AL'ADARMU

21 3 1
                                    

*AM*

By Qamshi✍️

🌟 *FCW* *association* 🌟✍️

46...

Jin alamar motsi ya sakata bud'e ido, sai dai ko kad'an ba ta motsa ba, ballantana ya saka ran juyowanta, "Madam" Ya kira sunanta, bayan ya isa gareta, sai a lokacin ta motsa, harma ta yaye duvet d'in jikinta, sai dai har a lokacin bata yunk'ura ba, ganin ba tada niyyar yunk'urawan ne, ya sakashi zama bakin gadon, ai kam cikin sauri ta ja jiki, saboda jikin shi da ya gogi nata, murmushi ya yi kafin ya ce, "lafiya?" Ba tare da wani tunani ko jin kunya ba, ta ce, "tab'ani fa kayi" Baki bud'e ya tsaya yana kallonta, kafin can wata zuciya ta bashi shawaran yi mata mai uban, wato rungumota, ai kam take ya anshi shawarar tata, in da ya haye gadon, kamar wanda a ka aika, taga yana k'ok'arin d'agowa, cikin hanzari ta mik'e tana zumb'uro baki, wanda har hakan ya sa suka ci karo da juna, sai dai basu wani bugu ba, "ni fa banson haka" Ta ce mai hakan tana k'ara cinno baki, "to me kike so?" Ya tambayeta a tak'aice, "ni dai banso kana tab'ani" Ita ma ta bashi tata ansar a tak'aicen, "to ni wani abin ki kaji na ce, cewa fa nayi me kikeso na yi maki?" Ya k'ark'are maganar yana k'ok'arin rik'ota, "dan Allah Yaya ka bari, banso" Ta ce tana ja da baya, "to naji, amma dai yanzun ki cire wannan hijabin, ko ba kijin zafine?" Cike da mamaki ta ke kallon shi, kafin ta ce, "to in da ina ji, da ban cire ba,.."hakane iya magana, to ni na ce ki cire, ina son ganinki" Sai da ta zumb'uro baki, sannan ta ce, "to ni me zaka yiman?" Fuska a d'an cunkushe yace, "ki yi abin da na ce" Da ga haka kuma ya d'auke kai, dan kartayi wani abu da zai saka shi jin tausayinta, da zai sakashi cewa, "ta bari" Tun tana kallon shi tana zumb'urar baki, da tunanin zai juyo ya kalleta, har dai fahimtar cewa fa da gaske ya ke, ya sakata fara k'ok'arin ya ye hijabin, tana cirewan ko ta d'aure fuska, don ma kada ya ce zai tab'ata, shima d'aure fuskar ya yi, baima juyo ba, ballema ta saka ran kallon nata, sun fi k'arfin 2minute's a hakan, shi be ce mata ba, ita ba ta cemai ba, ganin bai da niyyar juyowa ne ya sakata cewa, "tun fa d'azun na cire" Rai a matuk'ar murtuke ya juyo, wanda har hakan ya sakata d'an jin shakkar shi, dan tun da suke da shi bata tab'a ganin shi a hakan ba, ya bud'e baki da nufin cewa, "i thought ba ki da bakine" Sai dai kuma abin da idanuwan shi su ka ganemai, ya sakashi kasa k'arasa maganar, tare da k'ark'are hayewa gadon, a d'an razane Jiddah ta yunk'ura, sai dai dakatawan da ya yi daga k'ok'arin rik'otan da ya ke yi, da cewan da ya yi, "wai what's wrong with you?" Ya sakata dakata,  tana kuma cinno baki ta ce, "to ai kaine,.."ni ne mene?" Ya katseta da cewa hakan, kafin kuma ya k'ara da, "C'mn malama zauna" Ta na b'ata rai, tana komai hakanan ta zauna, ba don ranta na so ba, a hankali ya matsa kusa da ita, wanda hakan ya saka bugun zuciyarta da zan iya cewa har ya farajin shi k'aruwa, "Oh Allah!!" Ya ce hakan