34

1.8K 54 10
                                    

*ƘAZAMAR AMARYA*

Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 34.

Madina bayan ta shiga gidan Maman Murja ta zauna suka shiga yin hira bayan ta turawa mata dubu ɗari da malam yace ta bayar, a cikin hirarsu ne take bata labarin taƙaddamar da tayi da Hamid yanzu kafin ta shigo gidanta, maman Murja ta mele baki tana cewa.

Gwara da kika yi masa haka karki yarda kiyi masa sakwa sakwa ya raina ki, kuma aikin malam ma zaifi tasiri in kika nuna masa kema jan wuya ce.

Ai wlh ni bai isa ya riƙa takura mini ba balle yq yi mini kulle.

Kuma bari ki ga ki koma babu abinda zai iya yi miki sai dai hargagi. Ke Murja sakawa Amarya ɗan wanken in kin gama.

Cewar maman Murja ta ƙare maganar ga 'yarta, Madina ta washe baki.

Ɗan wake kuka yi? Aiko zanci dan na kwana biyu ban ci ba.

Ai shiyasa nace ta zuba miki saboda ɗan marmari ne ba kowa ke damuwa da yinsa ba.

Cewar maman Murja sai suka cigaba da hira har aka kawowa Madina ɗan wake ta saki ciki taci tana santi, ba ita ta bar gidan ba sai misalin ƙarfe biyu da rabi.

Hamid tunda ya gaishe da Abba bai zauna ba, ya fito ya yiwa Hajiya sallama akan zai fita sai ya dawo gidansa, shuru shuru ba labarin Madina bata dawo ba har aka kira sallar azahar yaje masallaci yayi salla ya dawo, haka ya cigaba da zama a falon yaga lokacin shigowarta. Madina da sallama ta shigo falon tana ganinsa ta wani haɗe fuska tazo taza gotashi ba tare da tayi masa magana.

Madina!

Hamid ya ambaci sunanta cikin kakkausar murya, sai ta ja ta tsaya ba tare da tazo inda yake ba.

Wani irin rashin mutunci ne haka? nayi kama da tsaranki da zaki riƙa kawo mini raini a cikin gidana.

Madina tayi banza dashi bata tanka masa ba, Hamid saboda ɓacin rai a fusace ya miƙe yana nunata da yatsa.

Wlh baki isa ki riƙa taka umarnina son ranki ba, kuma aikin da kike takama dashi idan naso zan hanaki yinsa, ki bar ganin Abbanmu ya saka baki ina da damar da zan yi hukunci a gidana, kuma daga yau idan kika ƙara fita bada izini ba ba ki tabbatar a gidanku zaki kwana, banza mara mutunci! Ai bansan cewa ke ɗin ba kida tarbiyya ba sai yanzu, nayi dana sanin aurenki wlh dan babu abinda ya haifar mini sai damuwa.

Ni kake faɗawa maganganun da ranka yayi maka? wlh kayi kaɗan Hamid, ni ba 'yarka bace da zata tasa a gaba kana gaya min maganar banza ba, kasan cewa banda aure ƙaddara ce amma nafi ƙarfinka wlh, dana san haka kake da fuska biyu mai zai sa na aureka, kuma wlh aiki yanzu na fara fita inda naga dama yanzu na fara, baka isa ka ja mini layi akan abinda naso ba, ai ba baiwa ka auro ba da zaka juyani son ranka ba...

Wani zabura Hamid yayi ya nufeta cikin ɓacin rai, tana ganin haka ta ruga ɗaki ko kafin ta kai ya cimmata ya figota ya kifa mata kyakkyawar mari tare da ya shaƙo wuyan hijab ɗinta yana zaro mata ido cike da tsantsar ɓacin rai.

Zan nuna miki nike aurenki ba ke kike aure na ba, ki kuskura ki ƙara fita bada izini na ba zan nuna miki cikakken asalina wlh, ƙazamar banza kawai.

Ya ƙare maganar yana sakinta tare da tureta har ta kusa faɗi, ba ƙaramin tsoratata yayi ba, hakan yasa bata iya furta komai ba dan ga dukkan alamu in ta kuma wata magana zata sha dukan banza ne, sai dai tayi aniyar sai ta rama marin da yayi mata koda bata kai hannunta jikinsa ba zata muzguna masa da abinda zai fanshe mata haushinta, tayi ƙofa ta shiga ɗaki, shi kuma tsaki yaja ya koma cushing yaje ya zauna yana mayar da numfashi, sosai ransa ya ɓaci har baya iya controlling kansa, dan da ya biye zuciyarsa dukan tsiya zai yi mata yadai raga mata ne ganin macece ba namiji ba abokin yinsa, amma yana jin dole ya kawo ƙarshen rashin kunyarta dan bazai taɓa ɗauka ba, ko Sakina ba rashin kunya take yi masa ba amma baya ɗaukar rashin kirkinta, dole ne sai ya nuna mata shi ɗin tsayayyen namiji ne a gidansa, daga ƙarshe miƙewa yayi ya bar gidan gabaɗaya bai kuma dawo ba sai wajen sha ɗaya na dare. Ɗakinsa ya shiga t'ya kulle yayi wanka ya shirya ya kwanta dama tun a waje yaci abincinsa, sai dai barci yaƙi ziyartar idanunsa saboda tarin damuwar da yake ciki, Sakina ta tafi taƙi dawowa ga Madina tana shuka masa iskancin data ga dama, haka ya raba dare idonsa biyu, hakan yasa ya sauko daga kan gado ya shiga toilet yayi alwala ya fito ya fara gabatar da Nafila, sai da yayi raka'a shida kafin ya zauna yayi lazumi da addu'a mai tsawo kafin ya miƙe ya hau gado, sosai ya samu natsuwa a zuciyarsa yaji kuma sanyi a ransa daga zafin abinda Madina tayi masa, shi kansa yaji daɗin Nafilar da yayi dan ya mance rabonsa da yayi shi, shima yasan yana da raunin ibada banda sallah biyar baya iya yin wata ibada, wannan nafilar da yayi ya tunatar dashi Allah ya kuma dace ya farga ta ƙara kusantar sa, wataƙila yadda ya bar Allah shiyasa yake ta jarabtarsa, da irin wannan tunanin barcin ya ɗauke shi.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 17, 2024 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

KAZAMAR AMARYA Completed Where stories live. Discover now