TADDA ƘADDARA TA SO 19

40 4 0
                                    

⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*Sadaukarwa zuwa ga Firdaus*

*BABI NA GOMA SHA TARA (19)*

*Titin ƙauyen hakuɗau*
*Da misalin 05:30pm*
Motoci ne guda biyar suka gangaro daga titin auyo suka hau kan jan b'irjin da zai kai ka har zuwa cikin ƙauyen hakuɗau, tun daga kan hanya yara ke binsu har sukayi parking a ƙofar wani gida me ginin bulo irin ginin zamani.
Gidan kamar ba'a ƙauye ba, hatta da fentin sa sabo ne, ƙofar gidan ma gate ne.
Yara da manya duka a ka firfito ana kallonsu, duk da ba wannan bane zuwansu na farko, suna zuwa lokaci-lokaci, saide kowa yasan cewa idande Alhaji Muhammadu ne yazo to kakarsu ta yanke saƙa, dan zai raba musu kuɗi, koma kayan abinci, dan shi kam ko bai zo ba yana aikowa.
Da gaba ɗaya yaransa ya taho, wajen su goma sha huɗu, mata da maza, matan sane kawai ba'a zo dasu ba, sai yaransa uku mata dake sa aure.
Uche ne ya fito daga motar Abba ta mazaunin driver, da alamuma shine yayi tuƙin, sai miƙa yake, duk da sun sha zuwa tare da Abban.
Hanam ce ta fito daga tata motar, dan ita daga ita sai Arya da Rafi'a suka taho a motar ta, sanye take da atamfa, ɗinkin straight gown me tsaga daga baya, kuma kamar kullum babu kalliya a fuskarta, ta ɗaura ɗankwalin atamfar akanta, sai mayafin data yafa a kafaɗarta, front seat ta zagayo ta buɗe ta ciro Aryaan daga car seat, lokacin da Rafi'an ma ta fito daga bayan motar.
“Yaya kawo shi, sai ki ɗauki jakar taki”
Miƙa mata shi ta yi tana ɗan murmushi, dan tun ba yau ba ita kaɗaice suke shiri a gidan, dan ma tana zuwa makarantar bodin a wancan lokacin yanzu kuma ta gama shi yasa zamanta ya dawo gida gaba ɗaya.
Booth ta buɗe ta ɗaiki jakarta data Aryaan, sannan ta sauƙo da su zata fara turawa.
“Kawo na ɗauka miki”
Da sauri ta ɗago ta kalleshi, dama da shi aka taho ?
“Dama ka zo ne ?”
Uche yayi murmushi yana karb'ar jakukunan hannunta.
“Eh mana, nine ma nayi deriving motar Abba”
Abun ya bata mamaki, bata san ya biyo su ba. Hayaniyar da yaran gidan kakanin nasu keyi ce ta ɗauki hankalinsu.
“Muje ko”
Suka fara tafiya yana tura mata jakar bayan ya ɗauki ɗayar, suka zo wucewa ta gaban Kamal, Hanam na kallonsa yana hararar su, sai kuma ta lura da hararar ba tata bace, ta uche ce.
Sai tunaninta ya dawo mata da sanda taji shida uwarsa suna magana akan wani Uche, wai Abba yana sansa fiye da kamal ɗin, komai sai Abba yace shi.
Ashe shine Uchen?, tayi murmushi kawai. A ƙofar gate ɗin ta karb'i kayan, ta masa godiya ta ƙarasa shiga ciki, gaba ɗaya mutanen gidan sun fito sai hayaniya ake ana murnar ganin mutan abuja, ta ƙaƙalo murmushi, tana gaida tsoffafin gidan, kada ran kada han suke amsa mata, ta sana da hakan dan haka bata damu ba.
“Ke kar ki zo min da wannna shegen kusa da ni!”
Hanam ta tsaya cak, ta karkata kallonta zuwa kan Inna Ai, kishiyar kakarsu, wadda a koda yaushe cikin hantararta take tun a baya ballan tana yanzu, ta kalli Rafi'a wadda take hawaye, dan a rayuwarta bata son taji Arya yana kuka, itama sai ta fara kuka kamar wata ƙaramar yarin.
Hanam ta haɗiye wani abu, lokaci ya wuce da zata zauna tana kuka, zuciyarta dakkakiya ce, tanada ƙarfi kamar karfe, ta daɗe da sanin cewa A strong woman will always turn pain into power.
Ta miƙa hannu ta karb'i Arya dake kuka, a lokacin data ƙarasa kusa dasu, ita kuma Rafi'an su Nabila sai zaginta suke sbd tana kuka akan wannan yaron, Inna Ai ta wurgawa Hanam harara tana faɗin.
