MIEMIEBEE👄 A WANKI GAGORI
🌹By Sad-Nas🌹
REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
we don't just entertain and educate,But we also touch d heart of the reader's
57
A yaune Kamil abokin Ammar suka kai sadakin Meela aka kuma tsai da ranan aure nan bada jimawa ba. Murna sosai k'awayenta suka tayata dan ya mata kaya sosai dai dai k'arfin shi.
Hakama Ya Mahmud ansa ranan aurenshi da Fatima tsakaninsu da su Meela dai sati biyu ne kacal. Dan a yanzu auren Ya Mahmud da Bilki wata uku kenan dan har sun samuwa k'aruwa ma'ana tana da cikin wata d'aya.Laila ta samu sauk'i sosai dan haka aka dawo da ita gidan mijinta Lukman. Yamal kuwa tun a wannan lokacin ta rage fitowa parlour barema ta shiga kichine aiki,dan a cewarta wai bata da lafiya,ta rame sosai ga wasu kuraje da suka feso mata. Babu yadda ba'ayi da itaba akan suje asibiti amma taqi,shi kuwa Ammar dayake Doctor tunda yaga yanayinta sai yaga ta mishi kama da mai ciwon k'anjamau,hakan yasa yaba Brother'nshi shawara akan lallai ya takura suje asibiti dukkansu domin a musu gwaji,dan bai b'oye mishi abinda yake zargi game da yadda yaga ciwon Yamal d'in ba.
Koda zo mata da maganan saita k'i amincewa,amma saiya mata baraza da saki wanda dokllenta ta ta shirya suka tafi amma badan soba,dan ita kanta tsorone yake hanata zuwa asibitin.
Banu wani jimawa result ya fito daga gun Doctor Shafi'u ya kuma tabbatar musu da cewa Yamal tana d'auke da cutar k'anjamau,amma shi Yazid bayi dashi. Dukkansu saida sukayi mamaki,ita kuwa yamal musawa tayitayi tace wlh bata dashi a ina zata samu bayan tasan Yazid ne kad'ai mijinta da take tarayya dashi?.
Koda Daddy ya samu wannan labari baiji dad'in saba sam,dan haka yasa d'ansa Yazid a gaba yace "Taya za'ayi ta samu wannan cutan ace kai kuma baka dashi,ba kai bane mijinta Yazid ka gayamin gaskiya" Yazid yayita rantsuwan cewa wlh baya bin matan banza,itama Yamal d'in ai zata iya bada shaida a kanshi.
Koda daddy ya sake yin bincike sosai agun Dr Shafi'u ya kuma gamsu sosai,hakan yasa Yazid cewa dole ita tasan wani abu tafito fili kawai ta gaya mishi gaskya,amma sam Yamal sai kuka takeyi da rantsuwa kan cewa wlh bata san komai ba kuma bata bin maza.
Hakan yasa yace taje gida zai nemeta amma dukda haka taqi tafiya,ananne Daddy yace yakaita gida da kanshi ya kuma iyawa mahaifinta bayanin komai shima yananan zuwa.
Bayan ya maidata gida bai b'oyewa Mahifinta komaiba ya gaya mishi,Mahaifinta yace bakomai Yazid jeka,banga laifinka ba dan ko nine hakan dakayi shi zan aikata. Mahaifin nata da kanshi ya kaita gun Dr'n shi dan a sake mata gwajin,nanma dai duk abu d'aya aka sake gaya mishi,yasata a gaba akan ta fad'i gaskiya amma sam tace bata san komai ba kuma bata ta
Rayya da ko wani namiji.Ayau aka d'aura auren Kamil da Meela,shagali akayi d'an dai-dai sannan aka watse,Kamilbda Meela dai ji suke kamar an musu sadakan Aljanna da murna.
Miemie tana wkance jikin Ammar inda take ce mishi "Cream wlh ina da wata shawara da hakan zai yuwu"
Cikin d'okin sonji me zatace yace "Enhen go ahead" tace "Me zai hana kama Ya Yazid magana akan hanifa k'awata,wlh tanada hankali da nutsuwa na tabbata zaiji dad'in zama da ita a matsayin mata"
Ammar yayi murmushi yace "To ance miki sun rabu da Aunty Yamal d'inne da har kike mata tayin wata?"
"Toh taya za'ayi suci gama da zama tare bayan tana da lalura shi kuma bayi dashi? Ai rabuwan su ya zama dole nidai inayiwa k'awata kamun k'afa agunka" dariya yayi sosai yace "Nidai na ruwana" itama tana murmushi tana zancen zuci "Waya sanima ko Bokan natane ta bashi kanta dan neman duniya tayu ta hakannema ta samu cutan,astagfirullah zato zunibi".
