YADDA ƘADDARA TA SO 5

29 4 0
                                    


⭐️YADDA ƘADDARA TASO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
©By Sai Kaska
*proud of my first novel*
*BABI NA BIYAR(5)*
Ya dinga wuce falukan dake turakar fulani kafin ya iso falo na biyun karshe, abinda ya gani ya tayar masa da hankali, jiki a sa6ule yayi sallama, fulani dake risgar kuka ta ɗago da kai ta kalli inda yake, hakama me martaba, zuwa lokacin nadra ta bar falon dan bazata iya jurawa ganin mahaifiyar tata na kuka ba.
kansa a kasa ya ƙaraso cikin parlon ya zauna a kasa kusa da kafar mai martaba, yana duƙar da kansa, me martaba kuwa tunda ya shigo yake ta binsa da kallo har ya zauna a kusa da ƙafar tasa, duk da ya jima bai ganshi ba, amma kuma yaga cewar ya rame sosai fuskarnan tasa babu komai sai dogon hanci, gaishe da me martaba yayi me martaba ya amsa a nutse.
"ina kwana ranki ya daɗe" fulani ta share hawaye, cikin dakiya tace
"lafiya tafeedah, fatan ka tashi lafiya"
"lafiya kalau"
"ina zakaje naga ka shirya"
"jawan angwancen da za'ayi zanje"
"kaji sauƙin jikin naka ne?"
muryar mai martaba ta tambaya, tafeedah ya ƙara ƙasa da kansa.
"eh ranka ya daɗe banajin komai"
"tashi kaje, nayi maka lamuni"
"aa bakaci abinci ba"
"zamuci tareda muktar"
ya faɗi bayan ya miƙe har ya fita daga parlon basu sami damar kallon kwayar idonsa data sauya kala zuwa ja ba, sun glasses ɗin daya saka a aljihun sa ya zaroshi ya saka a idonsa, dan yayi duk yanda zaiyyi amma idon yaƙi komawa yanda yake.
Yana taka ƙafarsa a parlo na farko ya motsa kunnensa ta yanda zai iya jiyo abinda ake tattaunawa a parlo na biyu, muryar me martaba ya tsinkayo yana bawa fulani haƙuri sbd kukan data ci gaba dayi.
Sai ya motsa kunnen nasa yaci gaba da tafiya, ƙarfin ji na ɗaya daga cikin baiwar da allah yayi masa, ga kuma baƙin ruhin dake jikinsa dake ƙara masa.
Daya fita waje ya iske tawagar mai martaba, suna ganinsa suka miƙe sunata zabga ƙirari, murmushin dole ya ƙirƙiro yayi musu yana amsa gaisuwar tasu.
MARYAM POV.
"ke dallah ki tashi muje "
Muryar badar ta faɗi yayinda take kallon maryam ɗin wadda ke zaune tana yankewa auta farce, maryam ta ɗago ta kalli badar dake tsaye ta ci uwar kwalliya kamar me shirin shiga hasar sarauniyar kyau.
"wai zuwan dole ne ?, sanin kanki ne ni ba zuwa kallon hawan doki nake ba"
Kuma haka ɗin ne, dan koda wasa maryam bata zuwa kallon hawan dokuna, sbd tsabar tsoranta, tsoran bingidar da ake harbawa kafin sarki ya ƙaraso dama shi kansa dokin tsoransa take ji.
"Dan allam maryam ki tashi mu tafi, ni yau so nake sai kinga TAFEEDAH"
Tafeedah ?, sunan ya maimaita kansa a cikin kanta, ita sam bata taba ganinsa ba koda sau ɗaya, amma babu budurwa da bazataji zancensa ba a bakinta, hatta da badar kuwa, itama batada zance sai nasa, dan haka yasa yauma da aliyu yace bazai samu damar zuwaba ranta ya mata fari, dan yau tafeedah zai hau hawan angwancen da ake yau, sbd auren ƴar sarki da ake, ko ba komai zata samu ta kalli kyakyawar fuskarsa, wannan ma kaɗai ya isheta.
"badar waini wannan tafeedahn annabi ne ?, da zaki dage akan sai nawani je na ganshi ?"
