27

1.2K 123 3
                                    

MIEMIEBEE👄 A WANKI GARORI

     
         🌹By Sad-Nas🌹

®REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS







   27

  Fatima da suke can Parlour'n Daddy taga komai ita da Maryam,hakan yasa ta taso da sauri tabi bayan Miemie.
Amai taji ta tana tayi sannan ta fito zuwa parlour inda suka had'u.
"Aunty lafiya?" Tayi mata alama.
Miemie tayi murmushi tace "Wlh haka kawai naji zuciyana na tashi sai kuma naji amai yazo min"
Murmushi Fatima tayi tare da nuna mata cikin ta. Ma'ana wai kodai ta samu ciki ne?
Sai a wannan lokacin Miemie ta fara tunanin hakan itama,sai kuma tace "Haka ake samun cikin a lokaci k'ank'ani?"
Dariya Fatima ta mata tare da d'aga mata kai alamu "Eh" sannan ta fice.
Miemie ta kimtsa kanta sannan ta sake komawa gunsu tace "Kuyi hak'uri"
"Sannu" cewar Brothers na Ammar d'in,Zayyad yace "Yazid kira Ammar muje hospital inaga hakan zaifi"
"Ok" sannan ya kira shi wayan yanata ringing ba'a d'auka ba.
Nabil yace "Ko kin kwana da rashin lafiya ne?"
Murya can k'asa tace "A'a ba komai da kun barshi ma"
Lukman yace "Kuma fa yau d'in zasu gama komai may be wayan nashi yana silent ne"
Spoon na biyu kenan ta kai baki wanda tun bata had'iye shiba ta sake mik'ewa da sauri sai toilet nanma aman ta kuma yi.
Daddy yace da Hajiya Nana taje ta duba Miemie'n ko lafiya?
Ta fito daga toilet d'in kenan tana zaune a parlour sai ga Hajiya Nana ta shigo da sallama. Sunkuyar da kai Miemie tayi tace "Sannu Hajiya"
"Sannu Miemie kodai wani abun daban za'a dafa miki?"
"A'a bakomai"
"Sannu to,bari kuje asibiti da Yayyun nashi kuga likita"
"Toh" Miemie tace kanta a k'asa sannan Hajiya ta nufi gunsu Zayyad tace "Zayya ko kai ko Yazid ku shirya da ita Zainab d'in ko Yamal kuje asibiti"
"Toh" cewar Zayyad sannan yace da Zainab "Ki shirya muje"
"Toh" ita d'inma tace tare da wucewa d'aki.
  Zaune ta sami Miemie a parlour tace "Sannu Miemie kizo mu tafi"
"Toh" tace sanna taje tasa himar akan doguwar rigan suka fito ana musu Allah ya kare.

Miemie ita kad'ai ce a baya su suna gaba inda suke ta hiran su.
Suna isa asibitin Zayyad yayi komai da komai na ganin likita su kuwa suna zaune akan benci sannan yace "Kuzo muje"
Gun Doctor Shafi'u suka wuce kai tsaye ya duba ta tare dayi mata  tambayoyi tana bashi amsa dayake Zayyad da Zainab d'in suna daga waje.
Bayan ya gama mata komai ne yace su d'an jira shi yana zuwa. Babu jimawa sosai ya dawo tare da result d'in test d'in a hannun shi yace "Ina taya ki murnar cewa kina d'auke da juna biyu"
D'ago kai tayi ta kalle shi "Juna biyu kuma Doctor?"
"Yes, baki gane niba ko?"
"A'a"
"Ni abokin Brother'n kine Mahmud"
Murmushi tayi tace "Ayyan,nagode"
Nan dai ya bata shawarwari sannan suka fito tare.
Zayyad yace "Ya dai?"
Ita kuwa ta wuce gurin Zainab ba tare data ce komai ba,shi kuwa Doctor Shafi'u ya gayawa Zayyad komai sannan yazo suka koma gida.

