05

985 43 5
                                    

*ƘAZAMAR AMARYA*

Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 5.

Da dare.

Sakina bata yarda tayi wani kuskure da zai fusata Hamid ba, dan har hira suka ɗan yi a falo bayan ya kammala cin abinci, daga bisani ya shige ɗaki ya barta da yara, itama ta tasa ƙeyar yaran ko wanne ya kwanta a ɗakinsa, kana ta kwantar da Rauda tayi barci sai ta tashi ta shirya cikin wasu kayan barci masu kyau ta gyara sumar kanta da yake a cefe ta feshe jikinta da turare kana ta saka hijab ta yiwa Rauda addu'a sannan ta fito ta jawo ƙofar a hankali ta nufi ɗakin Hamid, tun kafin ta shiga ta ji muryansa yana waya, sai da ta tsaya jim ta fahimci da Madina yake wayar, kamar zata juya ta koma ɗakinta sai kuma ta danne zuciyarta tunawa da shawarar da yaya Umma ta bata, sai kawai ta kama handle ta murɗa ta shiga ɗakin da sallama,Hamid ya waigo daga rufda cikin da yayi yana kallonta ga wayar a kunnensa yace cikin haɗe rai.

Lafiya?

Sakina sai da ta haɗiye miyau kafin ta danne abinda taji a ranta ta samu gefen gadon ta zauna tana cire jihab ɗinta ta ninke, da kallo ya bita ya tashi ya zauna, a lokacin Madina take cewa.

Baby Hamid waye ya katse mana hirarmu ne naji kayi shuru.

Madinar Hamid ki yi haƙuri zan sake kiranki.

Sai ya gimtse kiran ya mayar da dubansa ga Sakina da take ta sakin murmushin yaƙe.

Meya faru? lafiya kika zo nan.?

Haba Abban Mufeeda ya kake tambayata dan na zo mu kwanta.

Na kira ki ne?

Ya faɗa yana haɗe rai.

Yanzu sai ka kira ni ne zan zo mu kwana tare. Ina ce ba yau muka saba haka ba ko ka kwana ɗakina ko na kwana a nan.

To ban gayyace ki ba ki tashi kije ki kwanta a ɗakinki, haka kurum kin katse mini hira saboda jaraba ta kunno ki, ina ce yau kusan kwana biyar baki kwana anan ba, to duk ƙulaficinki sai dai ki mayar da shi dan na fara gyara dan tarban amarya ba zaki zo ki ɓata mini shiri ba.

Wani irin kallo Sakina take binsa dashi cike da mamakin furucinsa, wanda nan take hawaye suka cika mata ido har jikinta ya soma rawa saboda tsananin dukan da maganarsa tayi mata a zuciya, cikin hasala ya cigaba da cewa.

Shekara nawa muka yi muna a tare, dan haka yanzu kya sarara mini na yiwa Amarya tanadi, in ma wani abin kika sha ya tsayar miki da jaraba to sai ki san yadda zaki yi, ki tashi ki fita mini a ɗaki.

Sakina lumshe ido tayi hawayen daya taru a idonta ya sauka a kuncinta, bata ce masa komai ba ta miƙe riƙe da Hijab ɗinta dan tama kasa mayar da shi a jikinta, jiki a sanyaye ta fice daga ɗakin ko rufo masa ƙofar ma ta kasa yi ta koma ɗakinta tare da rufe ƙofar da key ta zauna a ƙasan tiles ta saki wani wawan kuka mai tsuma zuciya, da yake dare ne kukanta har falo ana ji dan da ƙarfi take yinsa saboda wani abu data ji ya danne mata ƙirji, jikinta har ciccira yake tana fidda gumi, haka fuskarta ta dame hawaye da majina tana yi tana gogesu da hijab ɗinta data ƙanƙame da hannunta, tunda take ba a tana wulaƙantata irin wannan ba, Hamid ya kai ƙololuwar ci mata fuska ya muzantata mafi muni data ji kamar ta haɗiyi rai dan baƙin ciki, sai da tayi mai isarta kafin daga bisani ta sassauta kukan ta ja jikinta zuwa jikin gado ta jingina bayanta tare da lumshe ido hawaye ne kawai ke gangarowa a kuncinta, alwashi da alƙawari ta riƙa ɗaukarwa kanta ba zata kuma kai kanta ɗakin Hamid ba zata nuna masa ita 'yar halak ce, zata nuna masa zata iya rayuwa ba tare da ya kuma kusantarta ba, nan take ta yiwa kanta alwashin bashi wata guda da amarya ba tare da ta amsa girki ba, yadda zai samu damar sauke duk wani gyara da ya yi akanta, koda ta amsa girki bata jin zata bashi haɗin kai kowa kuwa ya kawo kansa yana magiya sai ta jashi a ƙasa kamar yadda ya wulaƙantata yau, dan ba zata taɓa iya yafe masa wannan ba dole ne ta nuna masa ita macece 'yar halak, haka ta raba dare a haka sai da taji kanta yayi mata nauyi saboda sara mata da yake yi, kafin ta miƙe da kyar ta shiga bayi ta ɗauro alwala ta dawo ta kwanta tayi addu'ar barci kana ta cigaba da jan istigafari a ranta, tayi alƙawarin binne wannan damuwar a ranta ba zata faɗawa yaya Umma ba dan ya kamata ta koyawa kanta riƙe damuwa ta kuma iya ƙoƙarin magance shi da kanta, a haka barci ya ɗauketa.

KAZAMAR AMARYA Completed Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang