Al'adarmu

10 2 0
                                    

AL'ADARMU

By Qamshi ✍️

🌟 FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION ✍️🌟

13...
A yadda Anwar ya shigo d'akin, ya tabbatar wa Jiddah dake zaune gaban mirror tana gugan fuska cewa wani abin ne ya kawo shi, sai dai ba tayi gaggawar tambayar shi ba, in da ta d'auki ido kawai ta zuba mai, ba tareda wani tunani ko b'ata lokaci ba, Anwar da ya k'osa ya koma parlor, saboda kar abokin Dr Farouq ya tafi ya barshi yace, "Aunty, Abban Abdallah na kira" daga hakan ya juya da nufin barin d'akin, "Kai wait!!" Ta fad'i hakan a d'an hasale, sai da ya dakata da tafiyar sannan ya juyo ya kalleta, bakin shi gaba alamun ta takura shi, "Haka ake sak'o?, ko haka yace kazo kace man?" Da kai kawai yayi mata alamun "Eh" Daganan yay ficewar shi, bakin shi na fad'ar "Allah kiyi sauri" Madadin taji haushi, sai ma dariya daya bata, saboda fahimtar da tayi na cewa Anwar d'in yana cikin farin ciki tun sanda Farouq yazo k'asar, Sai da ta gama goge fuska da cleanser sannan ta jawo madaidaicin hijabin da tayi sallar zuhr ta saka, ba tareda ta tsaya wani goge goge na powder ko shafe shafen jan baki ba, ta kama hanyar barin d'akin, domin kuwa kwata kwata yin a do irin yanda wasu daga cikin mata ke d'auka wayewa ba ajinin Jiddan yake ba, koda ta isa main parlorn gidan bata iske kowa ba, sai kawai ta sa kai izuwa guest parlor, don tasan acan zata tarar da yayan nata, duk da ko matsayin shi na d'an gida, Da sallama a bakin ta ta shiga d'akin, muryanta ciki ciki kamar me tsoron a jita, shima a dak'ile ya d'ago ya ansa, daga haka ya maida hankalin shi kan abinda yake yi, wato operating phone, abinda ya k'ara tabbatar wa Jiddah da kallon da takeyiwa Farouq d'in, wato masoyin waya ne shi, bini bini ka ganshi da waya, ko gajiya ba yayi. D'aya daga cikin cushing's d'in d'akin ta nema ta zauna, in da mamaki ya cikata, don tayi tunanin zata shigo taga Anwar da Abdallah a dak'in, amma sai taga a kasin hakan, "Toh ina ya shiga?" Ta fad'i hakan a k'asan ranta, ganin ta d'auki lokaci a dak'in amma har lokacin bata gaida shi bane, ya sata saurin kawar da tambayar da take yiwa kanta, tareda cewa "Ina yini" Yan zun d'in ma muryarta k'asa k'asa tayi maganar, bai ansa ba, har saida ya d'ago ya kalli yanayin ta sannan yace "Lafiya lau" Daga hakan d'akin ya d'auki shiru na wasu 'yan dak'ik'u, ko wannen su zuciyar shi na yimai sak'a da warwara, tunanin Dr a wannan lokacin shine yanda zai fara yiwa Jiddah bayanin zai koma nan da 3day's, daganan ba zai dawo ba har sai december, tunda saura 'yan satittika, sai dai a duk sanda ya yunk'ura da nufin fad'a matan, sai zuciyar shi ta dinga tuhumar shi a kan dalilin shi na son fad'an, "Amm" Bud'e bakin shi yayi daidai da d'age cotton d'in parlorn, hakan ya sa dole ya dakata, da sallama suka shigo d'akin, Anwar, Abdallah sai wani da Jiddah batasan ko wanene ba, "Madam" Bak'uwar fuskar ta fad'i hakan fuska cike da fara'a, a d'an rissine Jiddah ta ansa da, "Ina yini" Sosai ya k'ara fad'ad'a fara'ar kan fuskar shi, kafin yace "Mun same ku lafiya, lafiya lau" Tace a tak'aice, tana cigaba da wasa da yatsarta, "Har kun dawo kenan?" Dr Farouq yace hakan a tak'aice, "Ai ba muje da nisa ba" Abdallah ya fad'i hakan yana nunawa mahaifin shi siyayyar da Dr Majid yayi masu, shima Anwar nufar Jiddah yayi, "Daga ina?" Jiddah ta tambayi Anwar tana d'an hararar shi, "Shopping, ke sarkin shan chocolate ai gayanan an siyo mana da yawa" Kunyar da takama Jiddah ne tasata kasa cema Anwar d'in komai, sai zuramai ido da tayi, "Allah sarki Madam, ai bansan kina so ba da an siyo da yawa" Dr Majid ya fad'i hakan yana murmushi, "Die heart fan d'inshi ce kuwa" Anwar yace hakan, ita dai Jiddah shiru tayi masu, saboda nauyi da kunyar da ta isheta, dan sosai takejin cewa Anwar d'in ya kunya tata, Surutu ne ya sark'e a tsakin Dr Majida dasu Anwar, inda Jiddah Dr Farouq suka kasa kunnuwa kawai suna sauraren su, cikin su babu wanda ya tanka, sun jima suna firan, kafin Dr Majid yace "Ya kamata mu shiga mu gaida grandma d'in koh, to 3 fa" Ya fad'i hakan yana kallon wristwatch d'in shi, duk kanin su mik'ewa sukayi, ciko harda Jiddah, inda kusan itace ma tayi masu jagoran zuwa gidan Yabin, tayi hakanne da niyyarta nason ganin Ikhram, suna shiga side d'in Yabin kai tsaye ta nufi hanyar bedroom d'inta, "Gani nan" Taji Yabin ta fad'i hakan daga bayanta, kafin kuma ta waiga ta cigaba da magana, "A'ah yau Malamin malamai ne a sak'on nawa, ai na d'auka bazaka shigo ba, tunda naga dukka yaran sun shigo, harda ita babbar" Shidai be ce komai ba, sai sakin murmushin da zan iya cewa iyakar shi saman leb'en da yayi, "Haba dai granny, to idan bamu shigo ba wa zai bamu matar ma?, ai dolen mu" Dr Majid yace hakan cikin sigar zolaya, ganin fira ta fara sark'ewa a tsakanin Yabi da Dr Majid dama su yaran ne yasa Jiddah Kama hanyar bedroom d'in Yabin, don dama bata zauna ba, sanin halin Jiddah na rashin kunya da tsoro yasa Yabi zura mata ido kawai, don gudun yin abin kunya gaban abokin siriki.

