39

1K 44 8
                                    

*ƘAZAMAR AMARYA*

Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 39.

Iro ne ya gyara gurin aman kana ya fita, sai Sakina ta fito tayi mopping ɗin kitchen kana ta ɗaura musu abin kari, Hamid kuma shiryawa yayi sai yayi sallama da Sakina ya fice abinsa bai sake bi ta kan Madina ba. Haka ta gama shirya 'yan makaranta suka tafi kana itama ta samu damar hutawa da nufin anjima zata yi sauran aikinta.

Madina jin ƙarar fitar motar Hamid yasa ta soma kukan baƙin ciki akan yadda ya nuna ko in kula da rashin lafiyar ta, hakan yasa ta ɗaga waya ta kira momy tana kuka ta faɗa mata bata jin daɗi kuma Hamid ya sani amma ya fice abinsa, momy ranta ya ɓaci sosai sai kawai tace ta shirya zata zo ta ɗauketa suje asibiti, haka suka rabu a wayar Madina ta gyara kwanciya dan yadda take jin jikinta ko wanka ma ba zata iya ba. Koda momy ta zo a bakin gate tayi parking ta kira Madina a waya akan ta fito su wuce, da kyar ta iya miƙewa ta saka hijab ta fito ta shiga motar suka kama hanya.

Binciken farko da likita yayi ya tabbatar da tana da maleria ne sannan kuma da laulayin ciki, nan ya ɗaurata akan magani daga bisani ya sallamesu, Momy gida ta wuce da Madina sai da ta tabbatar da ta samu natsuwa taci abinci da magani sannan tayi wanka kafin tasa Madina ta kira mata Hamid a waya, sai da tayi masa kira uku ana huɗu ne ya ɗauka a fusace dan ya manna mata masifa, amma jin ba muryanta bace tayi sallama ya sashi sausauta fushinsa, momy cikin haɗe rai tace.

Da Momyn Madina kake magana, yanzu Hamid duk bayanin da nayi maka akan yadda Madina take rayuwa bai gamshe ka ba, ace yarinya tana rashin lafiya amma ka shure ƙafa ka barta cikin wani hali, to gaskiya idan kasan ba zata iya riƙe ta ba to ka dawo mini da ita bazan jure ka wulaƙanta mini 'ya ba wlh.

Ayi haƙuri momy babban uzuri ne ya fitar dani, kuma dama na bari inna dawo gida zamu je asibiti.

Na riga naje na ɗauketa munvje asibiti taga likitanmu, dan haka in ka gama abinda kake yi ka zo ka ɗauketa a gida, amma gaskiya bana so daga aure a fara samun matsala da kai, dan ba haka muka yi zato ba a gunka.

In Sha Allah za a gyara ayi haƙuri.

Abinda ya faɗa kenan sai ta kashe wayar, Hamid yasa duka hannunsa ya tallafe kuncinsa, shi dai kam yasan ya saka ƙafarsa a cikin damuwa, tsabar sakarci da rashin wayon Madina yake gani, a madadin ta kirashi sai ta kira mahaifiyarta dan kawai aga rashin kyautawarsa, abinda yasan Sakina bata taɓa yi masa ba kenan, hasalima bata taɓa kai kararsa gurin danginta ba shine ma yake faɗa musu matsalolinta, yanzu ne ya ƙara tabbatar da tarbiyyar Sakina da kuma haƙurinta, haka ya yini a office yana tunanin yadda makomar aurensu zai kasance da Madina, dan hanyar da ta ɗauko baya tunanin mai ɓullewa ce.

Yau da wuri ya dawo aiki dan bayan sallar La'asar ya shigo ya samu Sakina tana ta aikin girki a kitchen, duk da ba tayi wanka ba amma tana cikin kyakkyawar shiga wanda tayi tun tashinta barci ɗazu. Yayi wanka ya fito ya shirya ya sameta a falo tana aikin yanka ganyen latas, yana gyara karin hularsa yace mata.

Madam yau salad za muci kenan?

Eh shinkafa da miya nayi mana kuma kasan zaka so a haɗa da salad harma da cream salad ɗinsa.

Gaskiya ne shiyasa kike matuƙar burgeni, in dai a abinci ne ko ban baki zaɓi ba kinsan me zaki yi naci yayi mini daɗi.

Abban Mufeeda yau da gobe akace ƙaryata boka, zama ne da an jima kaga ya dace ace nasan wasu abubuwa dan gane da kai ba sai an faɗa mini ba.

Wannan gaskiya ne, ni zan je gidan su Madina ashe ɗazun mahaifiyarta ta kira wai ba tada lafiya maimakon ta kirani, shine yanzu zan je da ɗaukota, gabaɗaya na rasa ina yarinyar nan hankalinta yake sam ba tada lissafi, ɗazun fa zo kiga maganganun da maman faɗa mini, raina ya baci sosai amma haka na danne tunda ni na jawa kaina, auren nan matsala kawai ya jawo mini ya zame mini ciwon ido.

KAZAMAR AMARYA Completed Où les histoires vivent. Découvrez maintenant