Suna isowa gida Ammar kuma ya fito kenan daga gun meeting d'in nasu ya fitar da waya dan ya kira Bride kenan,sai yaga missed call na Yazid har biyu.
Kiran sa yayi yace "Sorry Bro wlh phone d'in a silent yake sai yanzu na fito"
"Dama nayi tunanin hakan,ba komai sai ka dawo kawai"
"Ok thanks" sannan ya kira Miemie lokacin harta shige parlour'n ta ta cire himar d'in ta kwanta akan gado tana farin cikin samun babby.
Wayar ta taji yana ringing da sauri ta d'auka ganin Ammar ne ke kiran ta.
Murya cikin shagwab'a tace "Hello"
"Yes Bride ya kike?"
"Lafiya lau,kun fito ne?"
"Eh yanzu kuwa,gani nan ma dawowa cause i missed you a lot"
Murmushi tayi tace "Me too Ammar" kamar zatayi kuka.
Wani irin Sonta ne yaji yazo mishi har k'irji yace "Bride are you okay?"
Cikin muryan kissa tace "I don know,but please come home Ammar i really want to see you"
Gaba d'aya ta gama kashe shi a tsaye yace "Alright,i'm on my way okay?"
"Alright byee?"
"Bye my Bride" sannan ya shiga motar shi yanata sauri,kan kace kwabo harya iso.
Ba kowa a parlour dan haka ya shige side nasu dake slide door d'in a bud'e yake,yana shiga yasa lock.
Tana ganin shi ta mik'e da sauri taje suka rungume junan su yanata manna mata kiss a jikin ta.
A hankali ta janye jikin ta ta kamo hannun shi zuwa d'aki suka zauna akan gado sannan ya cire takalmin k'afan sa had'e da rage kayan jikin shi sannan ya janyo ta jikin shi yace cewa "Come here"
Tashi ta sake yi ta juyo ta yadda zasu na fuskantar junan su tasa hannayen ta zuwa bayan wuyan shi sannan tace "Ammar ina so in gaya maka wani abu"
Mamaki yayi sosai tare da cewa "Go on Bride,i'm all ears"
Pepan ta zaro daga k'asan pillow ta mik'a mishi tare da cewa "Inji Doctor"
Karb'a yayi cike da mamaki ya bud'e yana karantawa har yanzu hannayen ta na bisa wuyan sa,sai taga ya kalle ta "What! You'r pregnant?"
Fuskar ta ya sauya ganin yadda yanayin sa ya sauya tace "Akwai wani abu ne Ammar?"
Murmushi yayi ganin yanayin ta ya sauya yace "No ba komai,amma ke kina so?"
Murmushi tayi tace "Yes Ammar"
"Are you sure Bride?" Ya sake tambayar ta.
Fuskar shi ta shafa da hannu d'aya ta fara magana cikin so da k'auna kamar haka.
"Ammar nasan na b'oye soyayyar da nake maka tun randa nayi tozali da kai,amma bazan iya cigaba da b'oyewa ba saboda nasan kai ma yanzu ka fahimci irin yadda nake k'aunar ka,haka kuma nake farin ciki sosai da samun wannan cikin."
Ammar bai san wani farin ciki zaiyi ba,na samun cikin ne,ko dai najin kalmar da bai tab'a jiba a bakin Miemie?
Kissing nashi tayi sannan tace "Baka sone?"
"Bride gaskiya banyi fatan ki samu ciki da wuri ba naso ace mun more soyayyar mu kafin nan,amma tunda kina so shikenan nima ina so 100% Allah kuma ya raya mana abinda aka samu ya kuma albarkaci abinda yake ciki."
Dad'i taji har cikin zuciyar ta tace "Ameen" sannan ya tambaye ta "Meya faru har kika je hospital d'in?"
Nan dai ta kwashe labari ta gaya mishi sai murna yake yi tare da cewa "Kina nufin su Daddy ma sun sani kenan?"
Murmushi tayi tace "Ban sani ba gaskiya,may be Brother ya sanar dasu"
Murmushi Ammar yayi tare da fara nuna mata farin cikin shi wanda nima daga nan na fice a d'akin.

A wannan ranan Yamal ta nemi izinin fita unguwa cikin sa'a ya barta tana ta murna. Gun Boka ta wuce ta sanar dashi komai,Boka yace "Wannan haka yake domin mun samu labari tun kafi kizo,dan haka ga wannan maganin ki nemi abin da kika san tafi sha kisa mata a ciki ki gauraya sannan ki bata tasha daga nan shikenan cikin zai zube."
Godiya sosai tayi sannan ta dawo gida. Duk wanda ke gidan yasan Miemie nada ciki,su Mummy sai murna sukeyi haka ma Daddy dan ya dad'e yana jiran ganin jik'ansa.
Miemie babu abinda cikin ta yafi so irin madaran shanu. Kuma kowa ya lura da hakan,shiyasa Daddy yake sa a kawo mishi dayawa sai a dafashi sannan aba kowa.
Yamal ne zaune da Laila a parlour'n Yamal d'in,Fatima kuwa tazo kawo mata waya d'an Yazid ya kirata amma wayar ta baya shiga dan haka ya kira Fatima yace ta kai mata wayan.
Ta iso gurin slide door d'in kenan  har zata danna door bell dayake a rufe yake sai taji Yamal na magana da wata.
"Dama Boka yace idan na fahimci me tafi so na abin sha sai na zuba maganin a ciki,tana sha cikin zai zube"
Fatima ta kama baki tare da kasa kunne da kyau tana sauraro.
Muryan Laila taji tana cewa "Ai kuwa cikin nata yana son madaran shanu dan haka a ciki zamu zuba mata"
"Eh mana yanzu ma zanje na dafa madaran ne sannan nasa mata maganin a nata ki kai mata"
"To shi kenan bari na tafi"
Fatima tana jin haka tayi saurin danna door bell yayi dai-dai da fitowan Laila tace "Fatima shiga tana ciki"
Murmushi Fatima tayi sannan ta shige tare da mik'a mata wayan ta mata bayani cewa Bro Yazid ne zai mata magana.
Shuru Fatima tayi tana nazarin maganganun nasu "Wato cikin Aunty Miemie suke son ya zube? To meyasa suke son zubar mata da cikin?"
Yamal ce ta katse ta da cewa "Ga wayan Fatima nagode"
Murmushi tayi sannan ta wuce d'akin Miemie tare da niyan zama agun ta har sai an kawo madaran,kuma koda Bro Ammar ya dawo bazata fita ba. Ita kuwa Yamal ta wuce kichine.

Vote!
    Vote!!
       Vote!!! And also drop you'r comment dearis

                              Sadnas🌺

MIEMIE BEE A WANKI GARORITempat di mana cerita hidup. Terokai sekarang