a k'asan ranshi, kafin ya kai hannun shi saman cikinta da ya ga ya taso, wanda ya san ko kad'an ba haka ya ke ba ada, "me hajiya ke baki kina ci?" Shine tambayar da ya jeho mata, bayan ya cire hannun shi da ga cikin nata, duk da ko tuni ya fara d'ago halin da take ciki, "ni bana cin komai" Ta bashi ansa da shi a tak'aice, tana turo baki, "I see" Kawai ya ce, daga haka kuma ya mik'e ya nufi hanyar fita, har ya kai bakin k'ofa, ya juyo ya kalleta ya ce, "anjima zaki rakani" Daganan ya sa kai ya yi ficewar shi, tun kafin ya rufe baki, ta ce, "ni babu in da zanje" Meaning tun kafin ya fitan, "zaki maimaita anjiman" Ya ce hakan a k'asan ranshi, ba tare da ya juyo ya kalleta ba, kai tsaye d'akin hajiya ya koma, bayan fitar shi d'akin, in da ya iske kusan dukkanin su bacci ya fara kamasu, sai dai banda hajiyar, ita tana zaune a kan carpet ta rafka uban tagumi, tunanin nika barkatai sun yi mata yawo, babban abin da yafi damunta a yanzun, shine katsema Jiddah karatun da tayi, ita ta rasa me ya hau kanta a lokacin, da har ya sakata biyewa son zuciya da shawarar k'awarta, wato hajiya Sakinah, hak'ik'a hajiya Sakinah ta d'add'aurata a keken b'era, bama tun a kan bikin Farouq da Jiddah ba, a kan abubuwa da yawa, wanda sam sam d'amsil basira ya hanata fahimta, sai a yanzun da a kayi walk'iya komai ya haska, "Hajiya lafiyan" Da Dr ya ce ne, ya sakata d'agowa firgigi, kamar wacce a ka dungura, kafin kuma ta aro wani murmushin da zan iya cewa ko kad'an bai samu karb'uwa ba a kan fuskarta ta ba ta d'aura mata, "lafiya, me kagani?" Ajiyar zuciya kawai ya sauke, daga hakan kuma bai kuma cewa mata komai ba, dan baisan abin da zai ce mata ba, shi ya rasa me yake damun Umman ta su, tun lokacin da ta kira shi a lokacin da suka je Maiduguri, ya gane cewa ta samu matsala, sai dai rashin fuska da canjin da ta nuna mai ya sakashi kasa zama su yi magana akan sauyin nata, "a kwai wani abu ne?" Ta ce mai a tak'aice, saboda son katse shirun nasu, "um, um hajiya ba bu,.."ka da ka b'oyeman komai" Ta katse shi da fad'ar hakan, d'ago idanunshi ya yi ya kalleta, kafin kuma ya saukar da kai ya ce, "duk sun yi bacci" Ya ce hakanne saboda son kawar da zancen nata, dan shi sam a tsarinshi ba ya son tuhuma, ko da ko k'aramin yarone, ballantana kuma babba, babban ma mahaifiyarshi, shi ya sa ya kauda zancen, "umm sun kwanta, sai dai kuma ba abin da na tambayeka ba kenan" Sai da ya murmusa sannan ya d'ago da nufin cewa, "babu wani abu fa" Sai ga sallamar Sajudah da Nana a dak'in, ajiyar zuciya ya yi, dan dama dai neman hanyar sulalewa ya ke, ansa masu sallamar su kayi daga shi har Hajiyar, da ga haka ya yunk'ura da nufin barin d'akin, sai dai kuma me, ai Hajiyan cewa ta yi, "zauna ba mu gama ba" Ba musu ya koma ya zauna, su kuma su ka k'arasa shigowa, tare da samun wuri su zauna, "Abdallah har an yi bacci" Nana ta ce hakan a lokacin da idanunta su ka kai kan Abdallah da ke kwance a gefen Zee yana bacci, sai dai ba ta hango