MIEMIEBEE👄 A WANKI GARORI
🌹By Sad-Nas🌹®REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
DARASIN MU
Kamar yadda wata 'yar'uwa tamin magana kan cewa tana da k'awayenta su kusan hud'u da ita kanta biyar kenan basu iya yin TAHIYA ba. Kawai dai suna yine amma su kansu sunsan ba dai-dai sukeyi ba,kuma suna kunyan suyi tambaya saboda suna ganin kamar abun kunyane a garesu. Nidai a nawa ganin babu wani abun kunya indai ta fanin neman ilimine musamman na addinina,idan bakiyi tambaya kin saniba zakiyita zama cikin rashin sani kenan? Ana hakane sai sukayi tozali da wannan littafin nawa mai suna (MIEMIEBEE👄 A WANKI GARORI) kuma sukaga yadda nakesa darusa kad'an-kad'an a farkon shafin,shine suka nemi number na suke gaya min cewa dan Allah inda hali insa musu yadda ake tahiya,dan su biyar kenan duk basu iya ba sannan sunmin fatan alkhairi sosai wanda naji dad'i har cikin raina😊dan haka wannan shafin naku ne Allah yabar zumunci😘
YADDA AKE TAHIYA: Attahiyyatu lillahi, wassalawatu wadd'ayyibatu Assalamu alaika,ayyuhan nabiyu warahmatullahi wabarakatuhu,Assalamu alaina wa'ala ibadillahi saalihina,Ashhadu anla'ilaha'illallahu wa ashhadu anna Muhammadan abduhu warasuluhu.17
Bayan sati guda kenan da Ammar ya karb'i number'n Miemie amma bai tab'a kiranta ba.
Ta damu iya damuwa harta gaji da jiran ganin call nashi ta fara tunanin kodai ya hak'ura da ita ne?
Muryar Mama taji a hankali tana cewa "Miemie" "Miemie" dayake yau tunda suka tashi bata jin dad'in jikinta,gudawa ta kwana dashi haka kuma ta tashi dashi kana ganinta kasan bata da lafiya.
Cikin sauri tace "Na'am Mama" tare da k'arasawa cikin d'akin tace "Sannu Mama ya jikin?"
"Da sauk'i" tace cikin siririyar murya.
Muryar Ya Mahmud taji yana sallama sannan taji na Baba ma,ga dukkan alamu sunzo ne dan a kaita asibiti.
Ya Mahmud yace "Mama gara muje asibiti kawai" sannan ya kalli Miemie yace "Kisa mata hijabinta muje"
"To Ya Mahmud nima zan biku"
"A'a ki zauna a gida sai munje tukunna"
Shuru tayi badan taso ba tasa mata himar sannan ta rik'ota sukaje har gurin motar Babanta tace dasu "Allah ya kiyaye hanya" kamar zatayi kuka.
Mahmud ya lura da fuskarta yace "Zamu tafi mubar gidan ne ba kowa? Dan nace ki jira shine zakiyi kuka?"
Baba yace "Rufo gidan kizo mu tafi to"
Da sauri ta shiga ta d'auko wayarta mai tochi sannan ta shiga baya ta zauna kusa da Mama suka tafi.Ammar kuwa zaune yake agurin wani abokinsa,nan dai ya mishi sallama ya wuce gida.
Babu kowa a parlour su Mummy kuwa sun tafi unguwa da Daddy daga matan yayyunsa sai Maryam da Fatima.
Dakinsa ya wuce ya watsa ruwa sannan ya fito,parlour'n Daddy ya nufa dan acan ya gansu zaune suna kallo.
A tsakiyarsu ya zauna tare da d'aukan remote d'in yayi offing na TV yace "Ku aikinku kenan kallo?"
Maryam tace "Me zamuyi to Bro? Sai dai in zaka fita damu"
"In kaiku ina?"
"Ka kaimu muje muga Miemie mana"
Nan take Fatima ta nuna amincewar ta tana murna.
