MIEMIEBEE👄 A WANKI GARORI
🌹By Sad-Nas🌹
®REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
🎂🍾🎂🍾🎂🍾🎂
HAPPY BIRTHDAY AUNTY SIS💞💃💃
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
I know your birthday is a special day with or without me,but i have to say that you are the best Aunty i have ever had!💞
💐💐💐💐💐💐💐
May your birthday be filled with beautiful memories to cherish forever Aunty💞💞💞
🎂🌹🎂🌹🎂🌹🎂🌹
WITH LOVE FROM SAD-NAS🌹🌹
💞💞💞💞💞💞💞
ALLAH YA SAUKEKI LAFIYA MUZO CIN RENGEM AMEEN💃
🎂🍬🍾🍡🎂🍬🍾🍡
💞
💞
💞KUYI HAK'URI YAU BABU DARASI,AMMA DUK DA HAKA TUNDA YAU FRIDAY NE KARKU MANCE DA KARANTA SURATUL KAHFI, DAN NIDAI NAYI NAWA😊😊
12
Jin basu shigo bane ta sake fitowa ta d'auki sauran kayan har zata shiga gida Mahmud yace "Ki kawo mana buta muyi alwala" dad'i taji dan tasan idan suka tafi masallaci zata je ta karb'i sak'on Alhaji Abdul.
"To" tace dashi sannan ta wuce babu jimawa ta fito musu da buta guda biyu sannan ta koma gida ta wuce d'akin Mama tana cewa "Mama an sake kirana ko?" Mama tace "Babu wanda ya kira" kanta ta k'aik'aya tace "Wlh Ya Mahmud ya kopsa daya iso yanzu,nasan dole dai babban waya Alhaji Abdul zai aiko min wlh, wannan na Sadiq d'in kuwa sayarwa zanyi in sayi dogayen riguna" Mama ta kalleta tace "Kedai baki da aiki sai k'arya wa samari da son sayan kaya sai kace wata matar gomna?" Murmushi Miemie tayi tace "Wlh Mama sai kinga abokin Ya Mahmud bafulatanine sak kamar ni" tana dariya sai taji Mahmud ya k'wala mata kira a gigice ta fito tayi waje "Na'am Yaya"
"Kwashe butan kikai ciki"
"To" sannan ta kwasa tayi ciki su kuwa suka tafi sallah.
Lek'owa tayi a hankali dan ta tabbatar sun shiga masallacin sannan ta fice da sauri ta k'arasa gun motar.
Yana hangota ya fito rik'e da leda a hannunsa "Ina wuni" yace da ita murmushi tayi masa tare da amsa masa cike da fara'a sannan ya sake cewa "Alhaji ne yace in kawo miki" harda d'an sunkuya mata tasa hannu ta karb'a tare da cewa "Nagode,Allah ya mayar da kai lafiya" shima murmushin yayi yace "Ameen" sannan ya shige motarsa itama sauri takeyi karsu Ya Mahmud su fito su ganta har ta wuce gida.
Isarta kenan ta wuce d'akin Mama ta bud'e ledan ai sai taga Iphone5 ne,ihu da murna tayi sosai Mama tana ce mata "Kiyi da kyau idan ya jiyoki kyasan abinda zaki gaya masa" tsit Miemie tayi tare da rufe baki da hannayenta biyu sannan taci gaba da bud'e kwalin tana murna "Mama kina ganin wayan? Hmmm Allah dai yasa kar Baba yace aurar dani zaiyi yanzu dan wlh ban gama cin 'yan matancina ba,nafi so inga inata wankan su wlh abin burgeni yake" taci gaba dayin dariya Mama tace "Sai kiyi ta fama ai,tashi kije can d'akinki ki k'arasa ihun naki" taci gaba da cewa "Kuma nima gara dai a aurar dake ko kyayi hankali,sannan na gayawa Babanku babu wani wanda kike so sai abokin Yayanki,yace dai kiyi shawara nan da sati d'aya dan yasan me zai gayawa Alhaji Abbakar."
