AL'ADARMU

8 0 0
                                    

58...

Allah sarki rayuwa, a ka ce a na bikin duniya a ke na k'iyama, haka zukata ke kasancewa, a lokacin da wannan ke farin ciki a lokacin waccan ke bak'in ciki, hakanne ta kasan ga zukatan su Jiddah da Ikhram, domin kuwa a lokacin da zuciyar Ikhram ke farin cikin ganinsu a tare, har da Ummansu, a lokacin Jiddah ta kasance cikin damuwa, in da duk wani motsinata ya kasance cikin fargaba gamida tashin hankalin yan da had'uwarsu da Faridah za ta kasance, yan da Ummansu za ta k'arb'eta, ko ma ta ce iyayensu gaba d'aya, da kuma sanin dalilin da ya sata barin gida, sosai tunawa da hakan ke haddasa mata damuwa, gashi ta kasa sanar da kowa, bayan Dr ba bu wanda ya san zancen, "Ummah wai ina babyn ta ki ne?" Ikhram ta katse tunanin Jiddah ta hanyar yima mahaifiyarsu wannan tambayar, "ai kuwa dai, ni ma ina ta so in tambaya, na ga banji motsinta ba" Jiddah ta yi tsumbul cikin zancen na su, ta na mai yin murmushin k'arfin hali, sai da hajiyan ta murmusa, sannan ta ce, "sun je d'akko Khalipha,.."kai wallahi ya Khalipha ya faya tsirfa, da gangan fa ya tattara ya wani tafi zaria, bayan ya san cewa yau za mu tahonan" Ikhram ta ce hakan cikin sigar tsiwa, "umm gaskiyane Ikhram, ai sai ki bari ya zo ki fad'amai hakan" Hajiya Marwan ta ce haka, dariya Anwar ya saka masu, wacce dukkanin su su ka rasa ta mecece, ba kuma tare da an tambayeshi ba ya ce, "wallahi na yi missing d'in Yabi" Ya k'arasa maganar ta shi yana mai gyara kwanciya a kan cinyar mahaifiyarshi, "mai Yabin ta yi Autan Ummah?" Hajiya Marwan ta ce mai, murmushi ya fara yi kafin ya ce, "Allah sarki Ummanmu, wallahi shiyasa kullum na ke k'ara missing d'inki, ina kewar wannan sunan over, and i do really missed Aunty Faridah that always used to said anya autan Ummah, anya  idan na zo wurinnan ba zanci gidanku ba, idan na k'i ta ce, Ummah wallahi ki yima d'anki magana" Sai da dukkaninsu su ka dara, although a kwai ciwo a cikin dariyar ta su, sannan Jiddah da ta ta damuwar tafi yawa ta ce, "Allah sarki Aunty Ridorh, yanzun dai mai Yabin ta yi?" A wannan karon ma sai da su ka kuma  darawar sannan Anwar d'in ya ce, "wallahi Aunty Jiddah ba dai son jin gulma ba, to ai Aunty Ikhram ta san me nake nufi,.."uban me kake nufi?" Ikhram ta katseshi da fad'ar hakan, cikin d'an tsawa, don ta san tun da ya fara wad'annan dararrakun na iya shege, to wani rainin wayon zai yi mata, ballantana kuma ya riga ya fad'i hakan, "to ni me na ce?" Anwar d'in ya ce haka, yana zumb'ura baki "to ni dai yanzun ku canzaman fira, tun da wannan d'in fad'a za ta zame maku" Hajiya Marwah ta ce