Zainab din ba, saboda lullub'ewan da ta yi, kafin kuma su gaishe shi, "ku kuma fa?" Hajiyan ta ce masu, tana hararar su, dukkanin su dariya su ka saka, kafin su ce, "gida mana,.."amma haka mu kayi da ku?" Ta ce hakan ranta a b'ace, Sajudah ce ta ce, "ki yi hak'uri hajiya, wallahi" Dakatar da ita ta yi, ta hanyar cewa, "ya isa" Daga haka ta mik'e da nufi hanyar barin d'akin, ta ce, "ka sameni parlor" Daga hakan kuma ta k'ark'are fita, ba tare da b'ata lokaci ba ya mik'e ya bi bayanta, jikin shi duk babu k'wari, dan be san me ya had'ata da k'annan nashi ba, bai kuma san abin da zaije ya tarar ba, guri ya samu a k'asanta ya zauna, dan ya fahimci yau uwar take ji ba abokiyar ba, dan takance, "ita Farouq abokin firar ta ne da d'ebe kewa" Idan an ce mata, "ba ta jin kunyar d'an fari, sannan ta cika sakarmai da yawa,.."kana jina?" Ta ce hakan a d'an tausashe, dan ta fahimci kamar ya shiga damuwa, ita kuma sam ba ta son ganin shi a hakan, girgiza kai ya farayi alamar, "I" Kafin kuma ya ce, "ina ji" Sai da ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta ce, "magana ni keson na yi maka a kan Maijiddah, wanda na san kasani, sai dai na tunatar da kai,.."to" Kawai ya ce mata a tak'aice, "Farouq wai a kwai hanyar da za a bi Maijiddah ta koma makaranta?" Ita ce maganar da ta fad'a, wacce ta doki dodon kunnen Drn, cike da mamaki kuma ya d'ago yana kallonta, kafin ya ce, "hajiya ban sani ba, amma zan bin cika, saboda ba deferring karatunta ta yi ba, ballantana a ce ta koma, yanzun dole ko zata samu damar komawa, sai na bi long processes,.."to gaskiya ina buk'atar komawan nata, dan ma dai a halin da ta ke ciki ba zan iya bari ta matsa ko nan da can bane" Ta fad'i hakan cikin yanayi na mantuwa, sai bayan ta fad'ar ne ta tuno, "wane irin hali ta ke ciki Hajiya?" Ya yi mata tambayar yana murmushi, don ya fahimci ba ta so ya sani ba, "in shiga ciki" Ta ce mai, saboda son kawar da maganar, Hamdalah ya yi bayan tafiyar, tare da fara imagination a kan yanda komai ya kasance a tsakanin shi da Jiddah, "wai shi yanzun har wannan d'an abun ya isa ya samar da k'wai, hak'ik'a ubangiji buwayine, gagara misali" Ya ce dukka hakan a k'asan rai, kafin ya mik'e ya bi bayan hajiyar, ko da ya shiga ya iske tana ta zazzagawa su Sajudah da suka k'i zuwa su tayata aiki masifa, bayan sun san hannu d'ayane, su kuma a nasu, sun k'i zuwanne, saboda su ma sun shirya masu tasu liyafar, shigar shi ta sakata dakatawa, in da ya ce mata "dan Allah ta yi hak'uri" Su ma kuma suka had'e baki wurin ba ta hak'urin, daga k'arshe dai don dole ta hak'ura, ba dan taso ba, sai da suka tabbatar da hucewar tata, sannan su ka fito da ta su bettern, ai kam hakan ya yi matuk'ar yi ma mata dad'i, in da ta ce, "ai da sun san za su yi nasu da ba su bari sun wahalar da kansu ba, ita da Jiddah, don ko bacci ba su koma ba,.."Allah sarki Jiddan ta ji warware kenan?" Nana ta ce hakan, "k'arfin hali dai irin nata, sai kace dai ba ki san ta ba,.."wai har