Page 9&10

520 38 4
                                    

🌸 *HASEENAH*🌸

story nd written
by👇🏻
Aysher Abbakar (Meerah)

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303

follow me on wattpad @Aysherabbakar

*long live pml*

'''GODIYA GA ALLAH DA KUMA 'DUMBIN MASOYA MASU KIRANA DA MASU INBOXING DINA KAN WANNAN LITTAFI, KOWA DA NASHI RA'AYINDA YAKE FADAMUN, NA GODE SOSSAI DA KULAWARKU, KUMA KU KWANTAR DA HANKALINKU KU CIGABA DA BINA IN SHAA ALLAH ABUNDA KUKE TUNANI BAZAI FARU DA UMMAH BA, NA GODE SOSSAI ALLAH BAR KAUNA '''

*9-10*

Mummy mayafin ta kawai ta yafa ta koma bakin gado ta zauna tana faman kad'a k'afa, jiran zuwan Mum Haseen kawai Mummy take, ba jimawa kuwa sai gata ta iso, ko zama bata yiba suka fice daga gidan, basu tsaya ko ina ba sai wajan Bokan nasu, tun kafin Mummy tayi magana ya dakatar da ita sannan yace mata yasan duk abunda ke tafe dasu, Mummy sai mazurai kawai take jira take taji me zaice, seda ya gama dube dubensa sannan yace wa Mummy " yanzu me kikeso a miki?"

shuru Mummy tayi daga bisani tace" Allah ja da ran boka, nifa inta nice wallahi nafi son a kashe wannan mayyar matar da 'yarta, ko kuma a salwantar da rayuwarsu gaba ....

kafin Mummy ta k'arasa maganar Boka ya daka mata tsawa, cikin wata muryarshi me kuwwa yace" na fad'a miki hakan bazai samu ba inba so kike daga ni harke mushiga cikin bala'i ba, in abunda zai na kawoki knan kar ki sake zuwa mun nan, in ba haka ba zan had'a ki da muggan Aljanu"

ba k'aramin gigicewa Mummy tayi ba, cikin 'yan seconds ta hau kyarma, dubanta yayi da wannan mummunar fuskar tashi da taji zane da wasu fararen hoda yace" buk'ata ta gaba"

cikin sansayyar murya tace"to Boka a dubamun me yakamata ayi"

nan ya cigaba da dubanshi sannan yace" akwai wani abunda yake shirin faruwa wanda suke 6oyeshi, na gama duba iya abunda zan iya amma bangane menene ba, ynzu abunda zamu fara zamu tura mata aljanu su saka mata kasala, inmunyi galaba akanta to nanne zamusan ta yadda zamu 6ullo mata"

wani k'aramin k'ullin magani ya d'auko ya cilla mata sannan yace" ta raba maganin biyu ta barbad'a rabi a k'ofar d'akin Ummah sannan tasan yanda zatayi ta zuba mata sauran a ruwa ko a abinci"

hanunta na rawa ta d'auka nan suka dire mishi kud'i suka bar wajan.

da sauri suka fice awajan suna mayar da numfashi, seda sukayi nisa da bukkan Mumny taja tsuka ta kalli Mum Haseen tace

"nifa wannan malamin naki ba wani abun arziki ya iya ba, in zaki nema mana wani waje ki nema, dan gaskiya na gaji da hawa da saukan nan ba wani canji, nidai aiki d'aya yamun wanda zance naji dad'in shi amma sauran duk shirmensa yake zabgawa"

kallonta Mum Haseen tayi sannan tace " yanzu dai duk wannan me sauk'i ne, abun tanbaya anan shine, menene abunda yace an 6oye kuma shima ya duba be gane ba?"

wani tsukan Mummy tasake yi sannan tace " to ba ga irin shirmen ba, shima bai gane ba tayaya ni zan sani? amma zan zuba ido in san menene"

nan suka koma gida kowa da abunda yake sak'awa a ranshi, sun rabu da Mummy kan zata nema musu wani wajan koda awajan abokan kasuwancin ta nan bada jimawa ba, da haka sukayi sallama.

can kuwa a makaranta sai k'arfe biyu Haseenah ta dawo, duk damuwanta Ummanta waze kula da ita, ahaka har ta samu ta iso, da sauri sauri gudu gudu ta shigo gidan, tana shiga d'akin Umman tata ta samu Aunty Zuwaira na nan bata tafi ba, wani ajiyar zuciya ta saki wanda ya sanya dukansu kallonta, Aunty ce ta dubeta tace " wannan ajiyar zuciyar fa? k'alau?"

murmushi tayi sannan tace " wallahi Aunty nayi tunanin kin tafi, shine nake ta damuwar waze kula da Umma gashi bata da lafiya"

dukansu dariya sukayi ba tare da sunce komai ba, nan ta wuce bedroom ta cire kaya sannan tayi sallah ta fito, duban Ummanta tayi tace " mezan dafa miki Umma?"

