YADDA KADDARA TA SO 24

44 6 1
                                    

⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:08130172702
Tiktok @SAI_KASKA
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*

★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★

*Na sadaukar da wannan babin zuwa gareki yayata Oum Ahmad*

*BABI NA TALATIN DA UKU (33)*
HANAM POV.
A hankali ta shiga motsa idonta, kafin hasken dake wajen ya shiga idon nata, ƙara meda idon nata ta yi ta rufe, tunanin abinda ya faru har ya kawota asibiti ya dawo mata sabo, Ita de bata san me ya faru ba, kawai Haris yace mata tazo su tafi, shi ne ya ɗauki Arya ita kuma ta bi bayansa.
Gidansu taga ya nufa, kuma tun daga shigarta falon gidan tasan cewa ba lafiya ba, dan taga kowa na gidan yana kuka, kowa ta tambaya lpy ?, sai yaƙi mata magana, Kamal ne kawai ya iya furta mata cewa
_ “Hanam Abba ne ya rasu, ya rasu a hanyarsa ta dawowa Abuja daga Lagos....”_
Suman da ta yi shine ya hanata fahimtar ƙarshen maganara, sai kuma data farfaɗo ba sai yanzu.
Zabura ta yi ta miƙe zaune, tana bin wajen da take da kallo, asibiti ne, tabbas asibitine, bata ma lura da wanda ke zaune a gefen gadonta ba saida ta ji ya riƙo hannunta, ta kai dubanta gareshi, Harees ne, yanayin yanda taga fiskarsa ne kawai ya tabbatar mata da abinda Kamal ya faɗi da gaske ne.
Kanta ta gyaɗa masa alamun da gaske ne?, shima ya ƙara gyaɗa mata nasa kan, ƙris ya rage bata koma ta sume ba, wata ƙilama itama mutuwar za ta yi, Abba ya mutu ?, wai Abba ne ya mutu ?, tunanin ma kansa hargitsa mata lissafi yake, taji iska bata shiga huhunta yanda ya dace, kamar an sakata a cikin kwalba an kulle, babu ta inda iska ke shiga bare ta fita, Mahaifin ta ne fa ya mutu, mahaifin ta da ya zame mata uwa kuma jigon rayuwa.
Sai ta nemi hawaye ma ta rasa, dan da gaske ne abinda aka faɗi, wani tashin hankalin yafi gaban kuka.
“An ƙaraso da gawar tasa, zamu iya tafiya”
Idanuwanta a bushe ta zuro ƙafafunta ƙasa, babu ko takalmi a mafarta, saida Harees ya bata takalmanta ta saka.
*
Yanda taga harabar gidan nasu a cike ne ya ƙara tabbatar mata da abinda aka faɗa mata, kasa shiga cikin gidan ta yi, sai ta tsaya a jikin ƙofar entrance, tana kallon yanda mutane ke ƙara tururuwa a gidan.
Babu yanda uchenna be yi da ita ba kan ta shiga cikin gidan amma ta ƙi, ta kafe makarar da aka aje a compound ɗin gidan da ido.
Kamal ne yazo ya mata magana cikin sanyin murya kamar ba shi ba.
“Hanam, ki shiga cikin gida”
Sai yanzu ta motsa, juyowa da kanta ta yi ta kalleshi, a gaba ɗaya rayuwarta a gidansu, magana irin haka bata tab'a haɗata da Kamal ba, kullum cikin takun saƙa suke, basu tab'a shan inuwa ɗaya ba.
A hankali kammanin fuskarsa ke rikiɗe mata zuwa na Abba, domin dama kaf gidansu babu me kamar Abba sama da shi, komai nasa ya ɗauko, halinsa ne kawai ya kwaso na uwarsa.
Sai yanzu ta ji wata ƙwalla na taruwa mata a ido, kuma a hankali ta sauƙo mata. Ƙafarta ta fara takawa zata shiga cikin gidan, har ta kai ƙofar ta ji ana ƙoƙarin ɗaukar makarar dan fita da ita.
Sai kuma ta juyo da sauri, a dai-dai lokacin wata mota ta shigo cikin gidan, masu makarar suka fita motar kuma ta shigo, Hanam ta ji wani kuka na ƙwace mata, yanzu shikenan zasu rabata da Abba, inde suka ɗauke shi ba zata sake ganinsa ba.
Ta nufi gate da gudu zata bi masu makarar ta dakatar dasu, ta faɗa musu cewa kada su fita mata da Abbanta, su bar mata shi taci gaba da kallonsa, Haris da Kamal ne suka yi kanta zasu ruƙota.
