YADDA KADDARA TA SO 21

22 2 0
                                    

⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*Babin yau naki ne Fatima Abdulƙadeer*

*BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA (21)*

UCHENNA POV.
Tsaye yake daga can nesa da masallacin da ake taron ɗaurin auren Hanam, waya yake da mamarsa tana faɗa masa cewar bazata samu damar zuwa ba, sbd ciwon mijinta ya tashi jiya da daddare.
“To mom ba damuwa, kice ina gaida shi, Allah ya bashi lafiya”
“Ameen, ka bashi hakuri please kace masa inshallah zan zo ko bayan bikin ne”
“To”
“Zan kiraka letter”
Daga haka ya sauƙe wayar yana kallon Abba daya taho wajensa da sauri.
“Abba lafiya?”
“Ina fa lafiya Haris, call this number for me”
“Ok”
Ya faɗi yana karb'ar wayar da Abban ke miƙa masa sam, hankalinsa ba akwance yake ba, ya kira Jabeer amma yaƙi ɗagawa, Uchenna ya saka lambar a wayarsa sannan ya aika mata kira.
“Ta shiga ?”
“Eh ta shiga...”
Baima gama rufe bakinsa ba Abba ya warce wayar, saida ta kusa katsewa sannan aka ɗaga.
“Hello jabeer nine....”
Daga can b'an garen Jabeer ya sauke wayar daga kunnesa ya duba screen ɗin, shide lamba ya gani.
“Dan Allah kar ka kashe”
Ya rintse idonsa, dan da shirin kashewar yake.
“Ina kake Jaber ?”
Murya ciki-ciki jabeer ya amsa da
“Ina gida”
“Me yasa zaka min haka Jabeer ?, kasa na tara mutane amma kaƙi zuwa, haba jabeer”
Cike da rashin kunya Jabeer yace.
“Dallah daka tamin malam, ni bance me yasa kamin haka ba sai kai zaka zo ka wani titsiyeni da maganar banza, Da kake so na aure guntuwar yar ka to Allah ya toni asirin ku kaida ita, ashe karuwanci taje tayi a USA shine har ta dawo maka da jika, To Allah yasa matarka mutuniyar arzikice, ta kirani ta faɗa min komai, Dan haka ni bazan auri guntuwar yarka ba, wadda maza suka gama da ita, kada ka ƙara kirana sai anjima”
Dib!!, kiran ya yanke, duka abinda Jabeer ya faɗi a kunnen Uche, saurin kamo hannun Abba ya yi gani yana shirin faɗuwa.
“Abba ka nutsu, ciwonka kada ka bari ya tashi”
A lokacin Baba da kanin Abba suka ƙaraso wajen suma.
“Kai harisu me yake faruwa wai ?”
“Baba yaron nan yaci amanar mu, yace wai bazai iya auren Hanam ba”
Abba ya faɗi cikin wata iriyar murya dake nuna tsantsar tashin hankalin da yake ciki, tunanika da yawa suna ta yawo a cikin kansa, to yanzu me zaije yace da Hanam, kuma wai tsaya yace matata?, wacece ta kirashi ta kitsa masa ƙarya da gaskiya ?.
Mero, wata murya ta faɗi a cikin kansa. Idanuwansa suka kaɗa sukayi ja, wato Mero duk abinda zai zo ya samu Hanam na farin ciki ita bata so.
Yayi ƙwafa a fili, sannan ya juya ya kalli Uche wanda ke riƙe da shi, sannan ya furta abinda ya zama sanadiyar sauyawar Ƙaddarar mutum uku a lokaci guda. Hanam, Arya, da shi kansa Uchennan.
“Haris, dan Allah inaso ka auri ƙanwarka Hanam”.
second ɗaya.... biyu....uku.

HANAM POV.
Zaune take a ɗakinta ita da ƙawayenta biyu na amana tun na primary, Falaq da Iqra, she can't believe wai yau aurenta ake, abun na bata mamaki.
Sanye take da farin lace ɗinkin doguwar riga kuma kamar kullum fuskarta babu kwalliya, yau sai take jinta a kaɗai ci, dan tun safe Rafi'a ta rabata da Arya.
Hayaniyar mutane a waje da taji ne yasa ta fahimci cewa ƴan ɗaurin aure ne suka dawo, sai taji gabanta ya takarkara ya faɗi, yanzu wai an daura mata aure ?, shikenan yanzu ta zama matar jabeer ?.
Ƙofar ɗakin aka turo Rafi'a ta shigo hannunta riƙe da Arya dake sanye cikin farar shadda wadda su kayi anko shida Abba, Hanam ta kallesu su duka.
“A'a masoyi ina ka shiga ne bamu ganka ba?”
Cewar Iqra tana miƙewa ta ƙarasa inda Rafi'an ke tsaye riƙe da Arya.
“E ba, nima ban ganshi ba”
Cewar falaq, a lokacin kuma Rafi'a tace.
“Anti Hanam kije inji Abba, yana babban parlonsa”
Hanam taji gabanta ya tsananta bugu, kamar wani abu ne da ban ya faru da wanda take tsammani.
*
Ganinsu su uku a parlon yasa gabanta ƙara tsananta bugu, Abbane da Baba da kuma ƙanin Abba wato kawu Audu.
“Zo ki zauna a nan”
Taje ta zauna a kusa da Baba dake wannan batu, tun da ta shigo Abba ke binta da kallo tausayinta na ƙara kama masa zuciya, ta wahala sosai a rayuwarta, kuma yana fatan wannan auren da ya mata ya zama silar samun farin cikinta a rayuwa, yasan abinda yayi daidaine.
Dan yanaganin shine ma abinda da yadace ace ya yi tun-tuni, amma da Allah ya ƙaddara cewar hakance zata kasance gashi ta kasance, kuma yana da tabbacin za ta yi farin ciki a nan gaba.
“Hanam”
Ya kira sunanta, a hankali ta ɗago da kanta ta kalleshi tana amsawa, sai kuma ta ƙara sun kuyar da kan nata ƙasa.
“A yau na ɗauri miki aure da wani ba Jabeer ba, sai a yau na tabbatar da Jabeer sam bai dace da ke ba, ya sakani na tara jama'a shi da wakilansa kawai ake ake jira amma yaƙi zuwa, na kirashi a waya sai yake cemin wai shi ba zai auri sauran ƴata ba, ya faɗi maganganu da yawa, daga karshe yace kada na ƙara kiransa....”
Sai kuma ya yi shiru, Hanam dake jin duniyar ta mata shiru tun a maganarsa ta farko ta ɗago ta kalleshi, idan ba Jabeer aka aura mata ba to waye ?!!.
“Hanam, na aura miki wanda na aura miki ne dan na isa da ke, nasan da cewa ke me biyyayace ga duk abinda nake so, nasan baki tab'a bijire min ba, kuma nasan cewa wannan karon ma bazaki bijire ba....”
Ya kuma yin shiru yana ci gaba da kallon reaction ɗinta, har yanzu bata ce komai ba kallonsa kawai take, ita buƙatarta taji waye ya aura mata.
“Hanam, ba kowa na aura miki ba face UCHENNA!”.

YADDA KADDARA TA SOWhere stories live. Discover now