YADDA KADDARA TA SO 8

22 4 0
                                    

⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
©By Sai Kaska
My wattpad page @Sai_Kaska
*Proud of my first novel*
*TAURARI WRITTER'S ASSOCIATION*
*BABI NA TAKWAS (8)*
Maryam tana fita daga wajen ta samu wani wari can nesa da mutane, kusa da inda ake ajebmotoci, ta zauna a kan wani dakali, tana ta mitar ƙaran kiɗan da yayi yawa a ciki, Imran ta zaunar gefe tareda kunna masa cartoon a waya, sai kuma ta ɗago tanata bin motocin dake parker kusa da inda take da kallo, wato su masu kuɗin nan basu da wata matsala a rayuwa, ta faɗi hakan a ranta.
Tafida ya fito daga cikin wajen taron, sbd ya gaji da mitar da ake masa, ga jikinsa dake ɗaukar zafi, kuma kansa na masa ciwo, alamun baƙin ruhinsa na kusa, yazo ya tsaya kusa da motarsa yana ƙoƙarin shiga ya tsinkayi wata murya a bayansa.
“Barka dai”
Sai kawai ya fasa buɗe motar ya juyo yana kallon ma abociyar murya, wata budurwa ce, matse cikin dikin staright gown, kai da ganin farinta kasan na mai ne, ga wata b'ular hanci tayi, mayafinta riƙe a hannu, baice mata komai ba sai tsaiwarsa da ya gyara yana binta da kallo, kuma ko bata faɗa ba yasan me zaisa tazo ta masa magana.
“Idan bazaka damuba dan Allah lambarka nake so, ina sanka da soyyaya”
Ba itace ta farkon masa irin wannan abunba, mata da yawa sun masa irin haka, sbd yasani a karan kansa ba sai an faɗa ba shi kyakyawa ne, amma kuma bayan wannan kyakyawar fuskar akwai wani duhu, duhun da babu wata ƴa mace da zata iya juyashi zuwa haske, wannan fuskar tasa kawai suka sani, basu san ainahin shi ɗin ba.
Eshaan Auwal Tafida bai san cewa akwai mace ɗaya da zata sauya tarin duhun dake cikin rayuwarsa ba, zuwa haske.
Kafin ya samu damar bata amsa, kunnensa ya jiyo masa wata magana a bayan wasu motoci, da farko tsaki akayi kafin yaji ance.
“Aikin banza, wallahi wasu matan basu da kamun kai.....”
Ko ba'a faɗa masa ba yasan cewa abinda yake faruwa tsakaninsu taji, shi yasa take faɗin hakan, dan haka ya mosta kunnensa na dama, wanda yake kusa da inda maganar take fitowa, tayanda yana iya jiyo bugin zuciyar me maganar, ga kuma wani ƴar ƙara kamar ta cartoon, muryarce taci gaba da cewa.
“In banda rashin kamun kai ma me zaisa kazo kana wani cewa namiji kana san sa da soyyaya?”
Aka kuma jan wani tsakin, a hankali take maganar, dan idan ba me ƙarfin ji irin nasa ba babu me iya jiyowa maganar, kuma bayan ta gama maganar sai ya meda hankali wurin sauraron bugun zuciyarta, a hankali take bugawa, sai yaji sautin yana masa daɗi, kamar wakar da yake yawan saurare.
Yayi nisa wajen sauraren bugun zuciyar tata, har baya iya jin abinda budurwa dake gabansa ke faɗi, gani tayi kamar yayi banza da ita, dan haka tayi tsaki ta bar wurin, tana ta mita a ranta na cewar gaskiyane abinda ake faɗi akan Tafida kan bashi da kirki, shi kuma ganin ta bashi damar shaƙar iska yasa ya shiga cikin motarsa yana ta sauraren wannan bugun zuciyar da baisan mamallakiyarsa ba.
*HAKUƊAU GROUP OF INDUSTIRIES, ABUJA*
*Da misalin karfe 10:00 am*
“Uallabai!, yallabai!, yallabai!!”
A firgice Alhaji Muhammad Hakuɗau ya ɗago yana kallon PA ɗinsa, wanda ke ta ƙwala masa ƙira, sai kuma ya kawar da kansa gefe, PA ya samu kujera ya zauna yana kallon ogan nasa.