yanzun jikin nata?" Dr da baisan da ciwon Jiddan ba ya ce hakan, "a'ah ai jiki Alhamdulillahi" Hajiya ta bashi ansa da shi, ganin d'akin ya fara d'aukar haramar surutune ya saka shi mik'ewa, tare da ce mata, "ta bashi key, shi zai shiga wanka" kwatancen in da bounch of key's din su ke ta yimai, ya je ya d'auka, daga haka ya bar d'akin, instead of ya tafi can d'in, sai kawai ya shige d'akin Jiddah da ke kwance tana game, jin an turo k'ofane ya sakata ijjiye waya, tare da d'agowa ta kalli k'ofa, fuska d'auke da murmushi ya k'arasa ciki, bakin shi d'auke da kalmar da sakata fad'uwar gaba, wato "me ciki" Pretending ta yi ta hanyar cewa, "hum'umm, ni wa ya cema ina da ciki?" Yanda ta yi maganar ya yi matuk'ar bashi dariya, don haka sai da ya d'an daran, sannan ya ce, "bari in zo in nuna maki" Ya k'ark'are maganar yana nufota, aiko har da gudun ta wurin mik'ewa, zagaye zagaye su ka dingayi, bawai dan ba zai iya kamata ba, sai dan yana son ya ga iya gudun ruwanta, gajiyar da ta yine, ya sakata zubewa kan gadon, tare da cewa, "ni dai ka k'yaleni,.."in k'yaleki bayan ban nuna maki cikin ba,.."to ai na yarda, shikenan ko" Ai tun kafin ta k'arasa maganar tata ya tare da cewa, "kin yarda dame?" Dan dama dai hasashe ya ke yi, "ni dai na ce ma na yarda" Ta yi maganar tana murmushi, dan sosai abin ya sakata nishad'i, shima ganin hakan ya sakashi jin dad'i sosai, "I dan fa baki bani ansata ba, Allah zan bud'e cikin na gani,.."kawai dai kanason ka bud'eman cikine, amma ai kasan ina da ciki" Wani irin murmushi ne ya sub'uce mai, wanda shi dai kai tsaye ba zai iya cewa, "ga ma'anar shi ba, amma dai yafi alak'anta shi da na farin ciki,.."ashe Jiddorh an kusa zama Ummah, to wani suna kike son a sakama babyn idan namiji ne, idan kuma mace ne wane suna kike so?" Ya yi mata tambayar cike da sigar wasa, wanda hakan ya d'auke mata hankali, ya sata mance kunya tace, "Ina son ka sakaman sunan Ummanmu, idan kuma namiji ne Abbah" Ta yi maganar fuska d'auke da murmushin farin ciki, "um nicest name's, babyna ta iya zab'e" Ya ce hakan b tare da ya kalleta ba, dan beson katse firar ta su, murmushi kawai ta yi daga hakan kuma ta yi shiru, ta cigaba da wasa da yatsunta, "wai me ya samu wad'annan yatsun nakine, da ko yaushe ki ke wasa da su?" Ya k'ark'are maganar yana rik'o hannunta, sanin cewa ko ta yi attempting k'wacewar ba saki zai yi ba, ya sata dole ta k'yaleshi, "kina son ki koma sch Jiddorh?" Ita ce tambayar da ya yi mata, a lokacin da ya ke wasa da yatsarta d'aya, sai da ta lumshe ido, sannan ta bud'e, tare da d'aurama fuskarta ta murmushi, ta d'ago ta ce, "ina so mana,.."da gaske?" Ya ce mata hakan a hankali, ita ma a hankalin ta d'ago ta ce, "Allah" Yanda ta yi maganar with full of serious all over her voice and face, ya sakashi sakin hannunta, tare da cewa, "bari in watsa ruwa" Kai kawai ta gyad'a mai, daga haka ya mik'e ya shige bathroom....

08152163536.

AL'ADARMUDonde viven las historias. Descúbrelo ahora