"Ikhram" Jiddah ta kira sunan Ikhram a lokacin da ta isa gareta, don tunda ta shiga d'akin take sallama amma ko gezau batayi ba, firgigit Ikhram dake kwance tana bacci ta farka, saboda jin amon muryar da ta dad'e da sonji da gani, duk da tunanin ta yafi bata cewa gizo ne, sai dai duk da hakan batayi k'asa a guiwa wurin yunk'urawa ba, saboda matuk'ar zak'uwarta da son ganin mamallakiyar muryar, ita tanajin ma koda gizo d'inne tayi barka, tunda ko bata tab'ayi ba, Wani murmushi ne ya kufce mata a lokacin da idanuwnta su kayi tozali da fuskar yayar tata, take kuma hawaye ya biyo bayan murmushin, "A'ah fa, wannan ma ai iya shegene, Jiddah fad'i hakan tana b'ata rai, saida Ikhram ta share hawayen da suka fara wanke mata fuska sannan tace "Haka fa, tunda kina ganin Anwar kullum, kuma kinaji daga Yaya Khalipha da Ummah ai dole kiceman hakan" Ta kai k'arshen maganar tana juya baya, alamun yin fishi, Wani irin tausayin Ikhram d'inne ya dirar wa Jiddan, dan tabbas gaskiya ta fad'a, kuma a hakan ma da takeji daga garesun ba gamsar da ita yake ba, to inaga ita da ba taji kuma bata ganin kowa, idan ma tayi abinda yafi hakan ai ba laifi bane, ta mayi k'ok'ari, "To ni dai naji kiyi hak'uri, ya akai aka bari kika shigo?" Ikhram ta katse mata ban hak'urin da fad'ar hakan "Rakiya nayi" Jiddah ta fad'i hakan a tak'aice, "Wa kika rako?, Ya Farouq, kinsan yazo k'asar" Ta kuma bata ansa dashi a tak'aicen, "Waye kuma haka, karde kice wanda zaki aura?, Uhmm" kawai tace mata ta d'auke kai, "Oh shiyasa aka bari kika shigo nan d'in, wai Aunty wace irin rayuwa ce wannan, me su Abbah ke nufi da rabamu kuma su hanar mana ganin juna?" Ikhram tayi tambayar tana danne kukan da takejin yana taso mata, tun daga k'ahon zuciya, "Pls Ikhram mubar maganar nan, mu ci gaba da d'aukar hakan a matsayin destiny as Yaya Khalipha's said, kamarya Aunty Jiddah" Ikhram ta fad'i hakan tana mik'ewa, "Kamar yanda kikaji nace, ko kinada abinyi ne?" jiddahn tace hakan, daga haka kuma ta mik'e da nufin barin d'akin, don bata son famin tsohon gembon da take tunanin ya warke, sai dai kam ta lura matsawar ta zauna Ikhram d'in zata fama mata shi, Da sauri Ikhram ta bi bayan Jiddah, sai dai ko kafin tayi wani k'wak'wk'waran motsi Jiddan tabar d'akin, abinda yayi matuk'ar tada hankalin Ikhram, don tasan cewa b'acin rai ne yasa Jiddan barin d'akin, "Shikenan na sa ta tafi, ba tareda na bari munyi magana ba" Ta fad'i hakan tana fashewa kuka, kusan da rarrafe ta k'arasa saman gadonta, tana fad'awa ta kuma fashewa da wani irin kuka da duk mutumin da ya kwana ya tashi da d'igon imani a zuciya idan ya saurara sai ya tausaya mata.