“Abba me yake damunka ?”
Ya tambaya a matsayinsa na ɗa a wajensa ba wai shugaba da na ƙasan sa ba, Alhaji Muhammad Hakuɗau yayi ajiyar zuciya yana jingina da kujerar da yake zauna a kai.
“Abba ka manta that we are friends, we do'nt use to hide komai wa junan mu”
Maganar taso ta saka Abban murmushi, sai kawai ya gyara zamansa yana kallon PA ɗin nasa.
“Haris abinda ke damuna da yawa, ba duk kai zai iya ɗauka ba”
“Try me”
Abba yayi murmushi
“Matsalar ƴata ce Hanam”
Haris yayi murmushi shima, dama yasan zance gizo baya wuce na ƙoƙi, shi bai taba ganin ƴar me gidan nasa ba, amma a koda yaushe abban bashida abun faɗi ko abun magana akai sai Hanam, hakan yasa shi san ganinta koda sau ɗaya ne.
“Abba a matsayinka na mahaifin ta, addu'a ya kamata ace kana mata, duk da bansan abinda ya faru da ita ba, kuma ka kasance a kusa da ita domin ƙwarara mata gwuwa, ba kazo ka zauna kana tunani ba”.
“Haris Allah baya barin wani dan wani yaji daɗi”
“Ban gane ba”
“Ina nufin akwai mutuwa, akwai jinya dole wata rana zan zo na rabu da ita, hakan yasa nake san nayi mata aure kowa ma ya huta, amma kuma sam taƙi yarda da auren”.
“A'a abba bai kamata kace haka ba, kamar yanda na faɗa maka kayi mata addu'a just pray for her”
Ya ƙarashe yana murmushi, shima Abban murmushin yayi, Allah ya sani cewa yana matuƙar san Haris, da ace Hanam zata amince da ya saka ya aureta.
Abinda bai sani ba shine, wasu ƙaddarorin suna faruwa kamar yanda muka so.
“To meke faruwa ?”
Sai kuma ya dawo serious, ya miƙa masa file ɗin daya shigo da shi.
“file ne daga office ɗin manager”
Alhaji Muhammad Hakuɗau ya kar6a, ya buɗe file ɗin yana gyaɗa kai.
“Zaka iya tafiya”
“Ok sir”
Ya faɗi yana ƙoƙarin fita, a bakin ƙofa yaci karo da Kamal, babban ɗa a wajen shugaban nasu, wani banzan kallo Kamal ɗin ya watsa masa, dan Allah ya sani cewar ya tsani UCHENNA, dan a kullum mahaifinsu yana fifitashi akansa. Uchenna kam ko kallon Kamal ɗin beyi ba, ya rab'ashi ya wuce.
Ko ina ya wuce sai an kirashi, dan babu wanda bai san shi a kamfanin ba, dan Uchenna akwai raha, barkwanci da kuma haba-haba da mutane.
Office ɗinsa ya shiga ya zauna, tareda ɗora ɗaya akan ɗaya, ya janyo wayarsa ya kira ƙaninsa a waya, suka shiga waya, kuma bai kashe ba saida suka jima suna wayar.
Sai wajejen ƙarfe tara na dare ya tashi daga aiki, ya fito daga cikin ginin kamfanin  nasu ya isa parking lot ɗin kamfanin, ya buɗe motarsa ƙirar Honda Accord, ya shiga ya tayar sannan ya wuce gidansa dake Cosgrove Estate Wuse.
Yana shiga cikin kyakywan gidan nasa wuta ya fara kunnawa, sannan ya ya haura sama ya shiga ɗakinsa yayi wanka sannan yayi sallahr isha'i da bai samu yayi ba, ya sauƙo ƙasa ya Shiga kitchen domin ya samawa kansa abinda zaici.
Duk da kyau da tsaftar gidan shi kaɗai yake rayuwa a ciki, babu kowa nasa tare da shi, shi ɗaya yake rayuwarsa.
