Kuna neman group din daza kur dinga sarin kayan kitchen masu sauki wanda duk yanda zaku karade kasuwa bazaku samu kasa da irin farashinmu ba!!! Kuyi joining a mai nono kitchen utensils and more domin siyan daidai ko sari gamasu kiran waya zaku tintibemu akan wnn layin 09135298054
*ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabirPage 24.
Madina tana isa sashin su Hajiya ta faɗa ciki ko sallama babu, wanda kukanta shine abun da ya fara yin iso garesu, daga Alhaji har Hajiya a cikin tashin hankali suke miƙe tsaye suna kallonta dan duk suna zaune cikin falon kuma zatonsu ya basu ko Hamid ne rai yayi halinsa, tunda ga bigiren da suke ciki na rashin lafiya, Alhaji yayi ƙarfin hali yace mata.
'Yata kukan me kike yi haka? wani abun ne ya ƙara samun Abdulhamid?
Madina ta seta kukan tana share hawaye tare da koro musu bayanin wai ya hanata zuwa aiki akan sai ta riƙe masa yara saboda Sakina ta bar gidansa ba a san inda ta nufa ba, ba Alhaji ba hatta Hajiya sai ta taji mugun takaicin Madina yadda ta tayar musu da hankali sosai, Alhaji bai iya ƙara magana ba ya yi hanyar fita Madina ta rufa masa baya tare da Hajiya, duk da bata jin ƙarfin jikinta amma dole ta bisu taji kanun labari. Koda suka isa falon sun tadda Hamid yana cin abinci tare da yara suna kallo, baiyi mamakin ganin iyayensa tare da Madina ba dan yasan tunda ta fita to can tayi, yanzu ne ya ƙara tabbatar da Madina sargartacciya ce ga rashin wayo da rashin hankali gabaɗaya ba tada lisaafi, balle ta riƙa yiwa kanta tunanin abunda yake daidai, bai iya yiwa su Abba magana ba suma basu yi masa ba duk suka samu guri suka zauna suna kallonsa, har sai da ya kammala cin abincinsa ya miƙe ya kai plate kitchen ya wanke hannu ya dawo yasha ruwa kafin ya cewa su Mufeeda su shiga ɗaki su jirashi, tace to tare da jan ƙannenta suka shiga ɗakinta a sannan ne Abba ya soma magana.
Madina taje mana da maganar kace ba zata je aiki ba zata riƙe maka yara saboda Sakina ta bar gidanka, to ni bazan tambayeka meya faru da ya saka Sakina ta bar gidanka ba, sai dai ina so ka sani wajibi ne ka cikawa yarinyar nan alƙawarin da kasa muka ɗauka a lokacin da muka je niman aurenta, na lallai dole zata yi aiki kuma muka amince, Madina ba zata zauna dan riƙe maka yara ba kasan yadda zaka yi dasu.
Abba ai har motar da ya ce zai bani yace ya fasa ba zai bayar ba.
Cewar Madina tana turo baki, Alhaji ya dube ta yana cewa.
Ban san lokacin da ya yi miki wannan alƙawarin ba, dan haka bazan iya cewa komai akai ba idan ya ga dama ya baki in bai gadama ba ya riƙe wannan tsakaninku ne. Hajiya tashi mu koma gida.
Ya ƙare maganar yana dubanta, Hajiya cike da damuwa tace.
Ka bari yayi mana bayanin abinda ya haɗasu da Sakina ta tafi tabar yaranta, kasan dai a wannan gaɓar Madina ce ta dace ta riƙe masa su tunda ko ni ba ni da ƙarfin riƙe su, meye amfanin yin mata biyun? yanzu koda ace Sakina tafiya tayi ko taje wani sha'ani Madina ba zata kula masa da yara ba, ai wannan ba magana bace tunda tasan mai mata da yara ta aura, dolenta ne ta saka a ranta zata yi hidimarsu.
Ni bazan saurari maganar matsalarsa da Sakina ba domin na daɗe ina ja masa kunne akan karya ƙure fushinta, na tabbatar tunda ta iya tafiya tabar yaranta to ya kaita bango ne, sannan kina maganar Madina ta kula masa da yara kinga tana da natsuwa da hankalin da zata iya riƙe su? Ita kanta bata gama riƙe kanta ba balle ta kula da wani, ko so kike ta riƙa dafa musu abincin da kullun sai sun ziyarci asibiti, dan haka duk tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa kan duka kuma duk wanda ya siya rariya yasan zata zubda ruwa, tun lokacin da akace mini 'yar mace ce nace ya haƙura domin ba lallai a sameta da tarbiyyar da muke tunani ba fiye ga wacce namiji ya zama jagorarta ba, amma me yace? cewa yayi yarinyar tana da ilimin zamani dana addini mahaifiyarta ta kula da tarbiyyarta sosai, ba yi da tantama akan ta zai samu farin cikin da yake buƙata. Gashi yau kwananta tara a gidan abubuwa da dama sun faru wanda tuni na gano wannan tafiyar cike yake da Gargada, Allah ya sauwaƙe, ki tashi mu tafi gida shi da ya kwanto kura yasan yadda zai yi da ita ai.
