WANI GARIN....... 3

497 21 0
                                    

🍚 *WANI GARIN*🍚.....


*HUMAIRAH BASHIR MELODY*


3
Haka duduwa tafara yimata fura Da nono tana kaiwa kasuwar RUNHU ranar farko ambil ta siyar duka murna wajen ambil Baya nisaltuwa gata da kazanta Amma kowa kayanta yake rubibi har takai idan ta siyar saita taya amatu siyarda nata a takaice basa kwantai.

Wata ranar jumaa ne da dare ambil taje dandali don kallon masu rawa da gad'a kowa taci kwaliiya nagani na fade kowacce da saurayinta Sai wani yauki sukeyi ambil kuwa ta tsaya gefe saboda kowa gudunta yakeyi dayawa shegantata sukeyi anfara wasa ana kalangu ana rawa amatu kuwa Chan tsakiya na hangeta tanata rawa Abun Yaba ambil shaawa kwarai saiga wasu yan mata sunzo wucewa daya ta bige ambil Saboda tsabar tsokana, Sai wata ta juyo tace kinada magana ne?
Ambil tayi karaf tace "Inada Duk Wanda yace a zauna Lafya Nace yashi ubansa" tuni sukayi kanta suna duka akace Sarkin Yawa yafi Sarkin karfi Amma anan Sai naga maganar ta sauya kukan kura ambil tayi ta watsar dasu duka ta suka fadi tace "fulani kunya garemu ba tsoro ba Duk wacce takeji da rashin kunya tashigo Ni Menayi muku banda shiga harkar daba takuba badonku naxo nanba Don Amatu naxo".

Kamar ance amatu ta juyo taga kawarta Sai wuci take tayi tsalle tafito tazo wajen tayi tafi tace "me akeyi ubanme tayi muku kuka tsareta Koh sharrin da aka Saba zaayi mata Toh mafashi ya raina Allah daya halicceshi" Ai tuni sukayi shuru suka Fara wooooohhhhuu mundai San asali yar tsintuwa Ambil idanunta suka fito waje daman ya lafiyar giwa juyawa tayi Sai gudu takeyi har takai gida cikin Dan bukkansu ta fada ta kwanta kan duduwa tace
"baba meyasa akecemun yar tsintuwa bayan inada iyaye meyasa akemun kallon Mara tushe bare madafa? Baba meyasa Idan naje dandali naxama kamar mujiya?"

Kukane yaci karfinta duduwa ta kama hannunta tace Har zuwa yau kinki sanar dani inda iyayenki suke kullun saidai kice baki saniba Toh kisani rashin fade shine yakawo haka dole duniya ta shegantaki.

Inna na rufe baki saiga Amatul-jabbar tace "kwarai kuwa baba Ambil taki sanar dani komai gameda rayuwarta nima a duhu nake".

Hmmm....... Kawai ambil tace batareda ta Kara yimusu wani zance ba,
Haka suka kwantar mata da hankali harta Saki jiki amma taci alwashi saita jimasu jimmala Da ixinin Allah.

Amatul-jabbar niba shegiya bace inada iyaye, babana hamshakin mai arziki ne kuma dan kasuwa mahaifiyata bata aiki mun tashi cikin gata dajin dadi bamu taba nema mun rasa ba mutuwa itace tayimun shigar sauri kuma abokin mahaifina shine sila kuma naci alwashin zama kwararriyar lauya saboda in kwatowa kaina yanci koba jima koba dade yan fashi ne suka kashemun mahaifina,mahaifiyata,kannina biyu da direba Nima Allah ne ya kubutar dani inajin nice Zanyi fito na fito da azzalumin mutuminnan, bana fata Allah Ya kasheshi bancika burina ba tabbas zaisan cewa *WANI GARIN YAFI GABAN KUNU SAIDAI TUWON GABZA".

AMATUL-JABBAR tayi ajiyar zuciya Tana kallon Ambil tayi matukar bata tausayi Amma tambayan datakeyiwa kanta meyasa ambil taki kuka bare kwalla, Ambil Allah yayi mata baiwa na karantar halayyar Dan Adam, Ta Kalli amatu tace "Bana kuka idanna tuna iyayena saboda sun mutu basuda hakkin kowa sun mutu batareda dakon zunubi ba Masu kisan su aka daurawa Duk wani laifi kuma nasan iyayena yan aljanna ne Saboda sun mutu a hanyar zuwa zumunchi, nida kike ganina amatu bansan dangin iyayena ba Ke zuwa yanzu na mance wai iyayena yan inane.

Amatu tayi tsuru don Da itace Aida tuni ta dade Da mutuwa, Saboda gani take babu wanda yakaita son iyayenta,
"Ambil taya zaki zama Lauya a wanga kauye? Dakoh primary bamuda bare islamiyya kina gani Koh allo babu Sai kinje birni? Taya kike ganin wannan buri naki zai cika muna tafe da rashin sani muna cikin duhu na jahilci?

WANI GARIN YAFI GABAN KUNU....... Where stories live. Discover now