AL'ADARMU

10 2 4
                                    

*AM*

By Qamshi✍️

🌟 *FCW* *association* 🌟✍️

*43* ..
10:2pm. bayan Jiddah ta yi sallama da hajiya Baraka, harta kwanta wayarta ta fara ringing, da farko kamar ba za tayi picking ba, saboda bacci gamida rashin kuzarin da take tattare da shi, sai kuma ta yunk'ura, ta saka hannu ta d'auki wayar, ba tare da ta kalli screen din wayar ba, ta kaita kunne, tare da cewa, "Assalamualaikum"  Wata irin b'oyayyiyar ajiyar zuciya Dr ya sauke, don ko kad'an baiyi tunanin za tayi picking call d'in ba, muryan shi da ta doki dodon kunnenta ne, ya sakata saurin jaye wayan daga kunne, ta da kallon screen d'in wayar, kamar suna facing juna ta turo baki, tare da maida wayan a kunne, tace "ina yini,.."wannan yarinyar na son wahalar da tsohon mutane, gaisuwan ce ma ba za'a ansa ba, sai an ja man rai, an ya Jiddorh" Ya ce hakan yana murmushi, yi tayi tamkar ba ta ji shi ba, ta hanyar katse zancen nashi, da fad'ar, "ina Abdallah?" Murmushi ya yi, don ya fahimci zancen na shine ba taso, tare da cewa, "Abdallah ya d'anyi nisa, ya kike,.."ina lafiya, ya  Khairy,.."Khairy na lafiya" Drn ya ce, daga haka kuma dukkan ninsu su kayi shiru, sun fi morethan 10 second's a hakan, kafin Dr ya yi k'ok'arin breaking silence din nasu ta hanyar cewa, "an ceman ba ki da lafiya, amma da dukkan alamu kinji sauk'i,.."Alhamdulillah" Kawai ta cemai, daga hakan kuma wayar ta kuma d'aukan wani shirun, a wannan karon ita ce ta yi breaking silence din nasu, ta hanyar cewa, "ni fa bacci na ke ji,.."tun yanzun Jiddorh?" Drn ya ce, "toh ni me zanyi yanzun" Ta katse shi da cewa hakan, "fira ni keson muyi" Drn ya ce hakan, sai dai ko da ya yi maganar bata ce komai ba, abin da ya sakashi cewa, "kin ji" Cikin wata kalan murya mai masifar sanyin da shi kanshi bai san yanada ita ba, kuma idan a kace ya kuma maimaitawa ba zai iya ba, muryar da ta yi matuk'ar tasiri wurin karyar da zuciyar Jiddah, ta kuma sakata cewa, "toh ai na ji kayi shirune,.."ya ba zanyi shiru ba Jiddorh, bayan ko na yi magana ba tankani kike ba, kuma ni ina nan ina ta famar missing d'inki" Zumb'ura baki tayi tamkar wad'anda suke facing juna, kafin kuma ta ce, "hmmm,.."kin yi shirun" Da ya cene, ya sakata cewa, "ai ina jinka" Ranar dai a shiririce firan ta su ta k'are, although shi a wurin Dr fira ce mai matuk'ar mahimmanci, da ya saka a cikin ma'aunin da yake tunanin ba zai tab'a shareshi a babin rayuwar shi ba, sosai ya kejin yarinyar, ya ke kuma jin cewa ta shammace shi, shammata kalan wacce ko a mafarki bai tab'a tunanin ta ba, Jiddah fa, wannan k'aramar yarinyar" Abinda ya ke fad'a kenan a koda yaushe.
(Na ce a haka nan dai Dr😊).
   Hafsatu Muhammad, Ummu Mus'ab, Jiddorh👸, ku zo ku ba wannan Drn ansa, dan naga kamar yana son fad'ar wata magana ne, wai wannan yarinyar🙄.

Ku yi hak'uri dani da kuma halina, wallahi am very busy person, idan yau na yi tunanin zan samu hutu, sai aikin ya k'aru, har gwara working days ni a wurina, asibity kawai na ke zuwa, da na dawo bana komai sai dai in zan yi girki, amma weekend din ki nike yi sosai, wallahi ban da lokacin kaina, sai manage, shi yasa ku ke ganin short, short page's.

Na kuma gode sosai da addu'o'in ku ga paternal grandma d'ita, jiki yanata samun sauk'i👏🏼❤️❤️.

Ina son ku ku dukka fan's, musamman masu comments, voting.

WhatsApp commenter's ina kallon ku, Hafsat Muhammad, (ina godiya da kasancewarki cikin masoyana, Allah kuma ya ansa addu'o'in da kike yiman, kuma kema ya yi maki fiyeda hakan), Jiddorh, inata Jiddorh ban san takamai mai sunan ba, dalilin sanin sunan naki ma a comment d'inki ne da kike tambayar ranar da takwararki za suyi settling da Dr, anyway, (ina godiya da k'arfafaman guiwar da kike yi, Allah ubangiji ya bar k'auna, na san za kice requesting d'inki na k'arin read more's be karb'u ba, wallah ko kad'an ba haka bane, kuma in sha Allah zan k'ok'arta na k'ara, na gode k'warai).

Ummu Mus'ab, (kema ina godiya da comments d'inki, Allah ya bar k'auna❤️).

Kuma Wattpad commenter's ban manta da ku ba, amma ku zamu had'e a ranar k'arshe.

Ina son gyara posting d'ina, saboda haka ba zan dinga posting during weekends ba.

Qamshi✍🏻.

AL'ADARMUWhere stories live. Discover now