WANI GARIN...... 2

632 24 1
                                    

🍚 *WANI GARIN*🍚......

*HUMAIRAH BASHIR MELODY*


              2
Duk Ilahirin jikinta a gajiye kanta ne waje sauran gangan jikinta nacikin rafin Zanyi Ya debeta Sai bacci Kaman a mafarki taji ana binta Ai cikin daji tamike tayita gudu kaman ranta zai fita, ga kayoyi Duk Sun chaketa kafarta Sai zuban jini yakeyi nidai Humairah ambil tabani tausayi kwance tayi a kasa sumamma bata Koh numfashi.
       Meyi, sameer, jajere, kura, komai nama maza ku tashi wanaba ajiyan wannan yarinyar? Meye yayi rau da ido yace "oga nikaba" yanzu Ina take? Nace ina take? Mesuna gwame wanda shine oga ya shakeshi ai tuni idanunsa suka fito "Meyi Ka cuceni kasani Cikin kunci kayimun wulakanci Ka kasheni yakakeso Inyi da rayuwana yanzu bakada amfani"
Bindiga Ya dauko yaba jajere yace
"maxa Ka daukemun wannan mara amfanin" jajere ya amsa jiki na rawa ta dauke meyi tareda runtsa ido Saboda wani irin ciwo dayake ji a zuciyanshi, yana fadi sukabar wajen sukabar gawansa kwance babu maceci Sai Allah.
     Ambil Dai har zuwa wannan lokacin batasan me duniya take cikiba wani makiyayine dake kiwo yashigo daji neman abincin dabbobi kwatsam zai wuce yaga Yarinya kwance salati yayi Ya gaida ubangijinshi cikin yaren fillanci yace
“lafya Yarinya a daji?  Mutum Koh aljan? ” tambayoyin dayakeyiwa kansa kenan kusa Da ita ya matso ya tabata yaji tabbas Mutum ce kuma tana matukar bukatan taimakoh kawai Ya sab'ata a wuya yana gudu Kaman ransa Zai fita.
*KAUYEN RUNHU*
wani babban garine mai cikeda albarka garine Mai tarin niima irinna kiwo Da shuka Koh Ina ganye yayi shar saidai wasu dabbobin ba kowani ciyawa sukeciba shiyasa Malam Sani yakezuwa jeji Don samowa dabbobin sa abinchi, Cikin rugarsu yashiga Yana mai kwalawa matarsa Kira Mai suna duduwa, daga nesa naji ta amsa tafito a guje jin kira mai bada tsoro da tada hankali,
"malam wannan kira ai she Kasa inshi tuntube" Da hausarta irinta Fulani, tsayawa tayi cik ganin yarinya a kwance sharbam bata motsi, Malam Ina ka samo yaro?
"Duduwa duk kibar Magana kije kidebo kindirmo da dauri taimakonki kawai take nema" cikin sauri ta tashi ta debo magunguna ta watsa mata wani Ruwa a fuska kawai sai ambil ta tashi tana kiran monal Ummi Abba shuru tayi ganin malam sani Da duduwa zaune kallonsu takeyi Kallo irinna rashin Sani kindirmo aka mika mata ta wawuri kwaryar Tana kafa kai ta burtsoshi tace "babu sugar bazan iya sha ba" duduwa ta kalleta tace "yaro bamuda sikari sai ranan kasuwa Koh na goma babu saina ashirin kayi hakuri yaro kasha haka" ambil ta amsa tasha dayake akwaita da wayo ta shanye tas sannan takora magunguna sannan akayi tuwon K'asa aka fara cire mata kayoyi, Sai ihu takeyi ana gamawa duduwa takaita bayi  tayi mata wanka suka gashi babu kaya haka duduwa ta burma mata rigarta ambil mezatayi Sai bacci abunka da yaro.
      Saida ta kwanta kannan malam yafara bata lbari yadda akayi ya tsinci ambil, duduwa tayi murna kwarai dasamun diya kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa shima malam yayi murna Saboda Duk yayansu wabi sukeyi haihuwan duduwa goma Amma babu Koh daya daga cikinsu wanda Ke numfashi duduwa tayi kuka Har taji babu dadi,  Kwanan ambil daya Amman kusan Duk yan rugar sunsanda zuwan ambil sai zuwa Akeyi kallonta itakoh she feels ashamed saitayita rufe fuskanta, wajen cima bakaramin artabu akeyi da ambil ba Duk abunda bazai yuwuba shi take fade takeso Sai suyita bata hakuri itakoh kuka shita maida sanaa.
Asha shafe wata daya ambil ta kode saboda sauyin yanayi fuskannan tayi baki kirin hakora jajaye babu Koh sha'awa man shanu shiya zame mata mai na kai dana jiki Abun gwanin ban kyama gashi Duk fadin garin babu wacce takaita kazanta, ambil dai tayi kawa mai suna Amatul-jabbar itama haifaffiyar Kauyen runhu ce sun Saba amma amatu tafi ambil shekaru Don har saida fura Da nono takeyi, Ambil ta matsa itama Sai tayi tallah.

WANI GARIN YAFI GABAN KUNU....... Where stories live. Discover now