YADDA ƘADDARA TA SO 14

29 5 0
                                    

⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Arewabooks @18saikaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*BABI NA GOMA SHA HUƊU (14)*

*Babin mu na yau kuma naki ne, Badi'a Ahmad Sulaiman*

.........Tunaninsa ya katse a sanda Maryam ta buɗe ƙofar, abu na farko daya fara shiga ƙofofin kunnuwansa shine wannan bugun zuciyar, kuma a tsorace yake bugawa, kenan tsoransa take, tana tsoransa a matsayinsa na haka ina ga idan tasan waye shi, ainahin shi.
Sai kuma ya kalleta, hijabi ne a jikinta har ƙasa, hannunta da fuskarta ne kawai a bayyane, idonta ya kalla, wani abu dayafi komai kyau a fuskarta.
Maryam na haɗa ido dashi ta sunkuyar da kai, dan bata tab'a sanin haka kalar idonsa take blue ba sai yau, cikin tsoro da rawar murya ta sunkuya ƙasa tace
“Ina kwana”
“Lafiya”
Ya amsa mata cikin muryarsa me zurfi, kuma sautin muryar tasa kamar akwai gajiyab a ciki, Maryam ta miƙe kuma har yanzu kanta a ƙasa zuciyarta na tsere a ƙirjinta.
Shi kuma ya kasa kunnensa sai sauraren bugun zuciyarta yake, koda wuƙa za'a ɗora masa a wuya a tambayeshi me yake ji a bugun zuciyar tata bazai iya faɗar komai ba, dan baisan me yasa yake san sauraren sautin ba.
Kawai de yana jin kamar akwai wani abu a cikin sautin bugun zuciyar tata na musanman, kamar yanda fuskarta take very Innocent hakama zuciyar tata ke bugawa, musamman ma idan tana bugawa da sauri.
“Zanje aiki ne, shine nace bari na faɗa miki, akwai kitchen a ƙasa, zaki iya shiga ki girka abinda zaki ci, ko idan na fita na aiko miki ?”
Ya bata zab'i biyu ne dan be san me ya kamata yayi a cikin biyun ba, idan yace sai ya fita ne lokaci zai ƙure, kuma bai sani ba ko bata makara wajen cin abinci, idan kuma yace ta girka wata ƙila bata iya girkin ba, dan haka ya yambayeta.
Kamar Maryam zata ce masa ta rage abincin jiya kuma shi zata ci sai kawai ta fasa tace.
“A'a zan girki”
Muryarta ta fito da irin innocent dinta, a hankali ya gyada mata kai.
“Sai na dawo”
“Allah ya tsare, Allah ya kiyaye hanya”
Maryam ta faɗi bayan ya juya, maganar tasa Tafida ɗan dakatawa da tafiyar da yake, addu'ar ta dakeshi sosai. A hankali yaci gaba da tafiya cikin takunsa na izza da ƙasaita, tausayin yarinyar na ƙara kama zuciyarsa.
Maryam tabi bayansa da kallo, tana kare masa kallon da bata samu damar masa ba jiya, bata san cewa dogo bane sai yanzu data tsaya a gabansa, kuma wani abu data lura dashi shine yana da rukon al'ada, dan daga jiya har yau duka kayan hausawa take ga yana sakawa, amma ita a ganinta sai take ga kamar kayan basu wani karb'e shi ba, da a ce zai saka kayan indiyawa sai yafi karb'arsa, dan gaba ɗaya kamar indawace dashi.
Ɗakinta ta koma ta cire hijabin jikinta dan dama sbd ya kwankwasa kofar ne yasa ta saka, wajen data saka wayarta a chargy ta koma ta cire wayar.
Da ƙyar ta samu ta lalubo lambar Anti Fati, dan wayar bata dannuwa da kyau, alamun taci sensor, gaisawa sukayi sannan ta tambayeta ya su maanmu suke, Anti Fati ta ƙara mata nasiha, sannan sukayi sallama ta nemo lambar Badar za ta kirata amma sai aka sannar da ita bata da isasshen kati.
Tayi tsaki sannan ta aje wayar miƙewa tayi ta ƙara saka hijabin data cire sannan ta fita daga ɗakin, ta tsaya a ƙofar ɗakin tana kallon corridor ɗin dakunan, daga karshen corridorn daga dama kuma balcony ne, wanda yake facin kofar gidan.
