MIEMIEBEE👄 A WANKI GARORI
🌹By Sad-Nas🌹®REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
DARASIN MU
ADDU'AN DA AKEYINSA BAYAN KINYI TAHIYA KAFIN KIYI SALLAMA:
Allahumma inni zalamtu nafsi zulman khasiran,wala yagfirul zunuba illa ant,fagfirlli magfiratan min indika warhamni,innaka antal gafurur rahim.
Addu'ace mai kyau 'yar'uwa daure ki hadda ceshi kina yi bayan kin idar da sallah kinyi tahiya sai kiyishi kafin kiyi sallama.10
Miemie ta fara bawa Mama labari kamar haka "Mama kin tuna lokacin da Jidda ta gayyacemu biki har mukayi anko mu hud'u?" Mama tace "Eh" Miemie taci gaba da cewa "Bayan an gama bikin muna tsaye daga gefe sai naga wata sister'n k'awata naje muka gaisa ina dawowa inda su Jidda suke daga gefe dama akwai motoci sai naji ammin sallama hakan yasa na tsaya muka gaisa yana zaune daga cikin motarsa yace gaskiya na burgesa ya sunana,bayan na gaya masane yace shi kuwa sunansa Zayyad Abbakar shine d'an gidan Alhaji Abbakar gaskiya haka kawai yaji cewa ya kirani mu gaisa idan ba matsala na bashi no wayata,ba musu na bashi,ya gayamin cewa wlh sona yake har zuciyarsa nadai masa godiya na tafi,bayan tafiyata wani ya kira Meela lokacin data jene sai taji shi Zayyad d'in yana gayawa abokinsa cewa wlh yaga wata yarinya sunanta Miemie kuma yana sonta sai dai ta masa k'arama dewa k'aramar yarinyace sosai,Bayan Meela ta dawone take gayamin ni kuma abin ya b'ata min rai kamar ni ace min wai k'aramar yarinya? Kuma lokacin shekaruna goma sha shida nefa zai wani cemin k'arama,shine daya kirani a waya nace masa karka sake kirana tunda raina min wayo kayi,yayita bani hak'uri dan in fahimci manufarsa amma sam nak'i nace masa idan yana k'aunar Allah ya fita harkata karya sake kirana,shikenan kuwa yace min to shikenan yaji amma dan Allah inyi hak'uri kar nayi fushi dashi ban sake ce masa komai ba na k'atse wayar na goge number'n sa shima kuma bai sake kiranaba sai ranan danaga ana nuna bikinsu a TV ne na sake tabbatarwa ashe da gaskene shi d'an gidan Alhaji Abbakar d'inne."
Dariya Mama tayi tace "Kedai kina da wauta wlh,to aiba k'arya ya miki ba shekara sha shida kam ai yarinya kike" zunb'uro baki tayi tace "Haba Mama harda kema kike cewa haka,ni na tsani mutum ya raina min wayo wlh dan shi d'an gidan wanine saiya raina ni? Ai shima daga k'aramin ya zamo babban" ta kalli Mamanta tace "Gaskiya Mama nidai bana so,abokin Yaya Mahmud zanso"
"Kunji min shirme ko,aiga yaranta kam a fili kina gwadawa mutumin da ko ganinsa baki tab'a yiba taya zaki so shi?" Murmushi tayi tace "Nidai Mama dan Allah kicewa Baba inada wanda nake so shine abokin Ya Mahmud mai suna Aliyu" tana kaiwa nan ta d'auki wayar Mamanta da Sani kirta ne keta kira, yace da ita zaizo anjuma tace saiya zo sannan ta katse wayar tace "Hmm k'ila wayan zai kawo min ko mai tochi ce oho." Mama dai binta da kallo kawai takeyi.Ammar ne zaune da friends nashi suna hira inda kowanne yake burin daya fara aiki sai aure "Kai kuma fa Ammar kayi shuru?" Murmushi yayi yace "Ni ai nabarwa Daddy zab'i na,shi kad'ai nake jira ko yanzu ya kawo matar zanyi aure" nan dai sukaga da gaske yake "Haba kai kuwa sai kace a k'auye? Wlh a k'auyene ake irin haka" d'aya daga cikinsu yace "Kunfa san yadda Daddy yake ji da Ammar dan haka kawai muyi fatan Allah yasa ta gari ce ya sanya alkhairi" duk suka amsa da "Ameen" Ammar dai koda sukace haka babu abinda ya fad'o masa arai sai wannan yarinyar daya gani a hospital ita ce kawai ta fad'o masa ko menene dalili oho. Mik'ewa yayi ya musu sallama sannan ya shige motarsa sai gida,a parlour ya samu Zayyad yana shirin fita "Ango to be ina ka fito haka?" Murmushi kawai Ammar yayi yace "Gurin aiki,fita zakayi?" Zayyad yace "Eh zamuje anguwane da Aunty'n ka" tab'e fuska Ammar yayi tare da cire suite d'in jikinsa ya rik'e a hannu "Sai kun dawo ni zanje na kwanta" harya wuce sai Zayyad ya bishi da kallo yasan kawai Ammar yana da damuwa a cikin ransa yace "Idan na dawo zamuyi magana" Ammar daga nesa yace dashi "Ok" sannan ya wuce d'akinsa.
