WANI GARIN.........

2.1K 76 8
                                    

🍚 *WANI GARIN............*🍚

_*HUMAIRAH BASHIR MELODY*_


              1
       *ABUJA*
    *MAITAMA SULE CLOSE*
Gari yayi sanyi saboda ruwa da aka tafka a cikin garin abuja kowa ka gani sanye yake da sweater da head hummer Unguwar maitama kasaitacciyar Unguwa ce wacce sai wane da wane ke zama acikin unguwan saboda yawanci Attajirai ne da mashahuren yan kasuwa ne ke zaune a unguwan, wani Gida nagani Kamar gidan turawa kana iya ganin duk abunda ke cikin gidan,
Wasu alhazawa nagani zaune cikin wani lambu Sai yara su uku dake wasa a tsakaninsu, Babbar ciki zatakai kimanin shekara Takwas a duniya sai mabi da ita zatayi bakwai a kiyasi sai na ukun Wanda yakasance namiji daka gansu kaga buzaye Saboda tsabar tsawon gashinsu koh ribbon ba'a bata lokaci ansa musu ba, daganin magidantan nan bakaramin tattaunawa suke
“Alhaji *LAWAL IBRAHIM YABO*  a gaskiya bak'aramin Aiki ka bani ba saboda irin wannan rikon sai imani Amma insha Allah zakuje lafya ku dawo lafya da izinin Allah” Amin sukace baki daya lokacin Alh Lawal ya mike yace
“Alh CHILE bari in shiga gida don dauko document din” 
Shigarsa keda wuya yafara kiran Sunan matarsa “HAJIYA AISHA!!!!?!” cikin sauri tafito
Lafya irin wannan kira?
“Kinsan munyi magana kan zanba Aminina amanar komai a hannunsa shine nakeso kidauko in bashi ”Hjy Aisha ta bata rai Haba Abban AMBIL mekake tunani dahar zaka aminche da Chile a matsayin Wanda zai rike maka duk wata dukiya? Meyasa kake hakane na gaya maka zamuyi tafiyan nan lafya mudawo lafya amma kaki yarda ka tuna duk abunda akasa Allah an gama komai
“Dakata hajiya Aisha banason irin wannan rong allegations din naki karki manta waye Chile tare mukazo Nigeria Neman kudi dud duniya babu Wanda na yarda na aminche da Idan ba Alhaji Chile ba don haka do as I said maza ki daukomun takaddunnan”.
Shiko Alhaji Chile yana waje yana kitsa irin gadar zaren daza'aywa Alhaji Ibrahim Ambil duk taji yadda akayi saita tashi ta kalli Alhaji Chile tace
“Kawu meyasa baka tsaron Allah so kake ka kashe Abbanmu?  Meyayi maka?” tuni ya rude ya matsa kusada ita yace “muddin kika sanarda wani kema saina kasheki” idanun Ambil yacika da kwalla ta wuce a tsorace taja kanninta,
Jiki ba kwari tashiga daukowa amma hankalinta da baseerarta bata Gareta saboda tunanin yadda duniya ta baci Da mucuta masu ha'Inci dacin dukiyar daba tasu ba, Hajiya Aisha saida ta bata kusan minti biyar daga sama zuwa kasa tafe take har Gaban Alhaji tace
“gashi Abban Ambil meye na bata rai?ai saikasa hankalina ya tashi fatana muyi tafiyannan lafya mudawo lafya”
“Amin” yace a takaice, da dariya ya fita ya mikawa Chile duk wani documents Ambil tana window tana kallo wasu hawayene suka Zubo mata tayi saurin sharewa saboda muryar umminsu dataji nan suka fito don tafiya Alhaji Chile saida yaga sun bace kannan yadaina daga musu hannu,
Sun kama hanyan sakoto ta Abuja kafin sukai kauyen Gama barayi suka taresu ambil na ganinsu tace
“Abba Ummi ku sauka ku gudu tunda basu ganku ba banaso narasa daya daga cikinku Munir, Monal kubi abba nida direba zamu karasa”
“Ambil ke mai tausayi ce akoda yaushe nasani amma kisani Tunran gini tun ran Zane Babu abunda yake riskan bawa saida Izinin ubangiji sannan mu musulmaine yarda da kaddara namune Kinji direba mukarasa” Hankalin ambil ya tashi suna isa Barayin suka fara kusakko kudi koranku, tuni su ambil dakowa dake cikin motar kirar Highlander sukayi kasa Abban Ambil yace
“kuyi hkr muna bisa hanyane guzuri kawai garemu kuyi hkr ga wannan” kudi ya ciro dami ya mika amma kawai Wani ya daukeshi da bindiga tuni Ambil tayi kan mahaifinta tana kuka saiji tayi ankara sauke wani tana juyawa taga umminta kwance ta mike tayi kanta haka suka daukesu duka sai Ambil data fara tabuwa sai 360 takeyi wani daga ciki yayi magana a hankali yace
“Oga itama mu dauketa kawai” tsawa yamai yace “Inason wannan yarinyar meyi tanada kyau kumuyi gaggawan daukanta mubar wajennan kar Asirinmu ya tonu” cik sukadau Ambil wacce take suma tana farfadowa saboda sanyin Rab'a, cikin mota suka shiga sunata tafiya har wani daji da akecewa Kurar Gamji bakowa yasanda wannan daji ba sai makiyaya dake makwaftaka dashi,  har bukka garesu dasuke hutawa kwanta da Ambil akayi wani me Suna gwame wanda shine oga yace
“meyi, Kura, Komai nama, Jajere, sameer yarinyarnan kamar baturiya inasonta sosai   zan rayu da ita har randa tazama Mace kannan ranar zan more rayuwana ranan zan san mace mai suna mace fareeda da babanta Sun gasani Bari kuji bantaba zina ba sannan bantaba son wata bayan fareeda ba sai wannan kusani wannan kaya nane ba nakuba kunisanceta”
       Dare ya tsala ambil ta farka taga duk bacci sukeyi ga aci balbal nataci ta mike tana ganin jiri ta miki hanya sai gudu takeyi tuni taji wani karfi tafara gudun ranta yunwa dukta Kau Ambil tayi gudun awa Biyar kafin gari ya waye, gaban wani gulbi ta fadi tana Haki....



Ina rokon Allah yabani ikon kammalawa. Amin

WANI GARIN YAFI GABAN KUNU....... Where stories live. Discover now