haka, su na a haka Khalipha da babyn su ka yi sallama, kai tsaye babyn ta nufo wurin hajiya Marwah, sai dai ganin Anwar a kan cinyar Hajiyan ya sakata dakatawa, in da ta tsaya ta na kallon Umman nata, "Amnah zo mana" Hajiyan ta ce mata hakan, ta na mai mik'a mata hannu, ba musu yarinyar ta nufin wurin hajiyan, "Anwar ta shi kaba new Auta wuri,.."tabd'i, ai ko ni ba zan tashi ba, sai dai ta je wurin Aunty Ikhram" Anwar d'in ya cab'eta da cewa hakan, tun kafin ta kai k'arshen zancen ta, "zan fa tun kud'a ka,.."k'aton banza ta shi" Khalipha da ya kasa samun wata tarba saboda wannan dramar ya ce ma Anwar d'in haka, Anwar na zumb'ura baki ya mik'e, ba don ya na so ba, "ba ruwanka" Hajiyan ta ce ma Khaliphan, kafin kuma ta k'ara da, "ya hanyar?" Shafa kai ya yi ya ce, "hanya lau, ya mai jego,.."ya dai Ummanka?" Ikhram ta yi tsumbul cikin zancen na su, "Umman shin gaske" Hajiya Marwah ta ce, "Ummah wai su wanene wad'annan?" Amnah da ta kwanta akan cinyar Hajiya Marwah ne ta ce hakan a hankali, saboda ba ta so su jita, dalilin da ya saka hankulan su Jiddah da ma su ka mance da zancen yarinyar duk ko yanda su ke d'okin ganinta mai da dubansu gareta, murmushi Hajiyan ta yi, saboda yan da Amnan ta sak'a kai a tsakanin cinyoyinta, don ba ta so su ka jita ba, "Amnah yarana ne, ga Yaya Khalipha, ga Aunty Jiddah da babynta, ga aunty Ikhram da kuma auta Anwar" Hajiyan ta ba ta ansa da hakan, ta na mai yi mata nuni da duk wanda ta anbaci sunanshi, "gyad'a kai kawai Babyn ta dingayi, "Ummah babyn nan ta ki ta yi ta yi man kama da wata fuska da na tab'a sani, i can't remember but it seems familiar wallahi" Jiddah ta ce haka, ta na mai k'ara k'urama babyn kallo, "wallahi ni ma haka" Ikhram ma ta ce haka, gyad'a kai Hajiyan ta farayi kafin ta ce, "ko nima at first fuskan ta na yiman satan kallo da wata, amma da ga bisani na daina ganin kaman,."to fa, kina iya ganin mun santa, sai dai zumuncine da ya za ma sai a hankali ya sa mu ka kasa tunawa" Khalipha ya ce haka, ya na murmushi, suna tsaka da wannan firar a kayi sallama a bakin k'ofar d'akin, sai da aka ansa sallamar, sannan Hajiya Marwah ta ce, "shigo" Cike da girmamawa Hairatu ta shiga d'akin, "da ma Aunty Jiddah a kace in kira" Hairen ta ce hakan ba yan ta duk'a gaban Hajiya, "wanene ke kiran Jiddan?" Hajiyan ta tambayeta, "Jamilu ne ya ce man a na kiranta,.."je kice ko wanene ya shigo ciki" Hajiya Marwah ta katseta da cewa haka, tun kafin ta k'arasa zancen ta, "toh" Kawai ta ce, da ga haka ta bar d'akin, ba'a jima da fitan Hairen ba, wayar Jiddah ta fara ringing, don ko tambayar da Hajiyan ke shirin yi mata ba ta yiwu ba.