*Hadejia Emirates*
Mai martaba Abdullahi Abubakar Masu ya tsaya tsirawa matarsa ido, wadda ta gama shaida masa da ta samo yarinyar da ake buƙatar Tafida ya aureta, bawai be yarda da ita bane, saide yana san ya san taya akayi ta samo yarinyar. Suna zaune ne a babban falonsa wanda yake cikin turakarsa, kuma babu me ikon shigowa wajen idan bashi ba ko matansa, sai kuma amintattunsa da suke zuwa su gyara wurin.
“Fulani, taya kika samo yarinyar?” Maganar tasa ta fito cikin ƙasaita kuma a hankali.
“ Bayan abinda ya faru jiya..... Na saka an kiramin Ɗan Masani, kuma ya ƙara faɗamin alamomin yarinyar kamar yanda ya shaida mana a wancan lokacin, kuma na ƙira jakadiya babba mun ƙara tattauna maganar da ita...... Kuma bayan ta dawo daga gidan kamu ne tazo take shaida min da taga yarinyar kuma tayimin bincike akan yarinyar..... Sannan babu alama ɗaya da yarinyar ta rage wadda ake nema”.
Me mai martaba ya sauƙe wani gwauron numfashi
“Na roƙeka ranka ya daɗe....dan Allah ka aura masa yarinyar nan, na gaji da ganin ɗana cikin wannan halin, ina so naga ɗana nima ya warke, na ganshi cikin farin ciki, naga ya tara iyali....”
Sai kuma ta kasa ƙarasawa, sbd kukan daya ci ƙarfinta, me martaba ya rungumeta a jikinsa cikin sigar lallashi
“Amma kinyi bin cike sosai akan yafinyar ?, dan bana so muje mu kawo wadda bata dace ba cikin ahalin mu, garin gyaran gira a rasa ido”.
Fulani taja hanci
“Eh na ƙara sawa an min bincike akanta, yarinyar tanada tarbiyya sosai, kuma daga gareta babu wani aibi, mahaifin ta ne ba mutumin kirki ba”
Me martaba ya gyara riƙon da ya mata a cikin jikinsa sannan ya furta abinda ya zama sannadiyar sauyawar ƙaddarorin Tafida da wannan yarinyar da suke magana akai.
“Yarinyar ce zata zauna da ɗanmu ba mahaifin ta ba, dan haka na ɗauka miki alƙawarin a gobe goben nan za'a ɗaura auren Tafida da wannan yarinya, kamar yanda za'a ɗaura auren Amina da Nasir, wannan alƙawari na miki”.
**
A daidai wannan lokaci, a wani ban garen na masarautar Tafida ne yake tafiya cikin nitsuwa izza da ƙasaita, wayoyinsa ne guda biyu riƙe a hannunsa na dama, hannunsa na hagu kuma key ɗin motarsa ne yana tafe yana ɗan kaɗa key ɗin.
Bayace ga dalili ba, amma wannan bugun zuciyar daya saurare ya kawar da abubuwa da yawa a cikin kansa, ya mantar dashi sign ɗin zuwan baƙin ruhinsa, ya mantar dashi komai, sautin ne kawai ke bashi nishaɗi, kamar kaɗawar igiyar teku, yayinda yake tsaye a gab'ar tekun, iskar da tekun ke busowa me ciki da daɗi da ni'ima tana busawa akan fatarsa.
Haka yake jin bugun zuciyar tata, kuma kamar wata waƙa me daɗi daga bakin babban mawaƙinsa, yaso ace ya dawwama yana sauraron bugun zuciyar nan, dan bayan daya shiga motarsa bai fito ba, kuma baiga yarinyar ba.
Kawai de ya zauna yana jin bugun zuciyar tata ne, kuma jifa-jifa yake ji tanayiwa wani ƙaramin yaro magana, alamun ba ita kaɗai bace a wajen, kusan minti goma sha, sannan sai wata murya ta kira sunanta 'MARYAM' a lokacin ne kuma ta tashi ta bar wurin.
Kuma bai dena sauraron bugun zuciyar tata ba har suka fita daga wajen. Sunanta da kuma muryarta dama bugun zuciyar tata baki ɗaya sunyi gaba da zuciyarsa, har cikin ransa yake fatan sake ganinta......
🌸-SAI KASKA CE-🌸.

YADDA KADDARA TA SOWhere stories live. Discover now