A hankali take takawa zuwa wurin, balcony ɗin yanada faɗi sosai, ga wasu flower vase da aka jera daga ƙasa, ga grass carpet shimfiɗe a kasan wurin, ga kuma wani lilo a wajen, sai wasu flower vase din rataye a sama.
Daga jikin bangoma wasu ne jere kala-kala, karfen balcony ɗin an masa ado da neon strip light, hakama wasu daga cikin flower vase ɗin, Maryam har ta hango yanda wajen zeyi kyau da daddare idan aka kumma neon strip light ɗin, daga ɗan sama kuma kejin aku ne kuma akwai akun a ciki.
Maryam taji wani abu na farinciki na ratsa mata zuciya, sai kuma ta kalli sauran gidajen dake tsallaken nasu da ma na kusa da su, ko wani gini iri ɗaya ne hatta da fenti, view ɗin kasan akwai ban sha'awa. Ta koma wajen akun nan, tana kallonta, can tace.
“ Barka”
Akun ma ta maimaita.
“Barka”
Dariyar farin ciki ta sub'uce daga bakin Maryam, gaba ɗaya wajen ya gama burgeta.
Fita tayi daga wurin ta ci gaba da tafiya a corridor ɗin, bata buɗe dakin da taga ya shiga jiya ba, dan bisa ga dukkan alamu nasa ne, sai ta bud'e na kusa dashi, shi ma kamar nata yake, amma kuma babu gado sai katifa kawai, kuma komai na dakin an lillibe da kyalle alamun ba'a amfani dashi, ta jawo ƙofar ta rife.
Amma kuma sai taji tana san taga ya nasa ɗakin yake, dan haka ta koma da baya ta bud'e kofar
“WOW”
Kawai ta iya furtawa da tayi arba da ɗakin, tsarin ɗakin kamar nata yake amma kuma yafi nata girma, a hankali ƙafafunta sukaci gaba da takawa zuwa cikin ɗakin, tana ta santin kyan ɗakin a zuciyarta.
Ta kalli inda yake aje cricket kit bag dinsa, ga Jersey dinsa rataye a saman jakar, a ranta tace ashe ɗan wasan cricket ne,  dubanta yakai kan wani bango a ɗakin wanda yake cike taf da hotuna, kafafunta sukayo kwana zuwa jikin bangon, ta tsaya tana bin hotunan da kallo ɗaya bayan ɗaya, duka hotunansa ne, tun na yarinta har zuwa girmansa.
Idonta ya tsaya akan wani hoto guda ɗaya, kuma wanda yafi kowani hoto girma a cikinsu, wani baƙin fatane ɗan africa sanye cikin suit irin tasu ta lokacin, sai kuma wata ba'indiya fara tas da ita, sanye cikin sari hannun ta riƙe da wani yaro da ba zai wuce 3 yrs ba.
Abu ɗaya ne ya faɗo a tunaninta, tabbas wannan iyayensa ne, kenan babarsa ce ba indiya ?, ga zahiri kinga tunda kamarsu ɗaya da matar, wani sashi na zuciyarta ya amsa mata, Fulani ta faɗa mata cewa iyayensa sun rasu.
Sai kawai tayi musu addu'ar Allah gafarta musu, taci gaba da bin hotunan tana kalla, tun yana ƙarami suke hoto da wata budurwa itama kuma ba'indiyace, kode kanwarsa ce ?, to amma kuma ai bashi da ƙanwa a wannan hoton, wata ƙila yar uwarsace, dan suna kama hatta da kalar idonta irin nasa ne, amma ita nata idon ba light blue bane, nata dark blue ne, kuma duk da kasancewarta mace yafi ta kyau.
Ya samu gata sosai, ta faɗi a zuciyarta, sakamakon hotunansa da take gani na celebrating birthdays dinsa.
Saida ta gama masa tsurku akan hotunan nasa sannan ta bar ɗakin, ta sauƙo ƙasa. Kamar jiya, yauma ta tsaya tana ta kallon tsaruwar parlon, ƙofar farko da idonta ya sauƙa a kai ta fara shiga.
Sai taga store ne na a jiyar kayan amfanin gida, akwai irin su wheelbarrow, watering can, spade (shebur), hose (tiyo din ruwa), vacuum cleaner, pruner (abun yankan ciyawa), spenner, hammer, broom ɗinma wata doguwa ce, bucket, dustpan, squeegee mop(mofar goge glass), mop (mofa), scrubbing brush da dai sauransu.