" a.a ki nemi abunda ke zaki ci ni gashi Auntynki damun dambun couscous ya isheni daga nan har dare"

dariya tayi ta dubi Aunty tace" to ke mezan dafa miki?"

"nima naci danbun na gode saidai ke ki nemi abunda zaki ci"

nan ta wuce kitchen ta dafa indomie guda d'aya da k'wai biyu ta fito ta koma d'aki, Aunty ce ta dubeta tace" to da Allah tayaya mutum zeyi haiba kullum abincin kenan ba wani abun arziki"

dariya kawai tayi ba tare da tace komai ba.

nan ko Mummy ta saka saratu ta la6e ta jiyo mata duk abunda suke cewa, haka ta gaji da tsayuwarta bataji komai ba ta juya ta koma wajan Mummy, da yamma Mummy ta sake turota, nan Saratu ta la6e ko zataji wani abu nan ma shuru, hakan yayi dai-dai da fitowan Aunty Zuwaira dan zata tafi, Haseena na biye a bayanta zata mata rakiya.

Saratu bata ji tafiyar su ba illa uban rank'washin da taji an kafa mata a tsakar kanta, wanna aikin Aunty Zuwaira ce, nan ta janyo ta tace" lek'en me kikeyi munafuka?"

nan ta fara kame kame ta rasa me zata ce, Aunty zuwaira tace " to in kuwa haka halinki yake, wataran zaki jiyo abunda zai kurmantar da ke munafukar banza"

sum-sum Saratu ta kama hanya ta wuce wajan Mummy ba tare da tace komai ba.

seda Haseena ta raka ta har wajan motarta, nan Aunty Zuwaira ta bud'e boot ta fiddo musu da kayan abinci dasu drinks kaji da sauran abubuwa, ta bata dubu biyar tace tana siyawa Ummah duk abunda take so.

har Aunty ta shiga mota zata tayar ta sake k'walla wa Haseena kira, nan ta dawo, umarni ta mata tace ta shigo cikin motar, ba musu Haseenah ta shiga gidan gaba, Aunty ce tafara da cewa " Haseenah nasan ke mai hankali ce da sanin yakamata, kinga yanzu 'yar uwata tana buk'atan kulawarki, tunda bata da kowa ga kuma lalurar data sameta, kinfi kowa sanin halin abokiyar zamanta, tunda kika fara ganin Saratu tana muku la6e to da abunda yake ransu, duk wata hanya da kika san zasu bi to karki yarda ki bari a cutar da ita, ko kuna d'aki ne ban yarda kuna barin k'ofar palour a bud'e ba, kisa key ki kulle duk gulmar su haka bazasu jiyo komai ba, haka duk abunda suka baku to karku ci kuma karku rik'e koda cokalin su ne, shiga d'aki da BISMILLAH fitowa da LAHAULA, ki kiyaye Haseenah, ba ruwanki da su, in school zaki tafi ki ajiye wa Ummah duk abunda kikasan zata nema ba tare da ta fita ba har ki dawo, sannan kice mata tana kulle d'aki, ita ma zan kirata a waya in jadadda mata kinji ko?"

gyad'a kai Haseena tayi tace In Shaa Allah zan kiyaye.

nan sukayi sallama ta fita.

duk abunda ya faru kan idon Mummy tana raku6e jikin window d'akinta, dukda bata san meke faruwa ba taji bak'in cikin rashin jin abunda Aunty take fad'awa Haseenah, dan ganin yanda Haseenah ta nutsu tasan abu mai mahimmanci take sanar da ita.

tsuka taja ta koma ta zauna cike da bak'in ciki, Saratu ce ta dube ta tace" Mummy wai me take fad'a mata ne?"

harara Mummy ta watsa mata tace " ubanki naji, sabida nid'in aljana ce ai dole inji abunda ake fad'a cikin motar ko?"

shuru Saratu tayi batace komai ba, dan tasan inta sake magana duka ne da zagi zai biyo baya.

hakan yayi dai dai da shigowar Haseenah cikin palour d'auke da kaya a hanun ta, wucewa tayi ta ajiye ta koma dan kwaso sauran, dariya Mummy ta saki sannan tace" gida babu se an had'a da rok'o, to duk abunda ake 6oyewa zai fito fili dan uban mutum, inma ciki aka yiwo duk zamu gani, dan mutum shuru shuru tsiyarshi sai Allah"

gaban Haseena ne ya fara dukan tara tara jin Mummy ta ambaci ciki, amma da taji yanda maganar ta dosa sai hankalinta ya kwanta.

ba tare da tace musu komai ba ta wuce ta tafi, abunda yafi k'ona wa Mummy rai kenan tayi magana ak'i tanka mata, Haseenah tana shiga ta kulle k'ofa ta murza key.

Saratu ne ta dubi Mummy, Mummy ma saratun take kallo, ko meye dalilinsu na kallon juna oho....

for comments only 08144932303

HASEENAHМесто, где живут истории. Откройте их для себя