwanta su kayi arba da ita, kafin kuma ta dake tace, "wa alaikumus salam" Sai da ya murmusa sannan ya ce, "i thought ba za kiyi picking ba" Itama murmusawan ta yi tace, "ina yini,."lafiya lau anmatan Ummah, ya gida ya bacci" Murmushi ta yi tace, "wanene ya ce ma nayi bacci?,.."zuciya ce ta fad'aman hakan" Ya fad'i hakan a tak'aice, yana gyara kwanciyar shi, "uhmm" Kawai tace tana murmushi, shima murmushin ya yi yace, "ya dai,.."a'ahhh babu komai,.."a'ah da komai Jiddorh, ba ki yarda ba ko?" A wannan karon ma sai da murmusa sannan tace, "na yarda mana,."toh kin kyauta anmata, sai dai kuma wasa nike maki, saboda Ikhram ce fad'aman d'azun bayan kinyiman tsaki, sai na kirata, ta ceman haka" Sai da ta rufe baki, sboda son tare dariyar dake son kufce mata sannan tace, "innah, wai dama kaine?" Yanda tayi magana ya yi matuk'ar ba shi dariya gami da nishad'i, dan sai da ya dara sannan ya ce, "dan Allah fa?" Shima yanda ya yin ya sakata dariya, sai da ta zumb'ura baki, kamar suna facing juna sannan tace, "dagaske,.."uhmm, to meya saka kika yiman tsaki kuma kika katse wayar,.."ban gane numbern bane, kuma da nayi sallama aka yi shiru, shiyasa" jimm ya yi na wasu 'yan lokuta, kafin yace, "ai kin kyauta" Sosai Dr da Jiddah suka sha fira a wannan ranar, sosai kuma Dr ya yi mamakin yanda Jiddah ta saki jiki da shi, wata irin kewace ta baibaye su, bayan sun gama wayar...

Dan Allah ayi hak'uri da wannan, yau charger ta tazo, in sha Allah gobe zaku samu, sannan kuyi fata kada su hanamu wuta..

Qamshi✍️

AL'ADARMUWhere stories live. Discover now