MIEMIEBEE👄 A WANKI GARORI
🌹By Sad-Nas🌹®REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
Bansan me zance muku ba dan ya faranta muku raiba fans d'ina,amma dai kuyi hak'uri kumin afuwa please👏domin in sanyaya muku rai babu abinda zance muku sai dai ince muku duk wanda yake zaune a garin Maiduguri yaje ya nemi MIEMIEBEE👄 domin tayi muku make-up kyauta😍,kuna iya nemanta domin kwalliyan biki kona suna insha Allah,dan nima idan Auren Autan gidanmu ya tashi ita zamu gayyato tun daga Maiduri har Yola insha Allah😜
Kafin in mance wannan shafin nakune
Ayusher Moh'd
Seemby Luv
Murbash
Allah yabar zumunci ameen48
Ammar yayi murmushi yace "Hajiya albishirin ki?"
Tana murmushi tace "Yau kuma harda albishir? Me muka samu haka?"
"Kedai kice min goro"
Tayi 'yar dariya tace "Toh goro fari k'al"
"Koda yake bari dai in bari kuji daga gun Daddy zaifi"
Ammar ya kasa hak'ura yace "Hajiya D'an da Miemie ta haifa ba D'an Aliyu bane D'ana ne" ya k'arasa maganar da farin ciki.
Kaman a mafarki Hajiya Nana tace "Ban gane D'an ka bane? Ta yaya ya zama D'anka kuma Ammar?"
"Wlh da gaske nake gaya miki wannan maganan Sudeis D'ana ne wlh Hajiya,Baban Miemie'n zaizo gurin Daddy anjuma zakuji dukkan bayanin daga gare shi"
Ganin yanda Ammar yake cikin farin ciki yasa Hajiya Nana ma nuna mishi nata farin cikin a fili duk da dai acikin zuciyarta sak'e-sak'e kawai takeyi na rashin yarda sa hakan.
"Masha Allah indai maganar haka take to gaskiya na tayaka farin ciki Son,Allah ya tabbatar mana da alkhairin hakan"
"Ameen" suka amsa shi da Kamil sannan suka zauna yana kiran "Maryam"
Babu jimawa ta iso,nan ma yake sake gaya mata yadda akayi,Laila tana lab'e daga gurin slide door nata tana sauraran komai tare da rikicewa tana cewa "Kai da sake wannan zance k'arya ne wlh"
Maryam kuwa tunani ta shiga yi tana maganar zuci "Ta Allah ba taku ba Aunty laila da Yamal,duk da abin da kuka aikata gashi Allah ya nuna muku isharan sa,kuma saina tabbatar da cewa Daddy yaba Sudeis wannan kyautan da yayi niyan bawa jikan shi na farko"
Ammar ya katseta da cewa "Idan bazakiyi magana ko nuna farin cikin kiba kije kawai"
Hannunsa ta rik'o tana dariya "Haba Bro Ammar kaima kasan bama haka da kai,kasan wani farin cikin ba'a iya bayyanata a bayyane sai dai a cikin zuciya,na tayaka murna Bro,kuma ina sake tayaka murnan dawowar Aunty Miemie gidannan a matsayin Matar ka kuma Uwar yaranka,sannan ina sake tayaka murnan samun Sudeis,shine jikanmu na farko a cikin gidan nan,lallai wannan yaron zaiga gata,barima Daddy ya dawo in tuna mishi alk'awarin daya d'auka akan jikan shi na farko a duniyan nan!"
Tun da ta fara magana Ammar yake jin dad'i har cikin ranshi,murmushi ne kawai akan fuskar shi ya kasa dena yin ta,inda Kamil yake taya shi. Maryam ta d'aga murya taci gaba da cewa "Bro Ammar dolene gobe mu fita mu sake sabon sayayya wa Sudeis,babu abin da bazamu saya ba,kai dasu Mummy ma zamu fita insha Allah,sannan gobe zanje in duba lafiyar D'anmu Sudeis"
Yamal tun tana jiyo magana harta kasa hak'ura ta matso inda zata dinga jin komai,duk abin da Maryam take fad'a akunne su tas, jikin Laila yayi sanyi,ita kuwa Yamal katon cikin dake jikinta ta kalla tana tuna irin burin da tayi akan kyautan da Daddy zai ma abin cikin tan.