"aa fa, ba annabi bane, kinsan allah maryam dan baki ganshi bane, da zarar kin ɗora ido akansa wallahi zaki fara sansa, ba'indiye ne fa, najima wai anacewa babarsace ba'indiyar, shiyasa ya biyo kamarta"
Maryam taja tsaki a cikin ranta, badar bazata gane ba, itafa bazata iya wahalar da kan taba tana yankawa kare ciyawa, yau yankawa kare ciyawa mana, inba yankawa kare ciyawa ba me yasa zaka zo ka saka wanda baima san kanayi ba a rai.
"nifa danma bansan username ɗinsa bane a social media, da na ɗauko hotunansa da yawa na aje a wayata"
"dama kin kama hanyarki kintafi, dan wallahi ni ba zuwa zanba, kinga yanzu inayin abincin rana zan tafi shagari gidan anti fati"
"ke ki jirani na dawo sai mu tafi, kinsan gidanta kusa da gidan tafeedah ne, idan allah yasa nayi sa'a sai kiga mun haɗu"
ta faɗi idonta na haskawa da ƙyallin murna.
Yanxu tsakin kam a fili tayi, ta rasa meke damun kan badar,to ita yau bazatabi ma ta ƙofar gidan nasa ba.
HANAM POV.
*Da misalin ƙarfe 10 na dare*
Hanam ce take taku zuwa inda ta aje motarta, bayan ta fito daga wani shopping mall, gabanta ne yayi mummunar faɗuwa sbd wani mutum data gani a gabanta hannunsa riƙe da wuƙa yana nunata da wuƙar, aryaan ta ƙanƙame wanda ke cikin baby carrier ɗinsa yana bacci.
"give me the baby"
"what!!!!"
Ta faɗi a kiɗime cikin ƙaraji
"yes i say give me the bab...."
Dukan da wani yazo ya sakar masa a baki wanda daga ita har shi basu ga tahowarsa bace tasa shi ya haɗiye maganar dake bakinsa, daga nan kuma ya shiga dukansa tako ta ina, zuwa lokacin Aryaan ya farka sai kuma yasaka kuka, Hanam ta ruɗe tana kallonsu, daga me dukan har wanda ake dukan babu wanda Hanam ta samu damar ganin fuskarsa.
"Dan allah Kayi haƙuri wallahi wani ne waishi kamal ya bani dubu ashirin yacena karbo masa yaron"
Kalmar 'kamal' daya ambata ita ta bawa Hanam Mugun mamaki, ashe tsanar da 'yan uwan nata suka mata ta kai haka ?, yanzu ita me ta musu a rayuwa haka ?, ta juri abubuwa da yawa marasa daɗi a rayuwarta amma hakan bai isheta ba sai ƴan uwan nata sun ƙara mata da wani, me yasa ?, me yasa hakan ke faruwa da ita?.
"Oga pls"
Muryar wanda ake dukan nasa ta ƙara fitowa, kafin wanda yake dukan ya sake shi, da gudu wanda ake dukan ya miƙe ya falfala.
Kuma har yanzu Hanam bata samu damar ganin fuskar kowane ɗayansu ba, sbd shi ɗayan fusakarsa a rufe take da mask, ga kuma duhun dare kuma parking lot din babu haske sosai, shi kuma wanda yake dukan ya bata baya, ba tareda ya juyo ba yaci gaba da tafiyarsa.
"I can't thank you enough"
Ya tsaya amma bai juyo ba sai kuma yace
" dont mention it"
Ya ci gaba da tafiyarsa.
***
A fusace Hanam ta shigo cikin parlon gidan nasu, Aryaan goye a bayanta cikin baby carrier ɗinsa wadda zuwa yanzu ta juyata baya.
Kamal na zaune a kan 2 seete yana duba wayarsa jifa-jifa sbd yana jiran shigowar saƙon ɗan ta'addan daya saka ya ƙwato masa yaron Hanam, dan tun bayan data mareshi ya saka a ransa cewa ba zai barta ba, sai ya ɗau fansar abinda tai masa, ya kuma ƙudurta a ransa cewar sai ya rabata da shegen ɗan nata domin shine farin cikinta.
Kamar da akace ya ɗago kansa ya kalleta tana tahowa zuwa cikin parlon a fusace, da sauri ya miƙe sbd irin kallon da take masa, Mero da kishiyarta Hajjo da kuma sauran yaransu duka suka miƙe.
Tana ƙarasawa gaban Kamal batayi wata-wata ba ta ɗauke shi da mari, ya ɗora hannunsa akan kuncinsa na dama inda marin ya sauƙa, kuma bata barshi ya gama jin raɗaɗin zafin marin nata ba ta kuma sakar masa wani marin, a dai-dai lokacin kuma abba daya dawo ɗazu da rana ya sauƙo daga sama, kuma a lokacin ne Aryaan ya canyara kuka, bata bi ta kan Aryaan ba ta fara faɗin.