“Gara ai, gara kizo ki fitar min da shege daga rumfa,daga ke har uwarki babu na kirki, Ai mu Muhammadu ya gama b'ata nan zuri'a, tunda har ya auri mana dangin ano ba”
Hanam ta tsaya daga fita daga cikin rumfar, ta juyo ta kalli tsohuwar, zuwa lokacin kowa yayi shiru yana san ganin yanda za'a kaya, dan dama can a gidan basa san uwar hanam ɗin.
“Iya Ai, ya.....isheki haka, kiyi magana a kaina babu damuwa, amma kada ki ƙara dangantani da waccan matar, ni bani da uwa.....”
“shi kuma ɗanki bashi da uba ko?”
Inna Ai ta yi saurin faɗi, tana katse Hanam ɗin, harda wani miƙewa tsaye tana jijjiga,.
Hanam ta ɗaga kanta sama tana lumshe ido, tare da lasar lips ɗinta, bata so ta yi loosing temper ɗints, amma da alama yau Inna Ai tana so ta tunzurata, ga kukan Aryaan dake hawa mata kai, idonta ta buɗe.
“Lak kras wu laik!!”
(Kayi min shiru!!)
Ɗif, kukan da Aryaan ɗin yake ya ɗauke, sbd gigitaciyar tsawar data daga masa, ita ba ta san damuwa, sai yayi shiru yana kallonta, ta juya ga Inna Ai.
“For the last time zan faɗa miki wannan maganar, babu ruwanki da ɗana, ta ya na sameshi ?, waye ubansa ?, daga ina yazo ?, duka bai shafe ki ba, sbd wannan damuwata ce”
Ta nuna kanta
“Damuwatace ni ɗaya, sbd Arya ɗana ne ni ɗaya, ɗana, ina fatan kin fahimta?”
Tana kaiwa nan taja jakukunanta ta yi b'angaren Baabaa, matar kakanta ɗaya da duk gidan babu me ƙaunarta kamar ita. Dan mahaifiyar Abba ta rasu, kuma kakansu matanza uku yanzu.
Uchenna Franklin ya bar ƙfar gate ɗin gidan, bayan ya gama sauraren duk abinda ya faru, har cikin ransa yake tausayin Hanam, memakon su tambayeta cikin ruwan sanyi ta faɗa musu a ina ta samo yaron sai de kawai su riƙa jifansa da kalmar shege, me yasa ne haka ?, me yasa.....
“Ah-ah, Harisu ashe da kai aka zo ?”
Uche ya yi murmushi yana duban tsohon da suke tare da Abba.
“Ai kasan babu yanda za'a yi a zo ganinka babu ni, sbd nayi kewarka sosai”
“Ƙaryar banza, idan kana kewata ka dawo hakiɗau da zama, ka riƙi fatanya sai na yarda da kayi kewata”
“To ai ni ko ƙauyenmu ma bana zuwa sbd noma, haka kawai da kuruciya ta zan zo nayi ta maka noma kaida matanka da ƴaƴanka kuna ta ci ni kuma na tsofe na rasa me aure na ?”
Tsohon ya yi dariya irin tasu ta manya.
“Sai in baka ɗaya daga cikin jikokina”
Uche yayi dariya
“To ya Maman taka ta ke ?”
“Mamana lafiyarta ƙalau, tana Enugu”
“To idan kunyi waya kace ina gaishe ta”
“zakuwa taji”.
***
*Da misalin 08:00pm*
Hanam ce ke girki a ƙofar rumfar Baabaa, noodles take girkawa akan ƙaramin gas stove ɗin da ta taho da shi.
Hatta da noodles ɗin ma ita ta taho da ita, dan ita ba iya cin abincin gwana goma za ta yi ba, bawai abincin nasu ne ba zata iya ci ba, domin suna da cima me kyau, kawai de tsaftar masu girkin nasu ce bata yarda da ita ba.
Dan ta taso a cikin hausawa ne, amma wannan kyankyamin irin na larabawa a jininta yake, ko kaɗan bata san kazanta. Noodles ɗin ta juye a cikin plate sannan ta ɗorawa Arya baby feed ɗinsa. 
Data gama ta juye masa a baby bottle ( fida) ɗinsa me kan teddy, sannan ta kashe stove ɗin ta kawar da shi gefe, ta koma ɗakin.
Baabaa ta iske zaune tana lazimi ga Aryaan zaune a kan cinyarta, sai yunƙurin kamo carbin hannunta yake ita kuma Baabaan sai ɗaɗɗaga carbin sama take, sai ta miƙo masa kamar zata bari ya kama, kuma sai ta ɗga shi sama, shi kuma sai ya saba kansa sama sa hannunsa yana son ya kamo carbin.