Wasu abubuwan ma bata sansu ba, kuma komai a killace yake, akan kantoci, daga ƙarshen ɗakin kuma washing machine ne har guda biyu, wata chest drawer ta gani a gefen washing machine ɗin, ta bud'eta sai taga laundry detergent, bleach, pegs ( clips ɗin shanya ), ta mayar da rufe, sannan ta fita daga wurin.
Sai kuma ta shiga ɗayar ƙofar shi kuma bashi da girma dan guga kawai ake a ciki, daga ironing board sai wasu lokoki, ta shiga ta bubbuɗe lokokin, wasu kayane a ciki ba'a goge ba, wasu kuma an goge amma ba'a ɗauke ba, sai wasu iron guda biyu babba da ƙarami.
Ta fito daga ɗakin ta buɗe ɗayar ƙofar dake a tsalleken dakunan, shi kuma data buɗe gym ne kawai, katangu biyu da suka zagaye wajen gaba ɗayansu ɗauke suke da mirror, batama shiga ba taja ƙofar, dan a ganinta babu abinda za tayi a wani gym.
Ƴar wata kwana dake bayan ƙofar gym ɗin tayi, taja ta tsaya baki buɗe tana kallon danning table ɗin dake wurin, danning ɗin ya burgeta fiye da misali.
Ƙofar dake kusa da wajen tayi sbd ko tantama ba tayi ƙofar kitchen ce, abinda take ɗaukin gani kenan a gidan, kusan sumewa Maryam tayi, bayan tayi arba da kitchen ɗin.
A rayuwarta tana san kyakyawan kitchen, wasu lokutan kawai sai ta tafi gidan Anti Fati sbd kitchen ɗin gidan, yau sai gashi idonta na gane mata kitchen ɗin daya ninka na gidan Anti Fati girma da kyau, kuma wai na gidan mutumin da ake kira da mijinta ne, wani abu yazo ya tsaya mata a zuciya na murna, taji kamar tana yawo a gajimari, ita da ganin kitchen irin wannan sai a film, ko a social media.
kalar cabinet din kitchen din ash ne, ga wani kitchen island wanda aka kewaye shi da kujeru guda hudu, biyu daga kowani b'angare, wani abu da ya ɗauki zuciyar Maryam ya jefa a cikin ruwan sanyi shine.
Daga tsakiyar cabinet ɗin sama da na ƙasa wanda yake setin inda gas cooker take glass ne a wurin,a bayan wajen kuma garden din gidan ne, ga wasu flower vase da aka jera akan wajen, ga haske a cikin kitchen ɗin ta ko ina, kuma daga ƙasan cabinet ɗin sama akwai wasu led strip light dake haska kan cabinet ɗin ƙasan.
Maryam ta rasa ina zata saka kanta dan murna, a hankali ƙafafunta da babu takalmi suka shiga taka tiles ɗin kitchen ɗin, babu inda zuciyarta ke raya mata ta fara zuwa sai wurin glass ɗin nan.
Ta kai hannu ta zuge glass din zuwa gefe, daddaɗar iskar da bishiyoyin garden ɗin ke bayarwa ce ta silalo zuwa cikin kitchen ɗin, a hankali ta lumshe idonta, sannan ta buɗe, sai kuma tabi vase ɗin dake laye a wajen, green leafy vegetables ne dangin mint, coriander, rapini da dai sauransu, Maryam ta maida dogon glass ɗin ta rufe.
Sai kuma ta dawo ta shiga bud'e cabinet ɗin, gaba ɗaya dangin kayan aikin girki babu wanda bata gani ba, spoon, fork, knife , pot har set biyu kuma duka non stick ne, juicer, tray, tongs, bottle opener, blender, ladle, pestel and morter, choping board, plastic containers dama wadan da bata taba gani ba.
idonta sai ƙyallin murna ya ke, ga ba ɗaya kayan sauƙaƙawa mutum wajen aikin girki akwai a kitchen ɗin, tun daga toaster, coffee maker, oven har guda biyu, mixer, deep fryer, dish washer, microwave oven, hand blender hatta da dishwasher akwai.
Maryam kamar ta taka rawa dan daɗi, sbd wasu kayan ma ba'a ko buɗe su a ledar su ba, sabbabi dal, hakan ya nuna mata cewar ba sosai yake girki a kitchen ɗin ba, ta buɗe fridge ta ganshi cike da fruits da veggies, ga kayan miya ga kuma drinks amma komai a hargitse yake a ciki ga wasu kayan rober, shi kuma tasa kalar ƙazantar kenan ?.