Murmushi yayi yace "No Sis,nima yaushe muka saba da ita da har zan kaiku?"
Maryam ta marairaice tace "Please mana Bro bafa dad'ewa zamuyi ba? Infact ma ka barmu acikin mota karka nuna mata cewa damu kazo sai ka fita waje kawai ku gaisa muna kallonta daga mota please?"
Badan ya soba ya amince musu duk da dai dama shima yayi missing d'inta. Sake shiryawa yayi ya fito dogayen riguna suka sauya sai turare da suka fesa suka fito zuwa gun mota saiga motar Daddyn su ya shigo gida.
Ya kallesu suka kalleshi yace "Zamuje sayan ice-cream koda Daddy zai tambaye mu right?"
Kai suka d'aga mishi alamun "Ok" sannan suka k'arasa gunsu Daddy.
Hajiya Nana ce ta fara yin magana fuskarta d'auke da murmushi "Ina zaku haka?"
Maryam ta kalli Daddy'n su tace "Shan ice-cream" Fatima kuwa kai ta d'aga alamun "Eh"
Daddy yace "To karku jima sosai a waje"
Ammar yace "Insha Allah Dad" ya kalli Mum d'insa yace "Sai mun dawo"
Tace "To a dawo lafiya Allah ya kare"
Suka amsa da "Ameen" sannan suka fice Maryam ce a gaba tace "Bro amma dah ka sanar da ita ko?"
"Yeah you'r right" sannan ya fara neman number'n ta.Acan hospital kuwa gado aka bawa Mama domin Doctor yace sai an sa mata ruwa kuma har leda shida.
Hakan yasa Mahmud cewa "Miemie ki koma gida ki had'o duk wasu abubuwan da zaku buk'ata"
"Toh" tace dashi sannan ta karb'i d'ari biyar d'in da yake bata dan hawa nape.
Baba yana gun Doctor ta wuce,ta hau nape kenan wayarta ya fara ringing. Ganin bak'uwar number yasa tayi tunanin ko Ammar ne sannan ta d'auka.
"Assalamu Alaikum"
"Wa'alaikis salam,kina magana da Ammar"
Wani sanyi taji har cikin zuciyarta ga wani murmushi da takeyi kamar yana ganinta tace "Ina wuni"
"Lafiya ya gida da mutanen gida?"
"Alhamdulillah"
"Emm kina gida ne?"
Gabanta ya fad'i sosai tace "Lafiya?"
"Fine wlh dama ina so inzo mu gaisa ne"
"Ok,sai kazo to"
"Alright" sannan ta rigashi yanke call d'in tace da mai nape "Dan Allah Malam kayi sauri nayi bak'i a gida"
"To" yace da ita sannan ya k'ara gudu.
Cikin ikon Allah suka rigasu isowa ta karb'i canji ta wuce da sauri.
Kayan jikinta ta sauya zuwa atamfa d'inkin doguwar riga mai kyau sosai ta feshe jikinta da turare sannan ta shirya musu duk wani abu da tasan zasu buk'ata a asibiti ta ajiyesu guri d'aya,kaya yana cikin kit mai kyau,sai carpet darduma,flacks da cups kuwa suna cikin wani basket irin nasa abincinnan ta zauna zaman jiran isowar su.
Call nashi ta sake gani dan haka tasan sun iso kenan.
"Hello" ta fad'a cikin wata murya mai dad'i.
"Ina waje" yace da ita.
"Ok" tace sannan ta mik'e ta sake kallon kanta a madubi taga dai tayi kyau sosai sannan tayi murmushi ta fito.
Tun daga k'asa Maryam da Fatima suke k'are mata kallo suna cewa "Wow Bro Ammar she's so beautifull" suna sake k'are mata kallo suna murmushi.
Shima murmushin yakeyi tare da kallonsu yace "Are you sure?"
