*ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabirPage 7.
Madina tunda biki ya matso ta zama busy, shirye shiyre take ba kama hannun yaro duk wani gyara daya tace tayi to tayi shi, dan har gyaran jiki aka soma yi mata kusan kwana biyat da ya wuce, yanzu ma jikinta an shafe shi da kurkur haɗe da kayan gyaran fata tana zauna daga ita sai ɗaurin ƙirji akan wata kujerar ƙarfe a ɗakinta, da ƙawayenta da mai gyaran jiki duk suna ɗakin sai hira suke yi, yayarta Aisha ce ta shigo riƙe da ƙaramin ɗanta da take goyo, Madina tace.
Anty Aisha har masu kawo lefen sun wuce ne?
Eh sun tafi, Kausar zaku iya zuwa ku ga Akwatin.
Aisha ta faɗa tana duban ƙawayenta, da sauri suka miƙe duk suka fice har da mai gyaran jikin, dama tayi hakan ne domin su bata guri dan tayi magana da Madinar, Aisha ta kalleta da kyau tana cewa.
Gaskiya Madina ban ji daɗin ganin lefenki haka ba, Hamid yayi ƙaranta da yawa a yadda muke zaton zai yi miki ba haka yayi ba, domin kuwa babu kaya sosai kwata kwata zannuwa basu fi talatin ba sai sauran kayan tarkace, kuma akwati set ɗaya ne guda huɗu da kit wanda mukai zaton ki samu set biyu.
Madina zabura tayi ta miƙe tana zaro ido cike da damuwa ta dafe ƙirjinta tana cewa.
Amma Hamid yaci mutuncina ban zaci haka ba wlh, yadda yake ta kuranta ya kashe mini kuɗi a akwati, muje na gani.
Ta faɗa tana bin gefen Aisha ta fita zuwa falo, Aishan ma bayanta tabi, suka tadda mutanen falon sunata ɗaga kaya sai yabawa suke yi, mom dai taɓe baki tayi tana cewa.
Ni kam Wlh bai burgeni ba lefen, yadda dai nasan Hamid yana da kuɗi ai Madina tafi ƙarfin waɗannan kayan.
A'a fa Hajiya wlh yayi ƙoƙari domin duk zannuwa masu tsada ya saka babu na banza a ciki.
Cewar wata kasar momy, Madina ji tayi idonta ya kawo kwalla dan gabaɗaya ganin kayan baisa tayi farin ciki ba sai damuwa data samu kanta a ciki musamman furucin mom data yi, momy ta mele baki.
Hajiya Sa'a yaron fa yana da mugun kuɗi wlh, kawai dai ya nuna shi ƙaramin mutum ne amma yadda yake da arziki ya dace yayi kayan da suka fi haka, yace ma zai bata mota ai ya dace yasa key ɗin a ciki.
Nan dai mutanen falon suka shiga mayar da magana wasu suna yaba kaya wasu kuma suna zancen ƙila ƙaryar arziki yayi musu amma yadda madina take da kyau da ilimi ai ta wuce waɗannan kayan, da sauri Madina ta juya zuwa ɗakinta ta fashe da kuka, jikinta yana rawa ta ɗauki wayarta ta kira Hamid bugu ɗaya ya ɗauka yana cewa.
Amaryata kuma farin cikin Hamid ya aka yi.?
Abdulhamid.
Madina ta ambata cikin kakkausar murya, Hamid dake zaune saida ya gyara zama dan bai taɓa jin ta ambaci sunansa gabaɗaya kaitsaye irin haka ba, yace cikin bata dukkan matsuwarsa.
Meya faru ne Madina? naji muryarki wani iri.
Dole kaji muryata haka domin ka bani mamaki, yanzu fisabilillahi ban fi ƙarfin kayan daka saka a akwati ba, duk kuɗin ka ace akwati set ɗaya zaka yi mini sannan kaya 'yan kaɗan, gashi kasa family sai ƙorafi suke yi acewarsu yadda na haɗu ga ilimi bai dace aga akwatina haka ba, sannan kace zaka bani mota ai kamata yayi ka saka key ɗinsa a cikin akwatin.
Haba Madina ya kike magana kamar baki san yadda na keta fafutukar faranta miki ba, kin kuwa duba kayan ciki gabaɗaya kuwa, to babu zanin daya gaza dubu sha biyar a ciki daga haka ne zuwa dubu ɗari biyu da wani abu fa, duk kayan ciki masu tsada ne, ai in baki yaba mini ba bai dace ki kushe mini ba, dan haka ni gaskiya abinda zan iya yi miki kenan. Maganar mota kuma ni ban iya ƙarya ba bazan saka key ɗin a ciki ba haka nayi niyya, idan kin zo gidana sai na baki.