A sannan ne kuma ƙofar wannan motar data shigo gidan ta buɗe, wata farar balarabiya ta fito daga ciki, koda wutsiyar ido zaka kalleta zaka gano kammaninsu da Hanam, fari kawai zata fi Hanam ɗin, sai kuma shekaru, wasu yara ne guda uku suma suka fito daga cikin motar, wanda suma kana ganinsa kaga 'ya'yanta, dan suna kama da ita, mace ɗaya maza biyu.
“Hanam la shu hazal jnan! (Hanam wannan wani irin hauka ne!...)”
Cak Hanam ta tsaya, hankalin mutanen da suka rage a farfajiyar gidan ya dawo kansu, Kamal ya santa dan haka be yi mamakin ganinta ba, Haris ne ya tsaya yana kallonta, dama sauran ƙannen Kamal ɗin maza wanɗa basu san matar ba.
Hanam ta juyo ta kalli inda matar take, tunda ta taso bata tab'a ganinta ba, hotonta kawai ta sani, amma bata tab'a ganinta ido da ido ba, Matar dake amsa sunan mahaifiyarta, mahaifiya ?, mahaifiyar da bata shayar da ita ba, bata kula da ita ba, bata mata tarbiyya ba, bata bata ɗumin uwa ta sani ba, bata zaune da ita har girmanta ba, yau itace tsaye a gabanta tana mata magana cikin iko da isa harma da gadara.
Sai tashin hankalin da take ciki ya rikiɗa ya koma fishi, ta yi kan matar, Haris ya riƙo hannunta, amma ta fisge, hakan yasa ɗankwalin dake kanta ya faɗo, gashin kanta ya barbaje, wani a bayanta wani a kan fuskarta.
“Min inti ?!”
(wacece ke ?!)
Hanam ta tambaya idonta cikin na matar, wannan hawayen da ta fara ya ƙafe, idonta a bushe take dubanta. Cikin ƙarfin hali matar tace.
“Ana immik...”
(Nice mahaifiyar ki).
“Inti manik immi!”
(Ke ba mahaifiyata bace!)
Hanam ta katseta a tsawace, kuma tana ɗaga mata hannu, ta zaro mata ido tareda nuna matar da dan yatsa.
“Inti....manik...immi”
(Ke....ba....mahaifiyata bace)
ta maimaita mata dalla-dalla. Ji kake tas!, matar ta wanke ta da mari, Hanam ta dafe wajen sannan taci gaba da kallonta.
“Ana immik, iza biddik walala, ana hiya immik!”
(Ni babarki ce, ko kina so ko bakya so, nice mahaifiyar ki!)
Bisa ga mamakin kowa sai Hanam ta shiga yin dariya, zuwa lokacin matan gidan da yaransu dama mutanen ƙauye dana gari da suka zo jana'iza sun fito suma
“Akan me zaki mare ta ?!”
Kamal ya faɗi cikin wata iriyar fusata da yake jin tana tasowa tun daga ƙasan ruhinsa, bai tab'a jin tausayin Hanam ba kamar yau, su sunada iyaye mata a kusa da su, ita kuma bata da kowa sai Abba, Abban da ya mutu a halin yanzu.
Hanam ta ƙarashe dariyar ta kai hannu ta ture Kamal daya zo ya tsaya a gabanta, sannan ta kalleshi.
“Yaya, ka bar min wannan faɗan, nawa ne”
A karo na farko data fara kiransa da yaya, amna ya lura sam bata cikin hayyacinta, a lokacin ma Rashidat ta fito daga cikin gidan, hannunta riƙe da Arya yana kuka. Baabaa ce ta sauƙo wurin tana riƙo mata hannu.
“Hanam zo”
Ta fisge hannun bata ko kalli Baabaan ba.
“Baki shayar da ni ba, baki reneni ba, baki bani kulawar da uwa ke bawa ɗa ba, baki min komai da uwa kewa ɗa ba, shine zaki zo rana tsaka kice ke mahaifiyata ce ?”
Tai mata maganar cikin harshen hausa, dan tasan cewa tana jin hausar, sai kuma Hanam din ta fara hawaye, ta kai hannu ta tura gashin kanta baya.
“Me na miki Masarrat ?, me na miki ?, me yasa kika tafi kika bar ni?”
Ta kira sunanta na ainahi, cikin gunjin kuka, kuma tana murza goshinta, ta ja hanci sannan taci gaba.