A b'arayin Jiddah, tana shiga parlorn ta d'auke kai, ta kama hanyar barin parlorn, "Ke dai Allah besa kin iya gaisuwa ba ko Hauwa'un" Da Yabi tace ne ya dakatar da ita, sai dai koda ta dakatan bata gaisheta ba, "Ke kika sani" Yabin tace hakan tana kauda ido daga Kallon da take binta da shi, ba tareda son interfering ko nuna b'acin rai ba, Dr Farouq ya d'ago ya kalli Jiddan, inda karaf sukayi ido hud'u dashi, ita tafara d'auke idon ta, saboda tsaurin da nashi idanun suka yimata, "Haba madam ki gaisheta mana" Dr Majid ya fad'i hakan cikin sigar zolaya, me d'auke da alamun rashin jin dad'i, yi tayi kamar bataji shi ba, don har dukkanin su sun cire ran zata gaishetan, sai kuma can su kaji tace "Ina yini" Kamar wacce aka tsikara, Jinjina kai Dr Farouq yayi, saboda mamakin Jiddan daya cika shi, Ita ko Yabi ai dogon tsaki taja kafin tace "Rik'e kayar ki banso" Daga hakan ta mik'e tabar d'akin, dan sosai rashin kirkin Jiddan yayi mata zafi, a b'arayin Dr Majid ko cewa yayi, "Gaskiya madam baki kyauta ba, ai ko d'aki d'aya kuka kwana yakamata ace tunda kinjima bakinan idan kika shigo ki gaisheta, balle kuma ba hakan ba" Ita dai Jiddah bata cemai komai ba, sai wasa da 'yan yatsun hannunta da takeyi, "Ki bata hak'uri madam, cux iyaye ba abin wasa bane, kinji, dan Allah kar kice na takura ki" Dr Majid ya fad'i hakan cikin muryar da amonta yake a matuk'ar tausashe, yayi hakanne saboda yasan koda abinda yafi hakan tayi, wanda ya kamata yayi mata maganar ba zai tab'ayi ba, Cikin sanyin jiki ta mik'e tabi bayan Yabin, a hanyar kitchen sukaci karo da ita tana fitowa, wani irin kallo Yabin ta jefi Jiddan dashi, daga nan ta d'auke ido, ko kad'an hakan da Yabi tayi be sa ta russana ko tsorata ba, saima cewan da tayi "Ki yi hak'uri" Sai da Yabin tad'an murmusa sannan tace "Hak'uri kuma Maijiddah, ai hak'uri naki ne, keda aka matsawa kika gaisheni" Tana gama fad'ar hakan ta rab'e ta gefen Jiddah ta koma parlorn, "A'ah ba dai har zaku tafi ba" Tace ma su Dr da suka mik'e hakan, "Uhmm" Kawai Dr Farouq yace a tak'aice, Dr Majid ne yace lokaci na tafiya mama, gashi har an fara kiran sallah, kuma hakane, sai ku hanzarta" Yabi ta fad'i hakan tana bin Farouq da fuskar shi ta bayyana k'ararar kosawar shi da son tafiyar, jin jina bakar halayyar Farouq din takeyi, haka ta fad'a a k'asan ranta, an had'u an dace, "Toh sai kuma yaushe, may be kafin mu komai" Dr Farouq ya fad'i hakan yana tafiya, "Allah dai yasa" Kawai Yabin tace tana bin bayan su, har bakin k'ofar parlorn ta rakasu, inda Jiddah ke biye da bayanta, "Toh mu zamu shiga masallaci madam" Dr Majid ya fad'i hakan, a lokacin da suka kai side d'in su Jiddah, "A fito lafiya" kawai tace mai ta shige ciki..

Kuyi hak'uri da jina shiru kwana biyu, sannan ina barar addu'ar ku dan Allah, Allah ya kawo ma kasar mu da duniya baki d'aya zaman lafiya.

08152163536✍️

AL'ADARMUWhere stories live. Discover now