*ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabirPage 38.
Koda suka kammala cin abincin a falo suka yada zango suka cigaba da kallo, wajen ƙarfe tara Sakina ta sallami yara duk suka shiga ɗakinsu suka kwanta, dan yanzu Rauda ta fara yarda ta kwana da Mufeeda hakan yasa falon ya rage sai su kaɗai, Sakina ta muskuta tana dubansa.
Ya kamata kaje ka watsa ruwa naga lokaci ya tafi.
Hmmm kinsan kuwa na sha'afa, gabaɗaya yau ɗin nai kin rikita mini kai ba ga kwalliyarki ba ba ga abinci ba, komai yayi Masha Allah, wai in tambayeki mana.
Ina jinka Abban Mufeeda.
Yauwa! menene sirrin ne naga gabaɗaya duk kin sauya? Jalila ina ga ta baki wani maganin daya sauya ki ba kika dawo 'yar caras dake ko? wai dama haka kike duk tsawon lokacin nan kika nima mayar da kanki tsohuwa.
Ya ƙare maganar yana 'yar dariya, itama dariyar tayi bata ce komai ba dan ba tada amsar da zata bashi saboda basu saba hira irin haka ba, Hamid ya ɗaura da cewa.
Da tun farko nasan zaki iya sauyawa da tuntuni na turaki Kano kin ƙaro cos a gun Jalila, ƙila da babu abinda zaisa na ƙara ma aure wlh.
A'a fa ka daina wannan maganar dan bazan mance irin giyar soyayyar amaryarka daka sha ba, ka dinga amayar mini da ɗokin zuwanta a gidan nan, dan haka kayi shuru kawai.
Hmmm Sakina kenan, ba zaki ganne bane amma ina mai ƙara baki hakuri akan faruwar wasu abubuwan, Allah ya huci zuciyarki yanzu muje nayi wanka sai ki haɗo mini cofee nasha kafin mu kwanta.
To tace masa tana murmushi ta miƙe tayi gaba ya bita a baya, sai da ta fara haɗa masa ruwan wanka kafin ta fito ta wuce ɗakinta ta fara kuskure bakinta da mouth wash, ta wanke kwalliyar fuskarta ta fito ta shafa mai a fuskar da man baki, sai ta ciro kayan da zata saka, sai dai tsayawa tayi tana tunanin saka su dan bata taɓa saka irin su ba bata so Hamid ya gano ta zaƙe da yawa, dan haka ta mayar da kayan masu shara shara ta ɗauki wasu masu kyau riga zuwa rabin cinya da dogon wando, ta saka su tare da shafe jikinta da humra mai sauƙin ƙamshi ta saka turaren data ware na barci a jikin kayan ta zura hijab da nufin fitowa, ta isa kitchen dan haɗa masa cofee.
Madina tunda taji sun bar falon sai ta fito da sauri ta wuce kitchen dan ta ɗiba abincin da suka rage taci kamar dai jiya, ta buɗe taga tuwo nan take ta haɗiye miyau dan sosai cikin jikinta ya saka mata ƙaunar tuwo, ta buɗe miyar taga miyar yauƙi ne nan ma taji daɗi sosai dan haka cikin sauri ta ɗauki plate ta saka tuwon da miya ta ja kujera ta zauna ta soma saka loma tamkar tana cin nama saboda mugun daɗin da yayi mata, a wannan yanayin ne Sakina ta shigo kitchen ɗin, Madina tayi saurin aje plate a gefenta ta miƙe tare da ɓoye hannunta baya tana wani cin magani da zazzare ido kamar mage a kwali, sosai ta bawa Sakina dariya dan sarai taga yadda ta zura lomon tuwo a bakinta lokacin da ta shigo, sai ta gimtse dariyar tayi kamar bata ganta ba ta isa gefen inda kayan kitchen ɗinta yake, nan ta shiga haɗawa Hamid cofee ɗinsa harta gama Madina tana nan a tsaye kamar fosta ita bata cigaba da abinda take yi ba bata kuma fita ba, Sakina ta yi kamar ta fita sai Madina ta koma ta zauna ta ɗauko plate ɗinta ta zabtari ƙaton loma, takai bakinta kenan Sakina ta ƙara shigowa zata ɗauki cokali kuma da gangan ta ki ɗauka dan dai ta ƙara kama Madina, ai Madina tsayawa tayi ga lomar tuwo takai baki bata ƙarasa ci ba ga kuma plate a hannunta, wani sabon fosta ta kuma yi, a wannan lokacin Sakina sai da tayi dariya mai sauti.
Daɗi na da gobe saurin zuwa. Allah na gode maka.
Ta faɗa tare da ficewa tana dariya, Madina wani haɗe rai tayi tana cin magani, sai dai duk rashin kunyarta sai da taji nauyin ganinta da Sakina tayi da abincinta tana ci, tunawa tayi da lokacin da tayi mata rashin mutunci kan an ɗibar mata dambun da Hajiya ta kawo mata, maganar Sakina yana nufin habaici ta sakar mata kenan, taja guntun tsaki ta kai loman bakinta tana cewa a ranta.