“Wancan dake cikin makara, shine ya rene ni, ya bani kulawa, yamin duk abubuwan da ya kamata ace ke kika yi. Bayan kinsa ƙafa kin tsallake ni kin tafi, Abba ya bawa Mero ni, yace ta rene ni, Mero tace ai lokacin da kuka zauna tare kullum cikin mata sharri ki ke, dan haka bazata karb'eni ba, Abba yavyi haƙuri da wannan ya kaiwa Hajjo ni, ita kuma tace ita amarya ce, bazata iya renon ɗa ba. Haka Abba ya aje komai a gefe, ya reneni da kansa, kullum da kansa yake bani madarar yara, ya min wanka, ya sauya min kaya, tun ina jaririya har na tasa Abba bai dena reno na ba, na taso cikin gidan 'yan uba, waɗan da basa sona, kullum cikin hantarata kowa yake, tun ban gane hakan ba har nazo na gane, haka zansa Abba a gaba na tambayeshi shin ni bani da Mama?, sai yace min ina da ita mana, tayi tafiya ne, amma ta kusa dawowa, a koda yaushe haka yake cemin, har na taso na yi hankali, na gane cewa tafiya kika yi kika barni sbd san zuciyar ki, kullum kalaman da Mero ke faɗamin kenan akanki. Na kawar da wannan na rungumi Abba a matsayi uwata da ubana, domin bani da kamarsa”
Ta saki kuka me tsuma rai, data tuna cewar Abba fa ya mutu, ba zata sake ganin sa ba, kowa dake wajen saida jikinsa ya yi sanyi, hatta Mero da Hajjo, dan sun tuna lokacin da Abban yazo yana ta musu magiya akansu temaka su karbi yar tasa cikin tsimman goyo, amma kowacce a cikinsu taki, yayunta mata kuma da suka yi aure suka tuna yanda suka yi ta kyarar ta sanda tana ƙarama, hakama Kamal.
Hanam ta share hawayen dayaƙi tsayawa sannan taci gaba.
“Haka na taso cikin tabon rashin uwa, saide kuma hakan ni baya damuna, dan inada Abba. A sanda na samu ɗana sam banyi ƙokarin yada shi ba, duk kuwa da zan iya hakan, amma banyi ba, sbd me ?”
Ta tambaya tana kallon fuskar Masarrat dake ɗauke da damuwa, duk bata san cewa ta yi nadama ba sai yau, Hanam ta nuna kanta.
“Sbd akwai soyyayar uwa a tare da ni, lokacin da zan haihu babu kowa a tare da ni, ba yaya, ƙanwa ko ɗan uwa, ba uwa bare uba, daga ni sai maƙociyata, naci a zaba sanda zan haihu, har ta kai ma ance bazan sake haihuwa ba, bayan na haihu na ɗora ido akan waccan hallitar, naji duk baƙin cikina na duniya ya yaye, naji cewar zan iya kareshi daga duk wani abu na cutarwa a duniya, naji cewa zan zame masa katanga daga duk wani abu mara daɗi. Sannan a lokacin sai na yi tunanin cewa, idan har uwa zata iya jin wannan azabar kafin ta kawo ɗa duniya, to me zaisa ta tafi ta barshi?, wata ƙila ke baki ji irin azabar da naji ba, shi yasa har kika tafi kika barni, zuciyata ce ta faɗa min bakan”
Zuwa yanzu ta dena gunjin kukan, sai hawaye dake mata zuba, ta kafe Masarrat da manyan idanuwanta, tana jiran amsarta, bata tab'a tonawa wani cikinta kamar haka ba, bata taba faɗar ciwonta ba, koda Abba bata tab'a magana irin wanna da shi ba, ko wani ciwonta a cikinta take riƙe shi, bata barin kowa ya sani ciki kuwa harda ƙawayenta.
“Baki da amsa ko ?, na sani ai Masarrat, bazaki samo amsar ba,inti ananniye ya Masarrat, ma biddik yani li'annu ana bintu la Muhammad mu ?”
(kina da san kai Masarrat, bakya sona sbd ni 'yar Muhammad ce ko ?)
Ta girgiza kanta sannan taci gaba.
“Wata ƙila ba haka bane, au li'annu ana Hanam, Hanam yalli inti wulad tiyya, wa rahti wa taraktiya lahala, ma bihimmik amurah, am tattasili fiyya kil sini mu ?”
(ko kuma sbd nice Hanam, nice Hanam ɗin da kika haifa, sannan kika gudu kika barta, ba ki damu da lamuranta ba, kina kiranta duk bayan shekara ɗaya ko ?)
Sai kuma ta yi dariya.
