YADDA KADDARA TA SO 23

25 3 1
                                    

⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Tiktok @SAI_KASKA
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*Gareki na sadaukar da wannan babin Maryam Sani Salis*

*BABI NA TALATIN (30)*

*Murtala Muhammad International airport, Lagos*
Heleen ce ke tafe ita da yaranta, sanye take cikin wata jeans skirt me tsaga a gaba, skirt ɗin bata sauƙa mata har ƙasa ba, sai sweat shirt baƙa, wannan kalabar attachment ɗin ta zubo har gadon bayanta, rabin fuskarta rufe da sun glasses.
Sai taunar chewing gum take, tana taku akan hills ɗin dake ƙafarta, hannunta babu komai sai wayarta jakukunanta yaranta ne riƙe da su.
Koda ta sako ƙafarta wajen ginin airport ɗin, sai ta shaƙi iska tana murmushi.
“I miss lagos, and i miss you Dr. Eshaan”
Cike da nishaɗi take furta hakan, hoton kyakyawar fuskarsa na giftawa ta cikin idonta, a ranta take kudurta yau zata daure ta hana kanta zuwa wajensa, dan ta samu ta huta, zuwa gobe za ta yi wa St. Nicholas Hospital tsinkaye. Domin ta samu damar arba da kyakyawar fuskarsa da ta yi kewa tsawon lokaci.
*Cogrove Estate,st 3, house NO. 334*
*Da misalin 10:00am*
“Ina kuma zuwa haka ?”
Muryar Uchenna ta faɗi daga bakin ƙofar ɗakinsa, yayinda ya leƙo yana kallon Hanam ita da Arya, kwaliyar da a kayiwa Arya ɗince ta sa ya yi tambayar, sanye yake cikin wata baƙar suit, wadda ta zauna daidai jiknsa, gashinsa baki siɗik me taushi yana ta sheƙi, ga wani farin canvas da ya gani sanye a ƙafarsa.
Ita kuma Hanam ɗin tana sanye da farin cargo pants, da wata bakar sweat shirt, ta yafa mayafi a kanta.
Hanam ta kalleshi da kyau, a yau ne za ta je ta bin ciko waye shi, tana so ta tabbatar da abinda Abba ya faɗa mata, kuma za ta yi hakan, in Allah ya yarda za ta yi hakan, riƙon Arya ta gyara sannan tace.
“Babu inda zamu je, yau ne yake cika shekara ɗaya, shi yasa kagan shi a haka”
Uche ya ƙarasa fitowa daga cikin ɗakinsa ido waje yana duban Hanam, yau yake cika shekara ɗaya ?, amma shi bai sani ba?.
Wannan ranar tafi ko wace rana farin ciki a wajen Hanam, ranar da ta kawo Arya duniya, ranar da ta ɗora ido a kansa zuciyarta ta bashi wani shimfiɗeɗen fili, filin da bayan Abba babu me irinsa.
“Yanzu shine zeyi birthday baki faɗa min ba?”
“Ba wani celebrating zamu yi ba, shi yasa”
“No, that's impossible, taya za'ayi yarona ya cika shekara ɗaya babu wani shagali, na lie oo”
ya faɗi yana karb'ar Arya ɗin daga hannunta, yaronsa ?, ba wanna ne karo na farko da ya kirashi da sunan ba, saide a duk sanda zai kirashi da sunan wani abu ne ke motsawa a ƙasan ruhinta, yana sawa taji kamar akwai wani wanda yake sansu ita da Arya bayan Abba.
“Kawai ke ki tafi aikin ki, mu zamu tafi magic land, a can zamuyi celebrating ɗin, mun yafe miki”
Tayi murmushi tana kallonsa.
“Ok akwai baby feed ɗinsa, sai ku tafi da shi”
“No bama bukatar wani baby food, yau ai daɗi zamu sha, musha ice cream da massasa(sweet )”
Mamaki ya kusan daskarar Hanam, a ina ya iya larabci wai ?, kuma wai har yasan massasa ?.
Kai kawai ta gyaɗa musu sannan ta nemi hanyar fita, tana so komai ya zo karshe a yau ɗin nan.
*
“Ina jin ki”
Cewar Hanam yayinda take kallon matar dake zaune a gabanta, Saida taje wurin aiki lafin kai tsaye ta wuto unguwar da taga  jikin wannan takardar, sannan ta kira lambar da ke jikin takardar, ta yi wa matar bayanin da Abba yace mata ta yi.