Tayi musu dariya tana zama, hasken ƙwan lantarkin dake ɗakin ya haska ko ina, dan gidan kwana ake a yini da generator kamar ba kauye ba. System ɗinta ta cire a chargy, ta zauna ta shiga daddanawa tana cin abincin.
“Gashi ki bashi bulumbotin nasa ya sha”
Hanam tayi dariya
“saide na baki ki bashi da kanki”
Baabaa ta miƙa mata hannu, Hanam ta bata baby bottle ɗin.
“Amma fa da zafi”
“Bakya bashi abinci ne ?”
Hanam ta girgiza kai, tana ci gaba da danna system ɗin gabanta.
“Ina bashi, saide bana bashi me yaji”
Baabaa ta gyaɗa kai.
“Hanam ya kamata ace kinyi aure”
Hanam ba ta kalli Baabaa ba, dan wannan sabbabiyar maganace a wajenta, ta yi murmushi me ciwo, tana kai cokalin noodles bakinta.
“Aure ?, Baabaa babu wanda zai aure ni a haka, babu wanda zai aureni da ɗa, kowa kallon shege yakema ɗana, to waye zai auri uwar shege ?”
Tausayinta ya ƙara rufe Baabaa, tun tana ƙarama bata samu wani farin ciki ba, sbd uwarta data tafi ta barta, yanzu ta girma lokacin da ya kamata ace ta yi aure tana gidan mijinta kuma wata ƙaddarar da ban ta sameta.
“Kiyi haƙuri Hanam, Allah yasan da ke, wasu lokutan ɗan adam bai san sanda ƙaddarorinsa zasu ƙare ba, ki yi ta addu'a Allah zai baki wami sabon fata da ban”
Yanzuma murmushin ta yi kuma tana ci gaba da danna system ɗin.
“Baabaa nayi wannan addu'ar a baya, sai Allah ya bani Arya, na ɗauke shi a matsiyin wannan sabon fatan, shi da Abba kaɗai sun isheni”
Muryar ta fito cikin shaida abinda take faɗi gaskiyane, kuma haka ɗin ne bata buƙatar kowa ya shigo rayuwata, kullum cikin godewa Allah take daya azurta ta da Abba da kuma Arya.
“Salamu alaikum”
Sukaji sallama daga bakin ƙofa, Baabaa ta amsa. Uche ya leƙo ɗakin, Hanam tana mamakin yanda yake abu sai kace musulmi, ita dai bata amsashi ba, tanaga yanda suka gaisa da Baabaa kamar da suka saba sosai, abun ya bata mamaki.
“Hanam, Baba ne ke kira”
Uchenna ya faɗi yana duban Hanam, a hankali ta gyaɗa masa kai, shi kuma ya fita.
Ta miƙe ta saka takalmanta, wata farar cardigan dress ce a jikinta, ta san yanzu ba a gida take ba dan haka ta ɗauki wani ƙaramin gyale ta yafa a kanta, sannan ta karb'i arya a hannun Baabaa, ta ɗauki wayarta da ruwan gorarta ta fita.
A tsakar gidan taga gaba ɗaya ƙannenta da yayanta kamal ga abba ga uc3he a gefe, ga Inna Ai dake aiko mata saƙon harara.
Hasken globe ɗin dake wajen ya temaka mata wajen kallon kowa gaba ɗaya, daga gefen kakansu kuma ɗaya matar tasa ce, da kawunnansu suma suna zaune a wajen, duka de gida an taru, Baabaa ce kawai babu, waje ta samu ta zauna a kusa da kakanta tana masa murmushi
“Kai ɗan kauye baka kira Baabaan ba ?” Baba ya faɗi yana duban Uche.
“Wannan ai matarka ce, kaje ka kirata da kanka”
“Ja'iri ɗan nema, jeka kira min ita”
Uche na dariya ya shiga sashen Baabaa, Hanam de kam kanta ya kulle, taga kowama na gidan ya saba da shi, to yaushe hakan ta faru ?.
Bayan ɗan wani lokaci sai ga uche ya dawo  Baabaa na biye sa shi, hanyar ƙofa ya yi zai fita, Baba ya kirashi yana faɗin.
“Ina za kaje ?”
“Waje zan fita naga ka tara iyalanka ne, ban sani ba ko wasiyya zaka basu”
“Ɗan nema dawo ka zauna, ai kai ma ka zama dan gida”
Arya ya na ta ɗagawa Abba hannu Hanam ta miƙa masa shi tana faɗin.
“Abba gashi yana maka magana”
Abba ya karb'eshi yana dariya.
Nasiha Baba ya musu kamar yanda ya sabba musu idan aka taru irin haka, kuma ya ƙara da magana akan auren Hanam, ita de kawai jinsu take, dan ita tasa a ranta babu wani aure da za ta yi.

YADDA KADDARA TA SOWhere stories live. Discover now