“Inti bi hayatik marah tikun umm ya Masarrat, inti mara wa bas, manik um”
(A rayuwarki ba zaki tab'a zama uwa ba Masarrat, sbd ke macace kawai, ba uwa ba)
“Inti min bit kuni ?, la hatta rah tawa a'if idam umna, wa tikalli ha tabki bi hadolul kalam yalli andik!”
(wayece ke wai ? da har zaki tsaya a gaban Babarmu kina sakata kuka da waɗanan kalamana naki)
Hanam ta tsirawa yaron ido na 'yan wasu sakkani, Ta tab'a ganin hotonsa sau ɗaya akan dpn Masarrat ɗin, kuma ta tab'a faɗa mata cewa shine ɗanta na fari a auren da ta sake.
“Eh ba'arif ina hiyya umuk, wa ana ma andi ayyi haƙ annah, ilit wa rah irja'a id kalami, ya walad ummuk ananniyya, hai mara mabta'arif ma'ana kalmat um...”
(Eh nasan cewa mahaifiyar ka ce, kuma ni bani da wata dangantaka da ita, na faɗa kuma zan maimaita, yaro babarka me san kai ce, wannan matar bata san ma'anar kalmar uwa....)
Maganar ta maƙale a maƙoshinta sbd marin da Haris ya sakar mata, abun ya yi yawa, duk da tarin lefin da ta mata aƙalla ita mahaifiyartace, be kamat ace tana mata irin wannan rashin kunyar ba, ta dafe kuncinta tana meda gashin kanta baya, ta ɗago da idanuwanta ta kalle shi.
Sai kuma ta fashe da kuka ta kifa kanta a ƙirjinsa tana ci gaba da rera kukanta, Uchenna ya rintse idanunsa, Hanam ta nuna Masarrat cikin kuka tace masa.
“Harees ana ma biddi shufa la hai mara (Harees bana san ganin matar nan), kace mata ta tafi, ta tafi, ta tafi?!!...”
sai kuma maganar ta ɗauke dip!, sakamakon jikinta da ya saki, ta ƙara suma, Uchenna ya riƙeta da kyau, sbd kar ta faɗi.
Shi da kansa ya ɗauketa ya sakata a motarsa ,Sannan ya juya ga Masarrat.
“Nahnu asifin ya ammi, hiya galɗane, wa am uɗlub minnik samah, samihiya”
(Muna masu baki haƙuri ammi, ta yi kuskure, kuma ina nema mata yafiyar ki).
Ya ƙarashe hannayensa a haɗe🙏, alamilun roƙo, duk da halin alhinin da kowa ke ciki saida ya yi mamaki ciki kuwa harda Rashidat, domin bata tab'a sanin cewa ɗan nata ya iya larabci ba.
Masarrat ta share hawayenta tana kallonsa, bata tab'a nadamar abinda ta aikata ba sai yau, yau ɗin da 'yar data haifa a cikinta ta tsaya a gabanta tana faɗa mata cewar bata cancanci zama uwa ba, ita bata dace da zama uwa ba, haka tace, amma yanzu kuma ga wani da batama san waye shi ba yana bata haƙuri, harda kiranta da sunan uwa.
“La taƙal'a ya ibni, mani za'alane a badan, samahta”
(Kada ka damu yarona, raina bai b'aci ba, na yafemata).
Sai ya gyaɗa mata kai yana takawa ys soma barin wurin.
“Min bit kun ?”
(waye kai ?)
Ba tare da ya juyo ba ya amsa ta da.
“Ana bi kun zauja (Ni mijinta ne)”
Su Mero da 'ya'yanta sai kukan nadama suke, Hakama Hajjo, duk da ita bata wani ƙuntatawa Hanam ɗin sosai ba.
Haris ya tsaya a gaban Rashidat yana ƙoƙarin karb'ar Arya, sai ta girgiza masa kai
“No, you go, and take care of your wife, ka barmin shi, zan kula da shi”
“Kin tabbata ?”
Rashidat ta gyaɗa masa kai, shima sai ya gyaɗa mata kan.
“Idan kin shirya tafiya kimin magana, sai nazo na ɗauke ki”
“Kada ka damu, a gidan Hajiya zan kwana ai, fatan de yaron yana cin abinci ?”
Kansa kawai ya gyaɗa mata, dan tsabar damuwa ya rasa ina zai saka kansa ma, motarsa ya koma sannan ya tuƙa motar zuwa Cosgrove estate.
Yana zuwa ya shimfiɗe Hanam a ɗakinsa, sannan ya kira Dr. Hasina, dan tazo ta dubata.