Jikin Miemie yayi sanyi da tasan maganar gaskiya ce tace "To Mama ni yanzu taya zan amince bayan ban sanshi ba ban tab'a ganin saba,kinsan fa ni bana son mai k'aton kai irin na Sadiq" dariya Mama tayi tace "To sai Mahaifinku ya basu izinin zuwan yaron ai,idan kun dai-daita shikenan" shuru Miemie tayi tana tunanin lallai maganar Mama gaskiyace kuma ai ta hakanne ma zata samu ta wanke shi sosai bare ma shida Mahaifinsa yake da kud'i? Kallon Mama tayi tace "Eh wlh Mama ki gayawa Baban haka" sallamar su Ya Mahmud ne yasa tayi saurin tattara wayan da ledan tasa a walldrop na Mama ta rufe sannan ta fito domin kai musu abinci Mama kuwa tana gaisawa dasu.Bayan sallan isha Mahmud ya kira Miemie domin su gaisa da Aliyu,shi yana daga cikin d'akinsa Aliyu kuwa yana zaune a parlour ta shiga da sallama ya amsa mata cike daso sannan ta zauna daga gefe akan kujera shi kuwa yana nesa da ita.
Kanta sunkuye dan kunyansa da take ji tace "Ina wuni" a hankali dan bata so Ya Mahmud yajima abinda take cewa.
Murmushi yayi yace "Lafiya Miemie ya muka sameku?"
"Alhamdulillah,an gama aiki lafiya?"
"Lafiya lau wlh sai kuma aiki yanzu kam insha Allah" murmushi tayi tace "Allah ya bada mai albarka" yace "Ameen" sannan duk sukayi shuru na d'an wani lokaci sai ya kalleta ya sake cewa "Miemie nasan dai kinji komai akaina,gaskiya tun ban gankiba naji zuciyata ta aminta dake sosai,bayan na ganki kuma sai naga kamar karanbani nayi" dariya sosai maganar nashi ya sata, yace "I'm serious" d'an kallonsa ta sake yi tace "A'a ba haka bane kuma bakayi karanbani ba" murmushi yayi yace "Please ki gaya min gaskiya indai har baki gamsu dani ba,saboda na tab'a son wata 'yar'uwata amma daga k'arshe akace wani za'a bata bani ba,hakan yasa naji tsoro ban sake furta soyayyata ga kowa ba sai ke" shuru tayi na d'an lokaci sai kuma tace "Yanzu tayi aure?" Yace 'A'a bata yiba tukunna amma dai an kusa" kallonsa ta sake yi yayi dai-dai da shima ita d'in yake kallo tayi murmushi wanda yake masa kyau sosai tace "Ai duk abinda kaga bawa bai samu ba to dama can bayi da rabo akan wannan abun ne,dan haka ina maka fatan alkhairi" Mahmud dake zaune a cikin d'aki yana sauraron hiran nasu sai abin yana bashi mamaki yaushe Miemie ta iya hira haka, kodai tana hira ne sosai idan baya nan? Nidai sadnas nace babu ruwana.
Aliyu yace "Hakane,yanzu a ina kika ajiyeni?" Kunyar tambayar tasa taji dan batama san me zata ce masa ba,har sai daya sake tambayarta sannan tace "Ya Aliyu zanso kad'an ban lokaci... sai kuma ta kasa k'arasa maganar.
Murmushi yayi sannan ya d'ago yana kallonta yace "Ba damuwa zan jira har lokacin da kika d'iba ya cika,fatana shine Allah yasa inji alkhairi" kallon juna sukayi tare da sakarwa junansu murmushi tace "Ameen,ni zan shiga gida" sannan ta mik'e tsaye shima haka yace "Nagode da lokacin da kika bani,sai da safe" murmushi kawai tayi sannan ta fice ta nufi d'akinta tana mai jin tausayinsa har cikin ranta kuma bata san dalilin hakan ba.
