WANI GARIN.... 7

385 25 0
                                    

[9/4, 4:33 PM] Melody: 🍚 *WANI GARIN*🍚.....


*HUMAIRAH BASHIR MELODY*

           7

Kalleni Da kyau bude idonki wannan gidan nawane Da matata a ciki Koda wasa karki sake kice Ke matata ce kuma aunty Kasa aunty Sama Ki natsu kibar wannan haukar taki" Ambil tayi hamma tace     "Yoh Ni Ina ruwana dakai banda tsaigumi irin naka Ni muje yunwa nakeji".

Horn yayi cikin zumudi mai gadi ya bude Yana Washe baki  Arfat kuwa tuni tafito itada kanninta Yana fitowa tayi gudu ta rungumeshi tana shafa fuskarsa Ambil kuwa kasake tayi cikin mota tana kallon iya Shege sai kissing din king Arfat keyi tuni ta balle Mota tafito tace  "Malam kai wane irin Dan iskane agaban mutane kuyita Matse juna kai Amma yan birni lalatattu ne".

Kowa kasake yayi ana kallon ambil wacce tayi mutsu mutsu Duk ta yamutse Kamar wata TSUMMA, Arfat ta yamutsa fuska tace  "Mylove wacece wannan?  Daga Ina wani wari ne ya doki hancinsu Da gudu kannin Arfat suka shige ciki. Ambil tace Nifa yunwa nakeji kasan yadda zakayi dani fura zansha Da nono Koh ana samu a birni oho.

Look Arfat Kinsan mezai faru muje Daga ciki kira lami tazo ta shiga da ita ciki sasanta muje ciki I will explain to you Haka Arfat Da king suka shige Ai ambil taci gudu ta damiki King tace "Wato Ni naxama banza Toh kasani Ni amana ce a gareka kasani" wani wari ambil keyi maisa amai king Ya kwalawa lami kira da gudu tafito king yace  "Shiga Da wannan yarinyar Ki hada mata Ruwa tayi wanka Pls kisama mata kaya Koh a cikin nakine saiki bata abinchi karki manta kibata brush ta goge hakura.

Lami tace Toh Haka taja Ambil itakoh ambil sai turjewa takeyi.

King saida yatube kaya yayi wanka ya sake kaya tuni an gama Girki yaci kannan Ya dauki Arfat sai daki yafara kissing dinta tuni ta tashi tace "Tell me inaka Shiga Daga Ina kasamu wannan raunikan Sannan waccen yar Kauyen Daga Ina kasamota? King yayi shuru daga bisani yace "tsawon lokacin dana diba akan hanyata ta zuwa NIGER a birnin gwari na dauki wasu Ashe barayine suka amshemun komai nawa sukajimun raunika shine mahaifin wannan yarinyar Ya taimakeni shine takaitaccen labarin daxan Baka yanzu tashi zakayi muje wajen hajiya data shiga halin Ni aysu.

Sunje gidan hajiya dake Tundun wada bakaramin murna tayi ba ganin dsnta yadda yasanar Da Arfat hk yasanarda hajiya tayi murna Sannan tayi mishi Adua.

Sun koma cikin dare Misalin karfe takwas ambil ta hanasu sakat Dukta watsa taro a waje suka taradda Lami mai aiki Da kannin Arfat Da ambil cikeda mamaki king yafito yace "lafya naganku waje?" lami tace wannan yarinyar ce tace taga maciji Yana yawo shine muka fito waje.

King Ya dafe kai yace "inhar kuka biyewa wannan hamagon kundinga wahala kenan dakuke ganinta Tabin kwakwalwa gareta".
Mai gadine Ya bude gate yashiga suma suka shiga Arfat cikin dare ta tada balli Ai baxata taba iya zamada mahaukaciya ba bazai taba yuwuba.

Babu irin hkrn da king baiba Arfat ba Amma Ina Sai wani firga takeyi itafah saidai Yasan yadda Zaiyi da ambil basuyi Kwanan dadi ba gashi an dade baa haduba.

Washe gari safiyar asabar king Ya Shirya kanninsa Da Arfat sai gida Ya maidasu zuwa yamma suka Dawo gida, Mai aiki itake dawainiya Da ambil inda taci abinchi nan take amai kashi kuwa a kasa takeyi saboda tsabar gidadanci.
[9/5, 12:54 PM] Melody: 🍚 *WANI GARIN*🍚.....


