WANI GARIN....... 4

443 28 0
                                    

🍚 *WANI GARIN*🍚.....


*HUMAIRAH BASHIR MELODY*

*Allah ya kawomu Lokaci Ya kawomu Sallah Ina mika gaisuwana zuwaga yan'uwa Da abokan arzuka dake fadin DUNIYA kamar, NIGERIA, NIGER, LONDON, CHINA, MALAYSIA, DUBAI, SAUDI, FATAN KUNYI SALLAH CIKIN KOSHIN LAFYA ALLAH YA MAIMAITA MANA AMIN TSUMMA AMIN.*





              4

"Amatul-jabbar Allah babu yadda baya ikonsa" hakane kawata.
Duk zance su amatu duduwa tagama ji tsaf taji tausayin ambil taji sonta yashigeta
"yau shekara biyu Amma Ambil bata taba sanar damu komaiba Sai yau? Yauma amatu take gayawa?  Allah yayi mata baseera kwarai Allah yayi mata baiwa yarinya karama yar shekara goma tana tunanin daukan fansa? Allah ya cika miki burinki Ambil Allah ya kawo sauyi na alkhairi a rayuwarki ".

Irin wannan aduan itace Ke kawo sauyi a rayuwar Ambil gashi duduwa ta riketa hannu biyu duduwa dai bawata tsohuwa bace Don bata wuci shekara talatin Da biyar ba.

Sule yadda nakeson Ambil ta gidan malam sani Abun baa cewa komai bana iya bacci Idan bansata a idanuna ba, "Amma musuba kai wawane kazama irin ambil mezakaci Da ita dubi yadda haule take jidalin sonka Amma kake shareta karshema Ambil ta watsa maka Kasa a ido kaika Sani" karaf Sai a kunnen ambil tace tabbas Sai tayi maganin Sule daman ya tsaneshi Wallahi.

Ambil tana komawa gida taga malam zaune yayi tagumi sun tasa Mutum a gaba Baya motsi Sai    fitar numfashi, ta zauna turus ta ajiye nikan datakai bakin kasuwar runhu, tace "baba duduwa waye wannan daga Ina yake? Meya sameshi? Ambil ta rude sosai ganin Mutum kwance.

Sun kasa bata amsa illah Iya kokarinsu da sukeyi na ganin yasamu Lafya dun Susan daga inda yake Sannan suji abunda Ya sameshi,   Don ga motarsa chan gidan mai unguwa an janyota an rufe da tampol.

Magani kawai ake mishi wasa wasa saida yayi sati daya.

ambil ce taje bukkan da aka saukeshi taje tayi mishi gashin jiki kawai ganin Mutum tayi zaune ta zare ido zata gudu yayi saurin cewa "yarinya dakata zoki sanar dani nan inane? Menakeyi anan a Iya sanina zani Zaria ne kuma Daga Niger state na taho" Ambil tace
Bari inkira baba Da baba duduwa sukadai zasu iya baka wannan amsan.

Baba duduwa!!!!! Kira hudu tayi mata ta Amsa tace
"bako Ya tashi kizo yanayimum wani tambaya bansan me zance dashi ba".

Sauri sukeyi har sukakai baba duduwa tace
"sannu yaro Ya jiki kuma? Jiki yayi kyau me sunan malamin?"
Shidai kansa Ya kwance yace
"ku sanar dani nan inane?  Dan Allah" yaro nan Kauyen runhu ne cikin wani gari ana cemishi *Bakan* mu makiyaya ne da dabbobin mu gaba daya ta sanar dashi abunda yafaru yayi musu godiya sosai Ya gode musu yasanar dasu cewa sunansa *King* duka suka Kalli juna harda ambil data mance meye boko suka hada baki sukace basu ganeba yace "Sunana *Sarki* gaba daya suka washe baki "Au sarki kake nufi yace "eh".

Nan ma malam yadawo ya K'ara yimishi godiya akaci gaba dayi masa Magani, King Ya tsani ambil Saboda kazanta Don har wani wari takeyi gashi itake kawo mishi abinchi dole kesawa yakeci saboda Karya kwana Ya Yini baici ba, wata safiya Ambil ta fito zata kai mishi abinchi yakirata Tunda ta doso Ya toshe hanci yana cewa Idan kika ajiye kizo, Ambil Sarkin k'uluwa hartaji haushi Allah Allah takeyi tadawo, tana ajiyewa tadawo ta tokare tace "Gani"
Yace "yauwa wai Ke me sunanki kuma meyasa bakison Yin wanka dubakki Kamar wata jaka Ke bakijin kunya? Dubi yan matan garinnan fes dasu keko kamar wata daddawa look Koh brush bakiyi da Abun goge baki dakinyi Magana Kamar masai".

Ambil ta kulu tarasa me zatace ta watso mishi uwar harara tace
"Banyin wanka kaji Idan matsalanka ne mezai Hana Ka kamani kamun, wari kuma kaikeji nibanji kuma wanka Sai ranan kasuwa mukeyi nida Amatu kwaskwarima mukeyi brush kuma yanzu Zanyi" ta tsugunnan tana dagowa ta watsa mishi miyan bakinta ta gudu tayi nesa dashi tace "Daga yau Idan kaga abu kadinga shuru daga bakunta? Sai Mutum Ya bige da shegen zuba kamar magarya Ka kuma".

#SHARE VOTE AND COMMENT......

WANI GARIN YAFI GABAN KUNU....... Where stories live. Discover now