Bayan sallan magrib Sani yazo hira gurin Miemie suna tsaye daga k'ofar gidansu,yanata surutai ita dai tama gaji da Sanin nan gaba d'aya neman hanyar da zasu rabu takeyi amma ta rasa. Can dai yana hira tana d'an bashi amsa sama-sama kawai sai taji Sani ya sake tusan dashi kansa bai san zai fito ba kuma tusa mai k'ara dan shi kansa ya tabbata taji,ba ita kad'ai bama har masu wucewa daga gefensu sunji,dan fashewa da dariya sukayi suna cewa "Lallai kam ana hira anan,kina jin wani irin tusa daya fito daga gunsu?" D'ayar tace "Eh naji mana ke kuwa ai tusan masoyane kinsan dama akwai tusan masoya sai suyita sakewa junansu kawai suna shan k'amshin juna." Daga Miemie har Sanin duk sunji abinda 'yan matan suke cewa dama shikam Sani tun da yayi tusan sai kunya ya kamashi sosai amma saiya magze yaci gaba dayin hiransa,ita kuwa Miemie haushi ya bata ba kad'an ba saida taji 'yanmatan nan sunyi magana shine dariya ya kamata sosai kuma babu yadda zatayi dariyan a zuciyarta dai cewa take "Wlh kun cuceni da zakuce wai muna tusan masoya,shi dai dayake bodarine ko d'ure-d'uren alale da wake yayi yau oho masa." Katse mata tunanin yayi da cewa "Kodai kin gaji ne Miemie?" Azuciyarta tace irin wannan tusa naka ba dole na gaji ba shashasha kawai,a fili kuwa cewa tayi "Wlh kuwa bacci nakeji" murmushi yayi ya d'an sosa k'eya dan kunya sannan yace "To shikenan sai da safe" haushinsa yazo wa Miemie har wuya gashi dama ta fito ne dan tana tunanin ko waya ya kawo mata sai taga babu alaman waya sai d'oyin tusansa daya barta dashi haka ta wuce gida da takaicin Sani tana shigowa ta wuce d'akin Mamanta ta ajiye gyalen a gefe tace "Wlh Mama nikam na sallami Sani kenan daga yau sosayyar tamu ta k'are" Mama tace "Saboda bai kawo miki wayanba ko?" Miemie tace "Wlh Mama tusa kawai ya dinga sake min wane bodari ko kunya ma baijiba wlh kuma saiya nok'e kamar bashi yayi ba" dariya sosai Mama takeyi harda d'an hawaye tace "Yanzu Miemie dan kin tsanesa shine harda masa sharri?" Miemie ma dariya takeyi tana magana "Wlh Mama ba sharri na masa ba,harfa wanda suke wucewa akan hanya sunji tusar har cewa suke wai tusan masoya mukeyi ni da shi" dariya Mama ta dinga yi sosai Miemie kuwa sai magana takeyi "Wlh Allah daga yau bazai sake gane mimba dama inata neman hanyar rabuwa dashi kuma na samu sunansa ma zan canja a wayarki daga Sanj kirta zuwa Sani bodari" haka sukaci gaba dayin dariya ita da Mamanta har suka gaji sannan ta koma d'akinta ta kwanta suna chartn da Meela ta whatsapp tana bata labarin itama dariyan emojis d'innan ta dinga turo mata bayan hakama ta had'a mata da audio tana cewa "Miemie amarya a gidan Sani bodari wlh kuna burgeni" Miemie tana jin audio'n ta dinga dariya a d'aki ta mayar mata da amsa "Bana son iskanci fa,ai dama na dad'e ina so in bashi red card kuma ya samu kenan yanzu,ni zan rufe datana sai mun had'u gobe a islamiyya ya Jidda fa? Har yanzu bata huce ba?"
Meela tace "Wlh bamu had'uba yau tun safe kallo nake a gida"
"Ba damuwa sai mun had'u goben"
"Ok bye" sannan Miemie ta rufe datanta saiga call d'in Alhaji Abdul ya shigo nan take ta d'auka suna gaisawa.Vote and comment pls

KAMU SEDANG MEMBACA
MIEMIE BEE A WANKI GARORI
FantasiLabarine k'irk'irarre na tabbata zai Ilmantar tare da nishad'antar daku,kuci gaba da biyoni karku bari a baku labari... LOVE YOU