Wani hawaye mai zafine yake bin fuskarta wanda bata san sanda suka zubo ba. Ita kuwa Yamal cewa take "Taya za'ace Sudeis D'an Ammar ne bayan cikin Ammar ya zube? Wannan dai yaudara ce kawai da kwad'ayin abin hannun Ammar"Bayan sallan isha Mahaifin Miemie yaje gurin Alhaji Abbakar,dama dayake yasan da zuwan shi tunda Ammar ya sanar dashi. A harabar gidan aka shinfid'a mushi carpet na alfarma mai laushi kamar bargon duniyan kule,da kayan marmani da dai sauransu. Bayan sun gaisa ne Mahaifin Miemie ya mik'a mishi wannan wasihar Aliyu marigayin ya karanta shi tas,sannan ya sake mishi bayanin yadda akayi acan Azarei d'in,ya kuma cewa "Toh yanzu abu na k'arshe daya rage shine Shi Ammar d'in yayi gwajin DNA test tsakanin shi da Sudeis d'in,tunda ita Miemie tayi rantsuwa da Qur'ani mai girma akan d'an sa ne kuma ga takardun asibiti da binciken likita ya nuna,shiyasa nace zanzo da kaina dan wannan ba maganace da za'a yi aike akan shi ba"
Daddy ya sauke ajiyar zuciya yace "Wlh bakomai Alhaji tunda ga shaidu babu adadi,kuma tun ranan da Iyayen shi suka je barka suke ta mamakin yanda D'an yayi kama da Ammar d'in sosai,dan koda suka nuna min hoton Sudeis d'in ni kaina naga kamannin nasu harya b'aci wlh,amma da yake lokacin bamu san komai ba,kaga bamu isa muce D'an Ammar d'in bane,amma babu komai wlh mun yarda kuma mun amince,sai suje suyi gwaje gwajen Allah yayi mishi albarka,shi kuma Aliyu Allah ya jik'an shi"
"Ameen" cewar Mahaifin Miemie,sannan ya nuna jin dad'in shi sosai na yadda Daddy yayi na'am da maganan baiyi wani kokonto ba.
Bayan ya rakashi har gun mota ne da yake shi da Ya Mahmud suka zo,sannan sukayi sallama suka tafi shima Daddy ya shigo gida yake gayawa su Mummy yadda sukayi da Mahaifin Miemie,ya kuma nuna musu wannan wasihar kowa sai daya karanta har dasu Yamal iyayen gulma.
Daddy yace "Ammar sai kayi shirye-shirye akan gwajin da zakayi,kuma ya kamata a sake sabon sayayya amatsayin ka na Uba akai musu"
Hajiya Nana tace "Gaskiya kam haka ya kamata mune dai zamu shiga kasuwan,Ammar kam ai baisan me zai sayo ba"
Maryam tace "Mummy nima zan biku,yawwa Daddy alk'awarin dakayi akan jikanka na farko?"
Murmushi Daddy yayi yace "Ina sane Mamana,idan na yanke kyautan da zan mishi zan sanar daku"
"To Daddy" ta fad'a tana kallon Fatima suna dariya. Mummy dai farin ciki ne ya lullub'eta bata ce komai ba sai yanzu da tace "To yaushe kuma zaka dawo da Miemie'n?"
Ammar yace "Mummy wlh itace take k'i,har yanzu ta kasa mancewa da abin da ya faru a baya"
Hajiya Nana tace "To ai yanzu sai tayi hak'uri kodan albarkacin D'an da yake tsakanin ku,ai kaddara ce haka Allah ya tsara saiya faru"
Haka dai sukaita hira cikin raha sannan aka watse.Washe gari sayayya sosai suka yiwa Sudeis da kuma ita Miemie'n,bayan sun gama sun koma gida ne sai aka shirya tafiya da Zainab matar zayyad da Hajiya Nana da Nabila sai kuma Maryam,Nabil shine ya kaisu da yamma bayan sallan la'asar.
Jin tsayuwar mota yasa Miemie tayi tunanin ko Ammar ne yazo ganin Sudeis,sallaman Maryam taji sai ga su Hajiya Nana sunata shigowa da akwatuna masu kyan gaske.
Daga miemie'n har Mama suka mik'e suna musu sannu da zuwa tare da isar dasu parlour'n Mama suka zauna.
Bayan an kawo musu ruwa ne suka zauna suka gaisa dukkansu,Maryam ta d'auko Sudeis daga kan gadon Mama yanata bacci abinshi tazo ta zauna dashi.