Shi kuwa Aliyu cikin d'aki ya shige ya kwanta akan gadon Mahmud yana cewa "Dan Allah Abokina ka tayani da addu'a Allah yasa ta amince dani" murmushi Mahmud yayi yace "Insha Allah" nan dai Aliyu yayita yaba irin kyau da nutsuwan Miemie ga iya kalamai masu dad'i,gaskiya idan yayi missing d'in Miemie bai san yadda zaiyi ba.Gidan Alhaji Abbakar kuwa 'Ya'yansa Maza ne kewaye dashi suna cewa "Daddy yaushe ne Ammar zai je yaga amaryan nashi?" Murmushi Daddy yayi yace "Nayi magana da Mahaifin yarinyar ina jiran izinine daga gunsa kafin na sanar daku" Maryam tace "To Daddy 'yar gidan waye ne ita yarinyan?"
Daddy ya kalli Ammar yace "Shi Ammar d'inma bai tambayeni ba sai ku? 'Yar gidan Alhaji Bello mai Shanu ne,shine wanda nake sayan shanu da raguna agun sa" zuciyar Zayyad ya buga jin sunan da Daddy'nsu ya ambato "Alhaji Bello Mai Shanu?" Ya nanata sunan a zuciyarsa,kar dai Miemie ce? Dan bazai tab'a mance sunan mahaifin taba alokacin farkon had'uwarsu da yake nunawa wani abokinsa ita daga nesa sai yake gaya masa cewa "Ai 'yar gidan Alhaji Bello mai Shanu ce."
Ammar dai baice komai ba in banda d'an murmushi dayayi, Nabil yace "Daddy ni ko sunan sama ban tab'a jiba sai yau" Mummy tayi dariya tace "Duk ku tashi ku tafi gurin iyalanku kubar sauran ayi hiran dasu"
Babu musu suka mik'e su ukun Zayyad dai sai tunani yakeyi "To kodai ba Miemie bace? K'ila yaran nasa da yawa ne zayyu d'aya daga cikin sune amma dai zan sake tambayan friend d'ina inji yaran Alhaji Bello Mai Shanu nawa ne?" Da wannan tunanin ko wannesu ya wuce d'akin sa,su Ammar kuwa suna can parlour'n Daddy sunata hira ana dariya.Sani bodari ne keta kiran Miemie ta wayan Mama,har dai ta gaji ta d'aga yace "Haba Miemie me yake faruwa nake kira bakya d'agawa?"
Azuciyarta tace "Taya zan d'auka bayan ka zama bodari" a fili kuwa cewa tayi "Dan Allah Sani ka dena kiran wayan Mama haka,ka sanfa yanzu Ya Mahmud ya dawo gaskiya kawai kayi hak'uri idan na had'u da friends nawa zan dinga maka flashing saika kira mu gaisa"
"Bakomai dama ina waje ne,amma tunda Yayanki ya dawo zanje gidansu Hanifa in bata wayar dana kawo miki kinji?" Tab'e baki tayi tace "To nagode" sannan ta kashe wayar tasa dariyan mugunta.
K'ofar gidansu Hanifan ya nufa sannan ya kirata a waya dayake duk yana da number'n su. Batayi mamakin ganin kiran Sani ba dake suna gaisawa dama,d'auka tayi tare da sallama yace tazo yana jiranta a waje.
Da hijabi ta fito suka sake gaisawa sannan yace "Dama sak'o na kawo miki kiba Miemie,dan tace Min Yayanta yana nan baza ta samu daman fita ba"
Hanifa tasa hannu ta karb'a tare da cewa "Lallai kam ya dawo jiya da yamma" Sani yace "Toni zan koma sai anjuma" tace "To Allah ya kare" sannan ta wuce gida ta canja kaya ta sake fitowa da ledan wayan amma ta b'oye shi acikin hijabinta ta yadda baza'a gani ba.Vote!
Vote!!
Vote!!!
and comment please

YOU ARE READING
MIEMIE BEE A WANKI GARORI
FantasyLabarine k'irk'irarre na tabbata zai Ilmantar tare da nishad'antar daku,kuci gaba da biyoni karku bari a baku labari... LOVE YOU