Wata ƙofa ta gani a kusa da fridge ɗin ta buɗe ƙofar ta shiga taga store ne, kuma akwai kayan abinci amma ba da yawa ba, ta shiga cikin store ɗin ta shiga dudduba kayan ko zata ga abinda zata iya ci.
Aiko tayi kyakyawan gani, wata rice stick wadda tun sanda ta ganta a wani recipe na tiktok ta shiga santin taliyar, yau sai gata ga taliyar, a da kullum bata da zance saina idan tayi aure zata ce mijinta kullum ya dinga siyo mata ita, sosai taliyar ta tafi da ita, sbd a ido idan ka ganta kafin a dafata sai kace zarene ba taliya ba.
Maryam ta kai hannu tana ɗauko taliyar yayinda idonta ke cika da kwallar murna, sai kuma ta tuno gida, nan take murmushin fuskarta ya ɗauke, ko me suka dafa yau ?, ko waye yayi musu girki ?.
Sai kuma ta tuno makarantar ta, yanzu shikenan babu ita ba makaranta ?, Lalle rayuwarta ta sauya sosai a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, ta samu abubuwa da dama kuma ta rasa abubuwa da dama.
A hankali wata ƙwalla ta sulalo mata, ta daure ta share, sannan ta dawo cikin Kitchen ɗin, ta shiga ƙoƙarin dafa taliyar rice stick ɗin.
Saida ta haɗa komai sannan ranta ya raya mata me zai hana ta duba garden ɗin ma, sai ta rage wutar gas ɗin.
Sannan ta buɗe ɗayar ƙofar kitchen ɗin wadda take da tabbacin garden ɗin zata kaita. Ƙam, ta ƙame tana kallon yanda wajen ya bala'in tsaruwa, shuke shuke ne fal wajen, ga wani water falls wanda aka kewaye shi da stones.
Maryam taji kamar ta nitse a gun dan daɗi, wajen ya haɗu, ya haɗu karshen haɗuwa, wata rumfa dake tsakiyar wurin ta shiga, wadda ke ɗauke da kujeru da kuma table a tsakiya, kamar de balcony ɗin saman nan, shima nan wajen akwai wannaan neon strip light ɗin, an ƙawata wurin dashi, shima dai nan ɗin kamar can ta hasaso yanda zeyi kyau da addare, aiko zata zo ta duba shi da daddaren.
Wani stairs ta gani wanda zai kaita can saman rufin gidan, a hankali ta juya zuwa wajen, tana takawa har ta kai saman gidan, nanma haɗuwarsa ba'a magana, kuma saman ma akwai jerin kujerun zama ga grass carpet ga iska me daɗi dake kaɗawa a wurin, ta shiga duba gidajen dake kusa da nasu dama wanda ke nesa da nasu, ita kam yau ta rasa abunyi dan murna.
Tunawa da tayi ta bar girki yasa ta koma ƙasan ta shiga kitchen ɗin bayan ta leka wani lungu da tagan shi a bayan kitchen ɗin,  taga b'ulla gaban gidan ne.
Taliyar tata ta sauƙe ta haɗata da kayan haɗin da ta mata sannan ta komo kitchen din ta zauna ta saka taliyar a gaba tana kallo, sai kuma tayi bisimilla sannan ta kai bakinta, wasu lokutan burika na cika a gaske ba mafarki ba, yau gashi tana cin taliyar da take burin ci. Allah abun godiya.
TAFIDA POV.
Har ya kai ST NICHOLAS HOSPITAL, bai dena tunanin addu'ar da tayi masa ba, anya kuwa idan yaci gaba da zama da ita bai cuceta ba ?, anya kuwa ba zai zama me san kai ba ?, da haka ya fito daga motarsa har ya shiga floor na farko kuma kamar kullum yana gaisawa da mutane, a ƙofar elevator ya haɗu da Khabir.
“Ango, Ango”
Itace kalmar da khabir ɗin ya fara faɗi suna gaisawa, Tafida yayi murmushi, amma baice komai ba, suka shiga elevator ɗin zuwa hawa na 5 dan a nan office ɗinsu su dukan yake.
Khabir sai tambayarsa yake akan auren nasa amma Tafida yaƙi cewa komai sai da suka shiga har office ɗin Tafidan sannan ya bashi amsa.