"Dan na mareka shine kasa aje a satomin ɗa ko ?"
Cike da mamaki kowa ya shiga kallonsu, sai kuma taci kwalarsa
"To da kasa a sato maka shi uban me zaka masa huh?, faɗa min mana ?"
Ta faɗi tana jijjiga shi sai kuma ta sake shi, ta nuna shi da ɗan yatsa "kana ji ko ?, idan har ka kuskura ka taba koda silin gashi ɗaya na ɗana ne, sai na ɗaye maka fata, sai na tabbatar da na koya maka darasin da baka ta6a sanin da akwai irinsa ba a duniya, ɗana yafi ƙarfin ta6awarka"
Ta matsa gaba dashi dab da dab, ta ɗora ɗan yatsanta akan sa tana faɗin.
"Put this at the back or no, not at the back, put it at the front of your mind"
Tana kaiwa nan ta bar wajen a fusace tayi sama, ta bar kowa na wajen da mamaki, tanajin Abba daya rufeshi da faɗa, mahaifiyarsa kuma tana kareshi kamar kullum.
Kai tsaye ɗakinta ta shiga, wanda komai na cikinsa yake kalar fari da brown, fari shine kalar datafi so, dan a gaba ɗaya kayan datake sakawa babu wanda babu kalar fari a ciki, ɗakin Aryaan wanda yake haɗe da nata ta shiga.
A da ɗakin maƙotan ɗakinta ne, bayan ta dawo daga USA ne Abba yasa aka rufe kofarsa ta waje, aka fasa masa ƙofa daga ɗakinta. Kasan cewar ɗakin bashi da kofa kanta tsaye ta shiga, hand bag ɗinta ta aje akan kujera, har lokacin Arya na canyara kuka, belt ɗin baby carrier ɗin nasa ta shiga ballewa sannan ta sauko dashi.
Ta zauna akan wata kujerar da ban da wadda ta aje jakarta ta saka masa mama a bakinsa, nan take yayi shiru ya shiga tsotsa, tana shafa kansa tana faɗin
"Sssssshhhhhhhh!"
Ta sunkuyar da kanta tana kallon cikin kwayar idonsa, wadda take tuna mata da wani dare daya faru a rayuwarta a baya, a har kullum Idan ta kalli blue eyes ɗin nasa yana tuna mata da daren.
Sai kuma ta kawar da idonta ganin shima yana kallonta, hannunsa ya ɗago ya saka a cikin bakinta, tayi kamar zata cijeshi yayi sauri ya cire daga bakin nata, tayi dariya tana taba kumatunsa
"Ka dena kuka Arya, babu wanda zai rabaka da Ammin ka, Amminka tana tareda kai, bazan taba bari wani abu ya sameka ba, haza wa'adi ilak (wannan shine alƙawarina gareka)".
***
"Maman babanta"
Muryar Abba ta faɗa cikin shirun da ɗakin nasa ya ɗauka, bayan Aryaan ya gama shan maman tashi tayi tai masa wanka, tun tana masa wankan ya fara bacci, dan haka tana shafa masa mayukansa ta kwantar dashi a cot (gadan yara na katako), wanda ke cikin ɗakinta, babu bata lokaci ya fara bacci.
Itama wankan ta shiga sai kuma kiran Abba ya sameta, dan baka ta fito ta saka kayanta ta fita.
"Maman babanta magana fa nake!"
muryar Abba ta ƙara katse mata tunanin da take neman zurmawa ciki, a hankali ta ɗago da kanta ta kalleshi, yayinda take zaune a kasan ƙafafunsa, kwata-kwata idan ka kallesu bazakace ƴa da uba bane, sbd shi Abban baƙine wulik, ko a cikin baƙaƙen africa shi baƙine, ita kuma farace, fara sosai farinta yafi irin farin fararen africa, amma kuma farin nata irin na indiyawa ne, kasan cewarta halp cast.
"Na'am abba"
"Maman Babanta ɗazu Jabeer ya kirani, kuma ya faɗa min duk abinda ya faru tsakaninku, Maman Babanta me yasa bazakiyi aure ba ?, ya kamata ace kinyi aure, 25 kike fa ya kamata ace kinyi aure"
Hanam tayi murmushi me ciwo
"Kasan ɗazu da safe daya zo office me yace min ?"
