AL'ADARMU

10 0 0
                                    

59..
Mayafai kawai su Aunty Aysha su ka yayyafo, su ka tafi kai ta asibity, sosai Jiddah ta d'aga hankalinta, don ta na ganin ita ce silar komai, in da ita kuma Faridah ta juya da nufin barin gidan, don ta tabbatar da cewa ganinta ne ya saka Umman ta su cikin wannan yanayin, shikenan ta hak'ura, za ta koma ta cigaba da zama da Abban Aminah, ko da kuwa zai kasheta ne, "kee!!" Shine abin da a ka ce da ga bayansu, wanda ya saka Faridan dakatawa, duk da ba ta yi attempting juyowa ba, "Wacece ke?" A karo na biyu, muryarta ta kuma yin magana, har a lokacin ba ta ji a ranta za ta waigan ba, sai dai ta sa hannu ta share hawayen kan fuskarta, '"Ya Khalipha aunty Farid.." Jiddah ta bud'e baki da nufin fad'ar hakan, sai dai tashin hankali, gamida tuna a halin da a ka fita da Ummansu, ya saka harshenta hard'ewa, in da ta kasa k'arasa zancen na ta, don dole ta yi shiru, ba tare da ya k'arabi ta kansu ba, ya nufi daidai sit d'in da Faridan ke fuskanta, shi kanshi suman tsaye ya yi, a lokacin da idanuwanshi su ka yi mai tozali da Faridan, "ya ilahi" Shine abin da ya ce a k'asan ranshi, a baiyane kuma ya ce, "Aunt, Aunty!!" Ya k'arasa maganar ya na mai nunata da d'an yatsa, gyad'a kai kawai ta dingayi alamun, "I, ni ce" Don ba ta tunanin nauyin da bakinta ya yi mata zai barta ta tankamai, "da gaske Aunty Ridorh ce, da ma zamu k'ara ganinki, ina kika shiga, waye ya d'auke ki?" Sune  tambayoyin da Khaliphan ya jeho mata a jere, cikin tsananin mamaki, fargaba gami da farin cikin sake sakata a idanun shi, share hawayen kan fuskarta ta fara yi, kafin ta ce, "gani Khalipha, kuma a yau zan koma.." Ta bud'e baki da nufin cewa hakan, sai dai rungumar da a ka kai mata ta baya ya sakata kasa k'arasawa, "Ammi, Ammi, ammi waye ya nuna makinan?" Baby Amnah ce ta jeho mata tambayoyin, ta na mai k'ara k'wak'umeta. (Ya Allah, idan na ce zan iya baiyana kalan shock d'in da both of them su ka tsinci kansu a ciki, na yi ba'a, saboda ya nayine da baki ba ya isa misaltawa).