Hajiya Nana tace "Sai kin tashe shi kafin kiji dad'i ko?"
"Mummy rik'e shi fa kawai zanyi,ai bazan tashe shi ba"
Maman Miemie tace "Kinsan jarirai da farin jini,bare taga babu a gidan su ai dole"
Aka d'anyi dariya Hajiya Nana tace "Fitina dai kawai irin na Maryam shiyasa ta damu akan zata biyomu ai"
Ita dai Maryam dariya kawai takeyi tana ta kallon Sudeis tare da d'aukan shi a hoto.
Nabila tace "Ai kuwa zata tashe shi kam da d'auke-d'auken hoton da take mishi" Maryam ta kalli Nabila tace "Kema haka zan hana naki bacci ai idan kika haihu" kunya sosai Nabila taji dan Hajiya nana da take gurin.
Hajiya tayi magana ita da Mama na fahintan juna,ta kuma nuna farin cikinsu na fitowar gaskiyar al'amari akan Sudeis,hakan ya musu dad'i sosai kuma sun gamsu sun aminta "Hakanne ma yasa muka yiyo musu wannan sayayyan a matsayin mu na iyayen Sudeis".
Godiya sosai Mama da Miemie sukayi sannan Maryam tace "Aunty Miemie muje d'akin ki in baki sak'on Fatima"
Batare da tace komai ba ta mik'e suka fita zuwa d'akin ta.
Suna zama Miemie tace "Yawwa Maryam da gaskene wai Ammar zai karb'i Sudeis?"
Maryam ta tuna da Abin da Ammar ya fad'a mata tace "Eh haka ya fad'a amma ai yace sai kin yaye shi"
Hankalin Miemie in yayi dubu sai daya tashi wanda ita Maryam d'inma ta lura da hakan. "Ya naga kin damu? Inda nice ke sai in yadda cewa zan dawo gareshi kinga ai shikenan kina tare da Sudeis,Aunty Miemie wlh Bro Ammar yana k'aunar ki sosai kema kinsan hakan,ki dawo ku zauna tare please?"
"Hmmm kedai gaya min sak'on Fatima"
"Toh nima maganar nauyi take min a baki gaskiya bansan ta yadda zan fara gaya miki ba"
Murmushi Miemie tayi tace "Dan Allah ki gaya min"
Maryam tayi ajiyar zuciya tace "Wai ita wlh son Yayanki take yi"
Mamaki sosai ya bayyana a fuskar Miemie tama kasa magana sai dariya da takeyi.
Maryam tayi dariya tace "Wlh da gaske take yi,shiyasa ma yau bata biyo mu ba wai dan tana jin kunyan Mama"
Miemie tace "Wai Ya Mahmud kike nufi?"
Maryam tace "Eh shi,wlh tana son shi sosai,please Miemie ki taimaki Sister na,ina farin ciki da abinda zuciyar ta yake so,kuma bani kad'ai ba kinsan itace Auta a gidan mu dan haka muna son farin cikin ta inhar zai yuwu?"
"Wai Maryam kina nufin kowa yasan hakan a gidan ku?"
"A'a babu wanda ya sani daga Ni sai Ita,idan har abun zaiyu ne saimu fad'a a gida"
Miemie tayi ajiyar zuciya tace "Toh gaskiya dai Ya Mahmud an riga da an gama maganar auren shi da 'yar k'anwan Mamana wato Bilki,kinma santa ai tamin kawancen aure"
"Okay na gane ta,ashe dai yama fitar da Matar aure?"
"Eh gaskiya bashi ya fitar ba,itama Bilki itace take sonshi saita gayawa Maman ta,shine akayi magana akan za'a had'a su kuma har ansa rana ma"
"Toba damuwa,inaga kawai mubar maganan anan"
"A'a zan gaya mishi karki damu"
"Aunty Miemie please abar zancen tunda har zancen aure yayi nisa a kan shi,kawai mun hak'ura"
"Kun hak'ura kuma? Ki bari dai wlh zan mishi zance kuma duk yadda mukayi dashi zan gaya miki"
"To shaken an....."Vote and comment please
Mmn Shureim

YOU ARE READING
MIEMIE BEE A WANKI GARORI
FantasyLabarine k'irk'irarre na tabbata zai Ilmantar tare da nishad'antar daku,kuci gaba da biyoni karku bari a baku labari... LOVE YOU