Matar da kanta fa fito ta yi mata iso zuwa gidan, kuma Hanam ɗin ta mata bayanin abinda ke tafe da ita. Matar ta ƙara nisawa sannan tace.
“Babu komai, kawai de ina so na sani ne, kece ƴar Alhaji Muhammad”
Hanam ta gyaɗa mata kai tana ci gaba da kallonta.
“Kenan kece matar Haris ɗin ?”
Harees ?, itama fa Harees ɗin tace?, wai meke faruwa ne ?, wani ya temaka ya fahimtar da ita, a hankali ta gyaɗa mata kai still tana kallonta.
“Nasan mahaifin ki ya faɗa miki cewar babu wanda zai baki labarin Uche sama da ni, kuma bai miki ƙarya ba, dan bayan mahaifiyar Uche, nice mutum ta biyu da ta san shi ciki da bai, kinga nan ?”
Ta tambaya tana nunawa Hanam ɗin wani bango. Hanam ta gyaɗa mata kai.
“Nan shine katangar gidansu”
“Mahaifiyar Uchenna ta kasance musulma, sunanta Raahidat, ƴar a salin jihar Enugu ce, mahaifinsa kuma cristian ne sunasa Jhonson Aja, shima ya kasance haifaffen garin enugu, sede shi ba shi da iyaye, ya taso ne a hannun wani kawunsa, yayinda yake sana'ar ɗinki anan abuja.
A wani zuwa gida ziyara da ya yi ya haɗu da Rashidat, har suka fara soyyaya, daga baya se ya nuna mata cewar shifa aure yake so suyi, ita kuma Rashidat ta nuna masa cewar aure tsakaninta da shi ba ze iyu ba sbd shi cristian ne, yace mata ze musulunta.
Kuma ya musulunta ɗin, har kawunsa yace ba shi ba shi, kada ya ƙara nuna cewa shi kawunsa ne, Aja be damuba tunda yanaga ze samu Raahidat.
Bayan sunyi aure suka tare a nan garin abuja, awannan gidan dake kusa da nawa, farkon auren Aja ya nunawa Rashidat soyyaya, kafin daga baya ta gane cewa ashe ya koma zuwa church, seda su kayi ba daɗi kafin ya bata haƙuri akan ya dena,zeci gaba da yin addininta.
A haka har tasamu cikin Uchenna, ta haifeshi ana zaman lafiya, har aka raɗa masa Haris, amma Aja yace ana kiransa  Uchenne.
Sosai Aja kenunawa Uchenna so, komai na duniya Uchenna ze ce, a haka har ya kai shekaru bakwai, ya fara fita da shi kasuwa inda yake sana'ar ɗinki.
A sannan ne kuma Rashidat ta ƙara samun ciki, bayan wata tara ta haifo yara ƴan biyu, Zakiyya da Jude, haka a halin nasj ya ck gaba da tafiya har zuwa lokacin da su Zakiyya suka cika shekara biyar.
A sannan Rashidat ta gano cewa Aja yaudararta yake, be dena zuwa church ba, a sannan ne a kayi babu daɗi, ya fito mata a mutum kan cewar shi ba ze dena addininsa ba, ita kuma tace se ya saketa, shi kuma yace bazai saketa ba.
A sannan matsalar gida ta soma, Rashidat ta fita a harkokin Aja, ta ja yaranta a jiki tana ƙara nusar da su mihimmancin addinin musulunci, wannan abu baƙaramin bawa Aja haushi ya yi ba.
Dan haka ya ɗauki karar tsana ya ɗorawa Rashidat da yaranta, musamma ma Uche da Zakiyya, dan akwai soyyaya tsakaninsa da Jude, ko me zeyi bayamasa.
Aja ya dena basu abinci, ga duka ga zagi, zuwa lokacin Uche ya fara mallakar hankalin kansa, dan haka daga yaje kasuwa ya yi ɗinki ya samu kuɗi, se yakawowa Rasidat dan ga siya musu abinci.
Da Aja ya gano hakan se ya koreshi daga shagonsa, Uche ya koma shagon wani abokin Aja, amma Aja yaje yasa aka kore shi, duk shagon da ya koma dan ya rakab'a ya yi dinki se Aja ya sa a kore shi.
Ganin haka yasa Rashidat ta seda kadarar ta ta saiwa Uche keken ɗinki, ya fara ɗinkinsa a gida.