Ganin abinda ya faru da Yamal yasa Laila jin tsoro sosai,duk da dai ita bata zama shaid'aniya kamar Yamal ba,hakan yasa ta nemi zama da Miemie lokacin ba kowa sai su kad'ai,nan dai ta gayawa Miemie komai ta kuma nemi gafararta data yafe mata. Miemie taja dogon numfashi tare dayin salati tace "Tabbas zancena ya zama gaskiya,kina nufin agun Boka ta samu cutan da take d'auke dashi?"
Laila tace ko kokonto bazanyiba,dan lokacin tana cemin "Amma Laila baki da wayo,to wama zai san muna tarayya da Boka,tunda ke bazaki iyaba ina fata dai zai zama sirri a tsakaninmu,tayu idan kikaga aikin Boka yamin aiki kema ki dawo hanya" sai nace mata toh to da haka na fita yanzu taketa tata hidimar ita da shi.
Miemie tace "Allah ya k'ara tsare mana imaninmu,na yafe miki har abada Laila,domin naga kinyi nadama ba kad'an ba,Allah ya yafe mana baki d'aya" Laila tace "Ameen,amma dan Allah hakan ya zama sirri a tsakaninmu please?" Miemie tayi murmushi tace "Bakomai" azuciyarta kuwa tace "Ai kin makara domin Hajiya Nana Maryam da fatima duk sunsan komai,Amma insha Allah zanje inyiwa Hajiya Nana magana akai dan inci gaba da rufa muku asiri,idan kuma ita Yamal d'in ta tona muku asiri daga baya to shikenan."Acikin wannan satin kuwa gidan Alhaji Abbakar shirye-shiryen bikin auta kawai akeyi wato Fatima.
Ita kuwa Bilki ta kwantar da hankalinta kamar ba ita za'a kawowa amarya ba,dan duk ita take tayashi wasu shirye shiryen bikin,hakan yasa ta sake samun masauk'i na musamman acikin zuciyar shi. Ya Mahmud da dai inaga kamar baya son Bilki,amma a yanzu kam sai hmmm afili yake bayyana yadda yake k'aunar ta,nace Allah yasa ya d'aure ya kuma yi adalci a tsakanin su ameen.A yaune Miemie tacewa Hanifa tazo zata rakata wani waliman aure dan haka ta shirya sosai,hakan yasa Hanifa tayi shiga mai kyau ta d'auki hanya. Dama kuma tunda ta fara tunani had'a Hanifa da Ya Yazid ta fara shishshige mishi,yana dawowa zatace "Sannu da dawowa Ya Yazid ganan abinci harma dana musamman" tayi ta mishi hidima dai duk Ammar yana ganinta sai dai yayi dariya yace "Nidai ba ruwana" tace "Oho dai nikam da ruwana kuma insha Allah zanyi nasara"
Toh yau ta tabbatar Ya Yazid bazai fita ko ina ba shiyasa tacewa Hanifa tayi tazo zata rakata walima.
Yazid da Ammar suna zaune a parlour ta same su tace "Ya Yazid da badan kar ace nayi karanbaniba da sai ince wani abu" yana murmushi yace "Menene our Bride?" Nan tad'an sami k'warin gwuiwa tace "Amma fa idan nayi kuskure toka huce akan Little Bro naka" yayi dariya yace "Angama barima na rik'e shi sosai karya gudu" nan ya damk'o Ammar sunata dariya dukkansu.
Ta da'anyi shuru sannan tace "Dama bana jin dad'i ganinka kai d'aya ne,shine nida Little Bro naka mukayi shawaran sama maka abokiyar zama ta gari inhar ka amince" Ammar yayi saurin zaro ido yana ganinta cikin mamaki dan baisan haka zata fad'a ba. Ita kuwa gira ta d'aga mishi tana mishi gwalo.
Yazid kuwa kallon Ammar yayi yana bugun kanshi yana cewa "Nasan wannan shawaran nakane Little Bro,to ba komai ai nasan ka iya zab'e dan haka ina farin ciki da zab'in ku" dad'i sosai Miemie taji tace "Nan da wasu dak'ik'aima zata iso" yayi murmushi yace "Da sauri hakane abun?" Miemie ta kalli Ammar alamun yace wani abu mana,nan dai sai yace "Eh dan karkayi saurin hango watane mu rasa k'uri'a ai."
Dad'i sosai Miemie taji har cikin ranta,tayi mishi alamu ta yadda ma Yazid bai gani ba "Das why i love you my Cream" Yana mayar mata da wani murmushi mai d'auke da sak'on So...Vote and comment plsss
Mmn Shureim

ANDA SEDANG MEMBACA
MIEMIE BEE A WANKI GARORI
FantasiLabarine k'irk'irarre na tabbata zai Ilmantar tare da nishad'antar daku,kuci gaba da biyoni karku bari a baku labari... LOVE YOU