  Wani irin fad'uwar gaba ta riski kanta a ciki, tun kafin ma ta ga wanene ke kiranta, don tuni zuciyarta ta bata cewa Aunty Faridah ce, a lokacin da idanuwanta su ka tabbatar mata da abin da zuciyarta ta ai yana mata kuwa, ai zufa ce ta fara keto mata, gudun ka da Ummansu ko wani cikin 'yan uwanta ya ganta ne ya sakata saurin cewa, "network ya k'i ya barni na yi picking call d'in ma" Ta k'ark'are maganar ta na mai tashi da ga wurin da ta ke zaune, in da ta kama hanyar barin d'akin, hajiya Marwah da ta fara zargin wani abin Jiddan ke shiryawa ta ce, "sai ina?" A wannan lokacin kam ba zan iya baiyana kalan fad'uwar gabar da Jiddah ta riski kanta a ciki ba, don in da mutun zai matsa kusa da ita, ko da kuwa ba gaf da gaf bane, sai ya ji shi, "wayan zan yi picking" Jiddan ta bata ansa da hakan, cikin sigar shagwab'a, "a gama lafiya" Hajiyan ta ce, saboda tunawa da kalan kunyar Jiddan, sai ta yi tunanin k'ila Dr ne, duk da ba wai ta gamsu da hakan ba ne har k'asan ranta, kuma ta ga ba su jima da gama waya da su ba, "Aunty kin zo ne!!" Shine abin da Jiddan ta ce, cikin murya mai d'an sauti, bayan ta yi picking call d'in, ta na wayarne ta na cigaba da tafiya zuwa hanyar barin gaba d'aya part d'in, "na zo Jiddah, since na k'araso, amma fargaba ta hanani shigowa, da ma na yi attempting shigowa da farko, sai gateman ya ce man wanake nema?, na fad'amai Marwah, sai ya ke cewa mun yi making appointment da ita ne?, I was shocked Jiddah, da a yanzun ganin Ummah ya zamto sai an yi making wani appointment" Duk da damuwar da Jiddah ke cikin, amma hakan bai hanata darama maganar yayar tata ba, wai making appointment akan ganin Ummansu, su appointment manya, ta ce hakan a k'asan ranta, "serious fa na ke maki wannan maganar" Faridan ta katse mata dariyar tata da fad'ar hakan, "ki na ina ne yanzun?" Jiddan ta ce haka, bayan ta yi k'ok'arin ijjiye dariyar ta ta a gefe, "ina bakin gate,.."ok to ki jirani ina zuwa" Jiddan ta ce haka, daga hakan kuma ta katse wayar, ba tare da tunanin komawa ciki ba don saka hijabi, ta kama hanyar fita d'akin, "sai ina?" Murya mai kama da ta Hajiya Marwah ta jeho mata tambayar, ta k'aryata muryar ne saboda son yaudarar kai, cikin fad'uwar gaba, gamida tunanin ansar bata ta juyo, har muryarta na rawa, a lokacin da za ta ce, "compound,.."yin me?" Hajiyan ta ce haka, "Ummah dan Allah ki zo muje tare,.."wai mu yo me?" Hajiya Marwan ta katseta da cewa haka, "ki dai zo pls" Ta k'arasa maganar ta na mai had'e hannayenta wuri d'aya, alamar rok'o, ganin yan da ta marairaice mata ya saka ta amincewa, tare da cewa, "mu je" Ba tare da b'ata lokaci ba, don har hard'ewa Jiddan ta dingayi wurin tafiyar, su ka kama hanya, sun dib'i almost rabin compound d'in kafin hajiyar ta ce, "Hauwa'u" Sai da Jiddan ta juyo sannan tace, "na ji kamar kin ce compound?" Da kai Jiddan ta yi mata alamun "I,.."ai bud'e baki za kiyi ki man magana" Hajiyan ta ce mata haka, "Ummah bakin gate fa,."ai kin kyauta" Kawai Hajiyan ta ce, daga haka su ka cigaba da tafiya, a haka har su ka isa bakin gate, "ya ilahi" Ita ce kalmar da ta fito bakin Jiddah da ke gaba, a lokacin da idanuwanta su kayi tozali da yayarta ta, wacce duk ta yi bak'i, ta kuma rame, sosai Faridan ta zama tamkar ba ita ba, in har ba ka wani santa sosai ba, a ka fad'a maka cewa ita ce, ba zaka tab'a amincewa ba, don sosai sauyin kamannin na ta ya yi yawa, "Aunty" Shine abin da Jiddan ta ce, ta na mai sakin wayarta a kan interlock, ta ke kuma kuka ya kufce mata, ita ma Faridan cikin kukanta ta ce, "Jiddah" Jin muryar tata ya saka Hajiya Marwah da har yanzun ba ta san wace Auntyn da Jiddah ke nufi ba suman tsaye, ta ke kuma ta ji bata buk'atar ganin ko wacece, in da ta juya da nufin komawa ciki, Faridan da tuni ta shigo cikine ta ce, "Ummah" Ta k'arasa maganar ta na mai zubewa k'asa, "Ummah ki ya feman" Faridan ta ce hakan, ta na mai had'e kai da guiwa, "Ummah dan Allah" Jiddah ta ce haka ta na rik'e k'afar Hajiyan, hayaniyarsu da ta kai cikin gidanne ta jawo hankalinsu hajiya babba, da su Aunty da ke guest parlor, in da duk su ka fito compound d'in, ai su dinma dukkanin su suman tsaye su ka yi, saboda ganin Faridan, Aunty Aysha ce ta rik'o Faridah da ta had'e hawaye da majina wurin rok'on Umman na su, 'ta shi mu je ciki, ai magana a nan ba zata yiwu ba" Auntyn ta ce hakan, sai dai tashin hankalin ganin yan da ita kanta Hajiya Marwan ke kuka ya sa ko jin ta ba ta yi ba, "mu je Faridah" Hajiyan ta kuma cewa haka, ta na mai k'ara rik'o Faridan, a wannan karon Faridan ta mik'e, sai dai kuma daky'ar ta ke tafiya, iya ta shin hankali wannan a halin sun shige shi a wannan ranar, ba ma kamar Hajiya Marwah da abin da ya faru a can baya ya dawo mata, wato message d'in da ta gani a wayar Faridan, "da ma Hauwa'u ta san in da Faridah ta ke, ta san komai a game da b'atan Faridah, amma ta kasa sanar da ni, a she dama da nake tunanin komai ya dai daita yaudaran kaina nake yi, a she dama kallon shashasha Jiddah ke yiman, a gaban idanuwanta mahaifinsu ya sakeni, amma ta kasa sanar da ni in da take, "ya Allah!" Ta ce hakan a baiyane, ta ke kuma ta yanke jiki ta fad'i, abin da ya k'ara hautsina lissafin Fam Dumno.....✍️

Qamshi✍️.

AL'ADARMUWhere stories live. Discover now