Abba ya girgiza kai, taci gaba
"Cewa yayi ya kamata ace na tuna alƙawarin da mukayiwa juna, zamuyi aure, mu rayu tare, mu tsufa tare, mu gina gidanumu dagani sai shi, sai kuma yaran da zamu haifa"
Abba yayi wani irin murmushi
"To Hanam miye abun aibu anan ?, ai wannan abun farin cikine Maman Babanta"
Ta girgiza kai
"A'a Abba wannan ba abun farin ciki bane"
"amma me yasa Hanam?"
Abba ya tambaya girarsa na haɗewa waje guda, alamun kokonto.
"Lakin abba fi kul hazal kalam wain Arya ?"
(Amma abba a duka wannan zancen ina arya ?) .
Ta faɗi tana hawaye, kuma cikin harshen larabci, Abba ya ruɗe yana sauƙowa kasa kan carpet kusa da ita, duk abinfa zai saka Hanam kuka to ba ƙarami bane, akwaita da jajircewa, ta iya haɗiye baƙin ciki tun tana ƙarama.
"Abba wain Arya?, huwa biddu ya illi unu iza jawazna ana rah utruk Aryaan ?"
(Abba ina arya?, yana nufin idan munyi aure zan rabu da Aryaan?)
Tayi maganar a sigar tambaya, amma ba tambayar bace.
"ihdi Hanam shrahili kilshi bi tafsil"
(Nitsu Hanam, kiyimin bayanin komai dalla-dalla)
Shima ya tambayeta da larabcin, dan shine ma wanda ya koya mata, sbd shine mother tongue ɗinta, Hanam ta ɗora hannu akan goshinta tana kurzawa, wanda hakan sararta ce tun tana ƙrama, sannan ta share hawaye wani na, sauƙo mata.
"Abba nima fa mutumce, inada feelings, inajin bacin rai, nasan farin ciki, inajin haushi idan aka bata min rai, Abba duk rayuwar da babu Arya bazan iya yinta ba, Abba bana san rayuwar da babu Arya sam, abba Arya shine komai nawa bayan kai bani da wani kamarsa"
Ta ja majina tana share wani hawayen.
"Yanzu Abba ƙaddara nida jabeer munyi aure, kuma na haifa masa yara, kana ganin zaiso Arya kamar yanda zaiso sauran yaransa ?, ko iyayensa zasu soshi kamar yanda zasu so jikokinsu na jininsu ?"
Abba ya girgiza mata kai cike da tausayin ƴar tasa
"Abba duk mijin da zan aura baya san Arya nima bana sansa, kuma bazan iya na aureshi ba, Abba Arya shine gobena, Arya ya zama wani ban gare na labarina wanda bazai cikaba idan babu shi".
Ta kuma jan majina tana share hawayen dayaƙi tsayawa taci gaba da cewa.
"Abba me yasa kowa yake wasan kura da zuciyata ?, me yasa ni tawa ƙaddarar tazo da tsauri ?, abba me yasa komai nawa babu abu me daɗi ?, kaida Arya kune kaɗai abu me kyau da kuka faru a rayuwat me yasa ake so na rabu da ɗaya ?"
Abba ya rungumeta yana hawaye shima, fashewa tayi da kuka tana riƙe shi, daga mahaifiyarta ya kamata ace ta samu hakan, amma sbd san zuciyarta ta tafi ta barta.
Abba yaji zuciyarsa tayi nauyi ji yake inama akwai yanda zeyi ya cire kowace damuwa data faru a cikin rayuwar ƴar tasa domin tayi rayuwa me kyau, ta sami farin ciki, ta haɗiyi baƙin ciki kala-kala, yana fatan Allah ya bata wani sabon fata wanda zai sata farin ciki a nan gaba.
"Kiyi haƙiri Hanam, ki ɗauki hakan a mafsayin YADDA ƘADDARA TA SO ".
_godiya ta musanman zuwaga makaranta wannan littafi, ina muku godiya sosai wanda suka shiga group din YADDA KADDARA TA SO NOVEL GROUP, hakika naji dadin ganinku sosai, Allah ya saka da Alkairi_
_kuyi share, and comment pls_
_Na kara gode muku_
🌸-SAI KASKA CE-🌸

YADDA KADDARA TA SOWhere stories live. Discover now