Ganin ta kusa k'arasowa gurin motar ne yasa bai tsaya jin amsar suba,saiya fita tare da rufe k'ofar motar ta tsaya daga gefe tace "Sannu da zuwa"
Murmushi ya mata suna kallon junansu yace "Yasu Mama?"
Nanne ta tuno da Mamanta dake kwance a hospital tace "Mama bataji dad'in jikinta ba yanzu hakama nazo d'aukan wasu kayayyaki ne zan kai mata"
Cikin rashin fahimta yace "Ina kenan?"
"Tana asibiti an bata gado"
"Subhanalillah tun yaushe?"
"Yau da safe ta tashi da rashin lafiyan,sai d'azu mukaje hospital shine sukace za'a bata gado"
"Eyyah i'm verry sorry for not calling you on time?"
Murmushi tad'an yi tace "Don mind,idan bazaka damuba zan tafi domin suna jirana ne"
Nan kuma ya rasa yadda zaiyi,ya kuma san abin hawa zataje ta nema dan haka yace "Allah ya bata lafiya,muje in sauke ki mana?"
"No bakomai wlh nagode"
"Look Miemie,please let me" yana kallonta har cikin ido hakan yasa taji kunyarsa sosai tayi murmushi "Ok bari naje na d'ibo kayan"
"Ok" yace da ita sannan ta wuce.
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya koma gun motar yana shiga suka fara mishi tafi suna cewa "Bro ashe dai ka iya zance"
Dariya sosai yayi dan yasan basuji abinda suke tattaunawa ba.
"You know what? Mum nata tana kwance a hospital yanzu haka zata kai musu kaya ne and i tell her that zan kaita"
Zaro ido sukayi dukkansu Maryam tace "you mean zata shigo cikin motan nan?"
"Yes!" Yace dasu sannan yayi saurin fitowa dan ya ganta da kaya a hannu.
Karb'a yayi yakai but sannan ta sake komawa ciki.
Dawowa gunsu yayi yace "Zan gaya mata cewa akwai Sisters nawa a ciki,zata zauna da Fatima a baya"
Maryam tace "No Bro bari na koma baya ita saita zauna a gaba"
"No karki damu,nasan baza ta yadda ta zauna a gaba ba because tana tsoro na"
"Tsoro kuma sai kace taga dodo?"
Dariya sukayi dukkansu sannan ya sake fita ya k'arb'i sauran kayan tare da bud'e mata k'ofar baya yace "Bismillah"
Murmushi tayi tace "Thanks" sannan ta sake yin sallama dan taga mutane a cikin motar.
Ammar yace "Miemie meet my Sisters Maryam and Fatima"
Kafin Miemie tayi magana Maryam ta fara gaisheta cike da fara'a a fuskar ta,Fatima kuwa hannunta ta kamo tana mata murmushi.
Miemie tana kallonta ta tuna cewa lallai taga fuskarta a wayan Ammar. Tace "Kece Fatima?"
Fatima ta d'aga mata kai tana dariya.
Ammar yace "Fatima itace last born namu,sannan bata iya yin magana sai dai duk abinda zaki fad'a tana ji"
Miemie tayi mamaki sosai tare da sake kallon Fatima itama kallonta takeyi tana mata murmushi tare da gyad'a mata kai ma'ana "Hakane abinda Ammar ya fad'a.
Take Miemie taji k'walla yazo mata har ido wanda ta kasa tsayar dashi sai daya zuba.
Fatima na ganin haka ta janyo rigan Ammar tana nuna mishi fuskar Miemie dase hawaye take yi.
Kafin Ammar yayi magana Miemie ta rik'o hannun Fatima tana magana cikin murya mai sanyi "Kina sona da k'awa?"
Kai ta d'aga mata tana murmushi alamun "Eh..."

YOU ARE READING
MIEMIE BEE A WANKI GARORI
FantasyLabarine k'irk'irarre na tabbata zai Ilmantar tare da nishad'antar daku,kuci gaba da biyoni karku bari a baku labari... LOVE YOU