Cike da rud'u, ga mi da mamakin ganin Amnan Faridah ta duk'a, "Amnah me kike yi a nan, wa ya kawoki nan?" Ta yi mata tambayoyin ta na mai duddubata ta ko ina, tamkar wacce ta ga wata sabuwar halitta, "ni da kaina, Ammi ba na son Abbah ya na dukanki, pls ki ce mai ya dena" Amnan ta ce ma Faridah da a yau su Jiddah ke gasgata abin da idanuwansu su ka jima su na gaya masu a kan kamannin yarinyar, "it mean babyn Ummah daughtern Aunty Faridah ce!!" Ikhram ta yi jarumtar kauda shirun yayyan nata ta hanyar cewa hakan, ta yi tambayar ne a lokacin da ta ke nufa wurin Auntyn ta su, dukkanin su dakatawa su ka yi, in da su ka tsaya zaman jiran ansa da ga Faridan, sai dai ko kad'an ba ta yi yunk'urin fad'ar ba, sai ma k'ok'arin barin gidan da ta ke yi, hannunta rik'e da na Amnan, "ina za ki da ita?" Khalipha ya sha gabanta ya na mai yi mata tambayar, sai da ta murmusa sannan ta ce, "'ya ta ce fa Khalipha, da ma akwai shamakine a tsakanin uwa da d'anta?" Ta jehomai tambayar ta na mai sharar hawayen da su ka kasa tsayawa, "ba bu, amma ke ki ka kawota, ko ko kunyi da Ummah ce wa za ki d'auketa ne, da ma kin zo ne ki kuma rusa mana farin cikin gida, ke wace irin mutun ce?" Khaliphan ya jeho mata dukkanin tambayoyin cikin muryar da ke baiyana tsananin b'acin ran da ya ke ciki, don ya na ganin kamar hakan da za ta yi rainin wayone, ta ya za'a yi ta zo ta ce za ta d'auki baby, ba yan ta yi sanadiyyar kai mahaifiyarsu asibity, ko tunanin zuwa dubata ba ta yi ba, it mean haka za ta dinga yi masu kenan, a can baya ta gudu ta bar su da masifa da tashin hankali, wan da har hakan ya haddasama mahaifiyarsu barin d'akinta, yanzun kuma ta ta kaita asibity, za kuma ta koma, to me hakan ke nufi?, kenan ta zone saboda ta ji labarin Ummansu za ta koma d'aki, shikenan idan Abbansu ya ji ya ce dama Umman ta su ta san in da take, daganan maganar komawan ta fasu, to tabbas ba za su tab'a yarda ba, da ga kan wannan za'ayita ta k'are in sha Allahu, don zai ari wannan jarumtar da su Jiddah su ka dad'e su na advising d'inshi a kanta, amma ya k'i ji, dole ne ta zab'i d'aya, nan ko can, idan nan d'inne to dole ta zauna ta fad'a masu in da ta je, da kuma in da ta samu yarinya, idan kuma can d'inne sai ta koma, daganan kuma ka da ta sake ta kuma dawo masu, "Khalipha ni, ni Khalipha, ni ka ke fad'ama wad'annan maganganun?" Ta yi tambayar ta na mai nuna kanta da yatsa, tare da kuma sakin murmushi, wan da ya fi kuka ciwo da k'ona zuciya, "an fad'a maki!!" Khaliphan ya bud'e baki da nufin ce mata hakan, sai dai fashewa da kukan da Ikhram da Jiddah su ka yi, ya saka shi kasa fad'ar hakan, in da ya bugi goshin shi, tare da juyawa zuwa ciki, dan sosai ya ke jin k'una a k'asan zuciyar shi, shikan shi ya san jarumta kawai ya ke yi, "dan Allah Aunty mu shiga ciki, mu je ki jira a dawo da Ummah, kin ga yanzun idan kika tafi ba za ta ji dad'i ba, pls" Ikhram ta ce hakan, ta na mai rik'eta, girgiza kai kawai ta dingayi alamar a'ah, don ba ta tunanin za ta iya k'ara koda minti 1 a cikin gidan, "Aunty dan Allah" Su ka had'e baki wurin cewa hakan, sai da ta murmusa sannan ta ce, "a ina, ba dai a inuwa daya da Khalipha ba?" Ta yi masu tambayar fuskarta na baiyana murmushin ya k'e, "a inuwa d'aya da shi, wallahi Aunty kar ki yi mamaki idan na ce maki yah Khalipha ya na can ya na kuka" Ikhram ta ce mata hakan, "hmm!, shi Khaliphan, sai ka ce wani Anwar ko baby Noor, wai ina su ke ne?" Ta yi tambayar a wannan karon ma fuskarta d'auke da fara'a, "duk sun yi bacci" Ikhram ta ba ta ansa da hakan a tak'aice, "mu je ciki Aunty" Jidda ta ce mata hakan, a wannan karon ba musu ta bisu su ka shiga ciki, kai tsaye b'arayin Hajiya su ka kaita, in da su ka tarar da su sunata famar bacci, "wai nan a ka kawo su?" Jiddah ta yi tambayar ta na mai kallon Ikhram, sai da Ikhram d'in ta murmusa sannan, ta ce, "I, da Ummah za ta fito ne ta ce mu zo nan, to da mu ka jiku shiru shine mu ka barsu, dama kuma tuni Anwar ya yi bacci,.."Oh Allah" Jiddah ta ce haka, ta na mai samun wuri a kan sopa, "na yi mamaki da na ga banga hajiya a waje ba, a she ashe" Aunty Faridah ta ce haka ta na murmushi, tare da nufa in da baby Noor ya ke, "Masha Allah" Ta ce hakan a k'asan rai, a lokacin da ta d'auki babyn, "aunty kin ga babyn Aunty Jiddah" Ikhram ta ce haka ta na murmushi, "umm na gani Ikhram, ubangiji Allah ya raya mana mai sunan Abbah,.."ameen" Kawai Ikhram d'in ta ce a tak'aice, da ga haka kuma firar ta su ta canza salo, in da su ka fara yi mata tambayoyi a kan Amnah, da kuma in da ta tafi tabarsu, da dalilin barin gidan da ta yi?, although sun san dalilin, sai dai suna son k'arin bayani, amma ko gezau ba ta yi ba, bayan murmushin da ta dinga saki mai had'e da hawaye, idan ta kalli wannan sai ta kalli waccan, at the end ma dai fashe ma su da kuka ta yi, in da dole ta sa ka su ka k'yaleta, tare da ce mata ta tashi ta yi wanka, a wannan karon ba ta b'ata lokaci wurin yin hakan ba, ta na fitowa kuma su ka sa mata abinci, sai dai ko da su ka sa matan ba ta ci ba, sai tea da ta ce ma Ikhram ta had'o mata, ba tare da b'ata lokaci ba ta mik'e ta je ta had'o matan, an ko ci sa'a ta sha shi sosai.

AL'ADARMUWhere stories live. Discover now