Yana zaune a wurin har tazo ta dubanta, sannan ta sanar masa cewa ba wata babbar matsala bace, amma duk da haka hankalinsa bai kwanta ba.
Har zuwa bayan isha yana zaune a wurin, kafin ya yanke shawarar zuwa ya watsa ruwa a jikinsa, wata ƙila ko zuciyarsa zata huce.
Saide me?, yana shiga bandlɗakin beko cire kayansa ba ya tsaya akan shower tana zuba akansa, ya rasa tunani me kyau akansa. Tunanin Abba ya dawo cikin kansa, ba shiri yaji wani kuka na neman kufce masa, kukan da ya yi ta riƙe shi tun jiya, kukan da ya hana shi fita tun jiya har zuwa yau ɗin nan.
Kasa riƙe kukan ya yi, dan haka ya ƙyaleshi ya fito, ya shiga rera kunsa amma mara sauti, jikinsa na karkarwa sbd kukan da yake ɗin, ya juya yana kallon bango, tare da dafe bangwan da hannunsa.
Can kuma da takaici ya ishe shi sai ya naushi bangwan, wani abu na suya a zuciyarsa, ba 'ya'yan Abba ne kaɗai suka yi rashin sa ba, shima ya yi rashin Abba, a hankali memories ɗin Abban suka shiga dawo masa. Yaci gaba da kunsa yanzu harda shessheƙa.
Hannu yaji ya dafa shi daga baya, hakan ke nuna masa cewar Hanam. ta farka, ya yi sauran kai hannu ya share hawayen sannan ya juyo ya kalleta, tsaye take a bayan nasa itama ruwan na zuba a kanta, gashin kanta dake a hargitse ɗazu zuwa yanzu ya kwanta a bayanta sbd ruwan.
Yaga itama hawaye take, abinda yaga a fuskarta ne yasa ya kasa riƙe kukansa sai kawai ya rungumeta ya shiga rera sabon kuka, itama ta riƙeshi gam tana nata kukan, still ruwan yana zubowa a kansu.
An rasa waye zai rarrashi wani, domin babu wanda be yi rashi a cikinsu ba, shine ya fara ƙoƙarin seta kansa sannan ya saketa, ita har yanzu tana hawaye, wanda ya kasa banbance shi sbd ruwan dake zuba akan fuskarta.
Hannu ya kai ya tallafo fuskarta yana kallonta, kafin a hankali ya kai bakinsa kan nata, a karo na farko ya yi abinda bai tab'a ba, bai tab'a sumbatar mace ba koda wasa, kusan a tare suka lumshe ido.
Hanam bata tab'a tsintar kanta cikin irin yanayin ba, this was the first time ever da hakan ya faru da ita, a hankali Haris ya janye bakinsa daga kan nata, amma goshinsa a kan nata, tana jin yanda yake meda numfashi, hannayensa biyu ya saka ya kamo kugunta, sannan ya shiga raɗa mata kalaman ban haƙurin da bai samu ya mata ba.
Da yasan yanda kalaman nasa ke ƙona mata zuciya da bai fara ba, ita fa ta'aziyya ƙara tada mata miki take, shima kuma ya gane hakan, jin yanda teke shirin yin kuka, ya lalubo kunnenta sannan ya furta mata.
“ I have falling for you Hanam, I am sorry”
Sautin maganar tasa yasa jikin Hanam rawa, tsigar jikinta ta tashi, ba shiri hannayenta suka kewayo bayansa, sannan ta riƙe rigarsa ta baya, ta riƙeshi gam, kamar hakan ne zai sa ta dena jin abinda take ji.
Hannu ya kai ya kashe shower ɗin, sannan ya dawo da fuskarsa baya kaɗan, yana kallon fuskarta, idonta a rufe yake ruf, ruwan daya sauƙa a jikinta yasa fuskar tata jiƙewa, hakama kanta.
Kafin a hankali ya ƙara meda bakinsa kan nata, ya shiga kissing ɗinta a hankali, Hanam ta ƙara ƙanƙame rigar tasa, yayinda numfashinta ya shiga kai kawo a maƙoshinta.
_____________________
_To jama'a ina miƙo masa saƙon ta'azziyar Abba, Allah ya ji ƙasa ya gafarta masa, haskiya an rasa mutumin kirki😞_
_jiya banga comments ba, kode babin be muku daɗi ba ?_
_To a har kullum de ina muku godiya🙏_
🌸-SAI KASKA CE✍️-🌸.

YADDA KADDARA TA SOWhere stories live. Discover now