Kasan cewar Uche yaro me hazaƙa da baiwar ɗinki segaba ɗaya costomers ɗin shagon Aja suka tattara suka dawo kawowa Uche ɗin.
A lokacin baya zuwa makaranta, dan tun bayan faruwar matsalar ya dena zuwa makaranta, amma shi yake ɗaukar nauyin karantun ƙannensa duka ya ɗauki nauyin gidan da komai, kuma aƴan ƙalilan ɗin shekarunsa.
Matsala tsaninsu da Aja kuma kullum ƙaruwa take, duk daren duniya basa bacci, haka ze saka Uche a gaba yana tsine masa, tsiniwa kala-kala da alkaba'ai, wani lokacin idan haushin be isheshi ba se ya kama Rashidat ya daka.
A sanda Rashidat taga Uche se ƙara girma yake amma baya zuwa makaranta, se ta nemi shawarata, ni kuma nace mata ta saka shi ya koma makaranta, kuma hakan a kayi, ya koma makaranta ya ci gaba da karatu.
Sede matsaltsalun dake faruwa a gida basa saka shi ya yi focussing a kan karatun, sau uku yana maimaita aji, kafin ya samu ya wuce, amma duk da haka abokan karatunsa sun masa nisa a lokacin.
Wata rana da bana matawa Ina zaune a gid naji ihu da kururuwar Rashidat, na fita domin kai mata ɗauki, dan nasan Aja ne ke dukanta, a sanda na shiga gidan na tadda ta yashe a ƙasa Aja na dukanta, Jude da Zakiyya kuma tsaye gefe suna ta kuka.
Na shiga bawa Aja haƙuri amma ko saurare na ma be yi ba, a haka har Uche ya dawo daga school, shi kuma a ranar yaji cewa ba ze iya jurewa ba, dan haka ya ɗauki madoki, ina riƙe shi amma seda ya fisge ya daki Aja da abun a kai.
Aja ya bar kan Rashidat ya dawo kansa, yana dukansa yana tsine masa, Rashidat ma taga bazata iya jirewa ba, dan haka ta ɗauki madokin da Uchenna ya cillar ta daki Aja da shi.
Aja ma yaji ba ze iya jirewa ba a take a wurin ya saki Rashidat. Kar ko so kiga yanda tayi murna ranar, dan ko kwana a gidan ba ta yi ba, a nan gida na ta kwana.
Washe gari da safe ta ɗauki Zakiyya ta yi enugu da ita.
Kuma bayan ta gama idda miji ya fito mata ta yi aurenta. Rayuwar Uche a gidansu ta ci gaba da ta fiya cikin kunci da damuwa, Aja ya ƙwace keken da yake ɗinki da shi, baya ba shi abinci se anan gidan yake zuwa na bashi, gashi shi ba abokai gare shi ba.
Tsangwama babu kalar wanda Aja baya masa, ke hatta da dabbobin da yakw kiwo  ɗakin Uche yake ɗaure su, gwarama Jude dan shi baya masa komai, dan yana san yaron sosai, duk da shima musuluci yake.
Rana ɗaya Aja ya bushi iska ya ya kori Uche, babu yanda ban bawa bawan Allahn na haƙuri ba amma yace fir be san zancen ba, hatta da mijina se da ya bashi baki amma yace ba zs haƙura ba. Sai kuma a kazo ana bani labari kan cewa wai Uchenna ya hau kan titi mota ta kaɗe shi.
Wannan shine labarin uche, a washe garin ranar da uche ya hau titin nan mahaifinki yazo har gidan nan ya yi min tambayoyi akan uche da mahaifiyar sa, bayan nan kuma Rashidat take sanarmin da cewa ya samu aiki, yana rayuwarsa cikin kwanciyar hankali”
Ta ƙarashe tana kallon Hanam, wadda idanunta sukayi ja, tana so ta yi kuka amma ta nemeshi ta rasa, Bata san cewa akwai wani wanda ke cikin baƙin ci ba bayan ta.
Zuciyarta ta cika fal da tausayin Uche, lokacin suna makaranta yana cikin wannan halin amma sam baya hana shi dariya, murmushi da raha, amma ita fa?, ita abu ɗaya ta rasa a lokacin, kulawar uwa, amma take ware kanta da kowa, bata shiga cikin mutane, duk dan wannan ciwon dake cikin zuciyar ta.
🌸-SAI KASKA CE✍️-🌸.

YADDA KADDARA TA SOWo Geschichten leben. Entdecke jetzt