*HUMAIRAH BASHIR MELODY*

           8

Suna sauka Arfat tayi daki shiko yayi inda ambil yana shiga dskin wani wari Ya doki hancinsa tuni ya toshe yakira Lami ya hauta Da fada
"inace kenaba kidinga Lura da ita Amma kika Barta hk Toh kisani nakusa sallamarki Koh wanka bakiyi mata Toh kisani akan Ambil bake ba Wallahi Har Arfat Zan iya shata muku Layi matsawar bazaku gyrata taxama Mutum ba jibeta yadda take bacci dubi daki ambil tsnajin magana ba kurma bace Duk yadda kika koya mata abu Wallahi saita dauka don tanada baseerah ba irinki bace kisani maza ki gyra dakinnan afesa turare anjima zamu HUMAIRAH fashion wears musiyo mata kaya wanka Sau uku a rana wanke kai kuwa Duk sati Da kitso abinchi abaki zaki bata Sannan kidinga lallashinta".

Fuuuuuu!!!!!!
Ya fice yabar lami tsaye tace Toh aiki yasamu gwari daman Haka king yakeda masifa Meye halak'arsa Da ambil saina tambaya Tunda Har tana neman fin matsayin matarsa.

Tashin ambil tayi ta cire mata kaya tashiga Da ita bayi tayi mata wanka takaita dakinta, tadawo ta gyra daki Sannan ta Shirya ta Sai wajen wanke kai  suna dawowa king yayi bacci Ya hantse sai Humairah fashion wears inda aka siyawa ambil kaya itakoh ranan Kamar ansa mata kwado Da mukulli a baki.

Kaya Harda Arfat aka siyawa dukdai Ya kwatanta adalci tsakaninsu Tunda Duk nauyi a kansa ne, Bayan sun Dawo gida Arfat takasa gane ambil taga Sai wani shining takeyi tana walkiya tuni wani haushi ya Kamata ta dakawa Ambil tsawa "Ke ubanme yakawoki inda nake maxa Bacemun Da gani kinyi Da wani gashi kamar wata yar bararoji".

Ran king Ya baci yarasa yadda Zaiyi yace Ambil maxa Ki kwashe kayannan lami kuje Sai anjima Ki kula sosai Da aikin dana baki, Toh tace ambil kuwa takasa cewa komai Ruwa ya daki babban Zakara Ashe zaxxabi ne mai mugun zafi Ya damketa Bayan tafiyansu ambil tafara mimmikewa idanunta suna kakkafewa Da gudu lami ta fita domin kiran king cewa take "Alhaji Ambil ba Lafya zata mutu firgita yayi Ya ture Arfat Yasa doguwar Riga zai fita Arfat tace "Dakata muddin kafita Don wannan yarinyar Toh kasani aure dani dakai babu Don banga dalilin dazaisa muna tsaka Da jin dadi zata tsinke mana ba".

Idanun king suka cika Da kwalla Ya tsani ambil Amma tazame mishi dole *Karike ambil amana kai kadai zaka iya tarbiyantar Da ambil Sannan kaine hasken idanunta saboda ambil marainiya ce* maganganun malam sani marikin ambil ne yadawo mishi ya juyo yace
"Ambil amana ce a gareni kiyi hkr inceci rayuwarta batada kowa anan garin saini Pls Arfat do me a favour just to save the innocent soul".

Jikin Arfat yayi sanyi tace  "Naji my king ALLAH yabata Lafya Amma kasani banajin son wannan yarinyar Koh kadan  acikin raina kuma lokaci yakusa rabamu Da ita saboda tun zuwanta  muka Kasa samun kwanciyan hankalina".
Waje yayi Yana isa yaga ambil bata motsi daukanta yayi cik sai Mota Yayi horn aka bude mishi Sai *SICKBAY KONGO* yakaita emergency aka karbeta doctor Aurtu shine akan duty nurses sun zagayeta atake Saida ambil tasha allurai guda biyar Sannan akasa mata drip karamar Roba Amma Har yanzu bata motsi illah Harbin zuciyarta dakake iya gani.

WANI GARIN YAFI GABAN KUNU....... Where stories live. Discover now