“Khabir, yanzu bani da abin cewa akan auren nan, ka bari akwai wata waya da nake jira, daga baya sai muyi magana”
Kamar Khabir ɗin zai ce wani abu, sai kuma yayi shiru.
“Allah kyauta, bari naje”
Tafida ya gyaɗa masa kai, wayarsa ce ta fara ringing tun kafin ya zauna, zaman yayi kamar yanda yayi niyya, ya cire hular dake kansa sannan ya daga kiran, suka gaisa da Muktar sannan dalilin kiran ya taso.
“Me ka samo ?”
Muryar tasa ta fito cikin wannan ajin nasa da kasaita, yanayi yana tura sumarsa baya, muryar Muktar ta fito daga cikin wayar yayinda yake faɗin.
“Komai ma na samo, sunanta Maryam Tijjani Muhammad, haifaffiyar hadejia unguwar garko, tanada yan uwa huɗu, babbar yayarta itace Fati matar Habib, nasan ka sanshi ai gidansa ma kusa da gidan ka ne”
Idanun Tafida a lumshe ya gyada kai, kuma shima Muktar ɗin kamar da yasan ya gyaɗa masa kan sai yaci gaba.
“Tanada ƙanne uku, Hassan da Hussain sai autansu Muhsin...... Wato Tafida abun mamakin shine ƙannen nata ƴan biyu a secondary school suke, kuma sune suke ciyar da gidan nasu, and a shekaru bazasu wuce 18 ba”
Da sauri Tafida ya buɗe idonsa
“Me ?, but ina babansu ?, ko ya rasu ?”
Ya jerowa Muktar tambayoyin, cikin wata iriyar murya da bazaka iya gano halin da yake ciki ba.
“Wallahi yana nan da ransa, da drivern tilera ne, ya riƙi kuɗi a da, amma kuma yana bin mata kasan shi kuma ƙarfe ba'a haɗashi da kazanta, sai me motar ma ya kwace kayarsa, daga nan kuma sai ya talauce, sai yake ganin kamar wai matarsa mahaifiyar su kenan itace me farar ƙafa, sai ya fara mata cin mutinci baya kula da ita da yaranta, wani yayanta ne wai Usman, Shine yake kula da ita har yaran suka taso sannan suka fara aiki a wani gareji, kuma har yanzu sune suke kula da gidan, and baban kuma har yanzu bai dena halin banzansa ba, ni wani labari da naji ma ance kuɗin auren Maryam ɗin da aka bashi zaije yayi aure dashi, abun de abun tausayi”
“umhm ina jinka”
Tafida ya faɗi hannunsa akan bakinsa
“Shi wanna kawun nasu yayan maman tasu shine yake ɗaukar nauyin karatun Maryam ɗin, dan poly take ma, ta gama level one zata fara level two, kuma kasan wani abu ?, wallahi yarinyar akwai kamun kai, ga tarbiyya bata da matsala ko kaɗan, ko saurayi ba ta da shi sai wani wai shi sanata, kuma shima ba kulashi take ba, dan yanda naji labari ma ance wai daga karshe ce masa tayi ita yanzu bata da ra'ayin aure, gaskiya kayi dace”
Ya sauke hannunsa daga kan bakinsa.
“Gaskiya kam nayi dace, nayi dace da su Fulani suka aura min ita, dan nasan idan ba ita bace ba lalle na karb'eta ba, saide kuma ita batayi dacen ba, su Fulani sun hargitsa rayuwarta da suka aura mata ni, amma babu komai, zan nema mata gun karatu a nan polytechnic din alaro, sai taci gaba kawai kaje poly din ka karbo min takardunta ka aiko min pls”
“Tafida yanzu baza kayi haƙuri da auren nan ba?”
“Yaya zanyi Muktar ?, nesanta kaina da zanyi da ita shine babban gatan da zan mata, idan har naci gaba da kusantar ta zan iya cutar da ita, and if that happens bazan tab'a yafewa kaina ba, bana san na zama silar rasa innocent soul kamarta”
Yana iya jiyo ajiyar zuciyar da Muktar yayi.
“Kuma hakane, Allah ya mana me kyau kawai”
“Ina asibiti idan ka karb'o takardun just let me know”
“Inshallah”
Daga haka kuma wayar ta ƙare, ya ƙira drivern sa ya aike shi siyyaya, sannan ya fara aikin da yake jiransa.

YADDA KADDARA TA SOHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin